TUNA BAYA

204 13 4
                                    

*TUNA BAYA*

Daga yanda yake tafe jikinsa a matuk'ar sanyaye, fuskarsa cunkushe da damuwa ya tabbatarwa da Mahaifiyarsa yau ma ba'a dace ba, da matukar tausayi take kallonsa.
Kan tabarmar da ke shinfide a kofar dakin ya zube jagwab ya watsar da takardun hannunsa gefe guda, ya tallabe kansa da hannu bibiyu.

Murmushi tayi k'okarin wadata fuskarta dan kwantar masa da hankali.
   "Kamaluddeen?"
Ta kira sunanshi muryarta a tausashe.

   "Na'am Umma"
Ya amsa kanshi a kasa, muryarsa har rawa take saboda tsabar damuwar da zuciyarsa take ciki, ga kuma mugun gajiyar da ya kwaso.

   "'Dago fuskarka ka kalleni mana d'an Umma?"
Idanunshi ciccike da kwallah ya dago yana kallonta. Murmushi ta sake sakar masa ta sake gyara zamanta a kusa dashi.
   "Kar6i ruwa kasha"
Ta mika mishi babban kofin roba cike da ruwa mai sanyi wanda ta debo a randar kasar da ke ajiye a kofar d'akin.

Hannu bibiyu yasa ya kar6a yayi bismillah ya kafa kai ya fara kwankwad'a, kad'an ya rage sannan ya aje kofin gefe guda.

Mik'ewa tayi ta shiga dan tsukikin kicin din da yake tsakar gida ta zubo mishi faten tsaki a farantin roba, ta sako mishi cokali a gefe.
Hannu baka hannu kwarya ya ringa Kai loma, daman da Tsananin yinwa ya koma gidan.
Saida taga ya natsu yayi hamdala ta kalleshi da kulawa.
   "Yau ma ba'a dace ba ko?"

Saida ya had'iye wani dunk'ulallen miyau na tsabar bakin ciki da takaici,  hana idonshi barci yayi ya tashi tun bayan sallar  asubah ya fice neman aikin, saboda tun satin da ya wuce ma'aikatar suke ta sanarwar neman ma'aikata masu irin matakin karatunshi, amma  da yaje ko interview din da suka ce zasu yi ma basu yi ba, saida rana ya gama kod'asu tun safe har Karfe uku, sannan aka sanar dasu suyi hakuri har an rufe d'aukan ma'aikatan. Karin bakin cikinsa shine pure water na naira goma kawai ya saya a take ya shanye, baida ko sisi da zai sayi abinci.

   "Wallahi Umma ba'a dace ba, yanzu a kasar nan in kinga ka samu aiki to saidai in kai wani ne ko kuma dan wani, idan biyun nan basu samu ba to ya kasance ka san wani ko kuma ka san wanda yasan wani mai hanyar samun aikin. Amma in ba haka ba bazaka taba samun aiki ba duk kyan takardunka.
Muna tsaye a gurin fa sai lek'owa ake ana kiran sunayen wad'anda suke da k'afa a gurin, mu kuma da bamu da hanya ko oho, saida rana ya gama gasa mu sannan aka sallame mu da cewar an gama d'aukar ma'aikatan"

   "Babu komai Kamaluddeen, lokaci ne, watarana sai labari in Allah ya yarda"
Ta fada muryarta a tausashe, da salon kwantar mishi da hankali.
Amma fa zuciyarta cike take da matsananciyar damuwa.

   "Allah yasa haka Umma"
Ya fad'a yana k'ara jin kwarin gwiwa a zuciya da gangar jikinsa.

    "Ameen"
Shiru ne ya ratsa tsakaninsu, kowa da irin tunanin da yake yi a zuciyarsa.
Umma kam har idanunta sun fara tara kwallah, babu wanda ta tuna sai marigayi Malam Ahmad, mahaifin Kamaluddeen, wanda ya rasu shekara d'aya da ya wuce.

A lokacin rayuwarsa shi yayi ta fafutuka ya buga nan ya buga can har Allah yasa Kamal ya kusa kammala karatunshi.

Sunsha jik'a garin rogo su sha babu suga saboda a biya kud'in makarantar Kamaluddeen, idan ta zauna tana mitar yanda karatun yake jan kud'i da cinye duk d'an tattalin arzikinsu saidai ya kalleta yayi murmushi.
Bai cika tankata ba saidai idan yaji mitar tak'i k'arewa sai yace
   "Kiyi hakuri Hajara, wata rana sai labari, wannan karatun da kike gani kina rainawa shi kadai ne gatan da zan nunawa Kamal,  Yanzu wani lokaci ne da Ubangiji ya Kawo mu matukar baka da ilimi to a komai zaka zama koma baya, masu ilimi dasu ake damawa a komai na kasar nan"

Idan taji haka sai hankalinta ya kwanta, harma tayi murmushi tace
   "Toh Malam, Allah ya k'ara maka k'warin gwiwa, Ubangiji Allah ya bada sa'a"

BARA A KUFAI !!Where stories live. Discover now