SANADIN CHATTING

1.8K 96 0
                                    

🌪🌪🌪🌪
           
          🌪🌪🌪🌪

🌪🌪🌪🌪 

*GUGUWAR ZAMANI*
Stream B(ci gaba)

🌐🌐🌐

           🌐🌐🌐

🌐🌐🌐

*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*

Wannan labari ba kamar sauran labarai bane, anyi shi ne domin bada mihimman gudunmuwa, wajen ilmantarwa da wa'azantarwa akan rayuwar da wasun mu suke tsintar kansu a zamanin yanzu, labarin had'in gwiwa ce ta kungiya r brilliant writers association don Haka ba muyi shi dan cin zarafin kowa ba.

*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION🖊*

Written by BRILLIANT WRITERS

Story by: FATIMA USMAN

Page 001

*Tittle: SANADIN CHATTING*

Kwance take kan fad'add'an gadonta da waya a hannunta , tana latsawa sai saki murmushi take saki, da alama tana mutuk'ar jin dad'in chat d'in da take.Da saurin ta duro daga gadon, jin mijinta na kwala mata da kira, wani dogon tsaki taja sannan ta fice daga bedroom tana, fad'i take a zuciyarta shi kenan yanzu bazanji dad'in yin chat ba, dan yanzu zai bi ya takurawa mutum.

Tarar da shi tsaye falon rik'e da briefcase a hannunsa, ransa a mutuk'ar b'ace sai huci yake, kalle ta yi  yace, "yanzu dan Allah  kina ina da kika bari miyarki ta kone?", ya fad'i haka cike da takaici cikin tsananin b'acin rai.

Zumb'uro k'aramin bakinta tayi tace, "haba only kai ma ka san dole sai haka ta faru saboda rashin sabo, shi yasa nace ka nemo 'yar aiki amma ka k'i amince".

Wani irin takaici ya k'ara ji ya kama shi, ji yake kamar ya rufe da duka, yana jin wani tuk'uk'in bakin cikin a zuciyarsa ya kalle ta yace, "Sau nawa kika san na fad'a miki bana ra'ayin d'aukar 'yar aiki yanzu".

K'unk'uni ta shiga muryarta a kasa tace, "to tun da haka ne ka bar takura min man, idan na gaza yin wani abu".

Nan take ransa ya k'ara mugun b'aci ji yayi muddin bai bar wajen ba zai iya controlling d'in kansa ba anymore, komai zai iya faruwa.kwafa yayi sannan ya wuce ta fuuuuu ya shiga bedroom d'insa cikin tsananin b'acin rai.

Bin sa da kallo tare da tab'e baki tare da  d'aga kafad'a alamar bata damu ba, juyawa tayi ta koma d'akinta ta d'auki wayarta ta ci gaba da chat d'in da take.

Yana shiga bedroom d'insa ya fad'a kan gado ragwab, ringingine yana kallon saman d'akin, zuciyarsa cike da takaicin matar tasa, dan ita sam bata san wani abu kula da tarairayar miji, bar ta dai chat a kullum,  sam bata gaji, ga shi kuma shi mai yawan bukata ne, ya so su shimfid'a rayuwar aure abar sha'awa ga kowa, cikin farin ciki da annushuwa tare da nunawa juna zalla love, amma kash!, "Sanadin chat", hakan ya faskara, kamar ba auren love sukayi ba.Nan ya shiga tunanin farkon had'uwarsu.

*Asalin labarin*

Asalin sunansa shine Hafeez Umar Hafeez, amma ana kiran sa da Khaleefa  dan sunan kakansa wanda ya haifi mahaifinsa ne da shi, fulanin Adamawa ne aiki ne ya kawo mahaifinsa Abuja har suka zama acan.Su biyu ne wajen iyayensu shi ne na farko sai kaninsa Ahmad.

Sun had'u da Mimi wajen bikin amininsa wacce amaryarsa ta kasance aminiya ga mimi, yana ganin ta yaji ta shiga ransa dan irin matar da yake so kenan wato wayayyiya wacce zasu shimfid'e rayuwar love da ita, kuma yayi sa'a itama ta kamu da mugun san sa lokaci d'aya.Cikin k'ak'anin lokaci suka iyaye suka shiga ciki, ba tare da b'ata lokaci ba akayi auren nasu amarya tare a had'add'an gidan dake maitama a Abuja.

Saudat Khaleel Yusif shine cikakken sunanta, itama sunan kakarta ne da ita, itama su biyu iyayensu  suka haifa ita da yayanta mai suna Nazir.Mahaifinsu da senator ne, asalin su 'yan Maiduguri, amma a Abuja suke da zama.Sun taso cike gata da sangarta ba kwab'a.

Tun tana gida bata aikin yi sai chat, sam bata san wani aikin gida ba, komai mai aiki ce ke yi mata, saida ta ci ta kwanta, komai na aikace aikacen gida bata sani ba.A cikin wannan halin suka had'u da Hafeez har sukayi aure.Cikin sati biyu da aurensu  ya fara da na sanin aurenta, sam baya samun kulawar daya zata daga gare ta "Sanadin Chatting".

Naunauyan ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama tunanin da yake, tashi yayi ya cire kayansa tare da d'ora k'aramin towel a kugunsa ya shiga band'aki dan yin wanka...

Muje zuwa

Fatinku ce 😘😍

GUGUWAR ZAMANIWo Geschichten leben. Entdecke jetzt