*⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION🖊*
_{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}_*🌍GUGUWAR ZAMANI🌍* _{ƙALUBALEN RAYUWAR MU A YAU}_
_Daga alƙalamin marubutan zamani da suka yi zarra._
'''TURMI NA FARKO'''
*tittle 001:BAYA DA ƘURA*
_{illar zina akan ƴaƴan mazinaci}♣_
*A TRUE LIFE STORY*_*Daga Alƙalamin:SIYAMAIBRAHIM*_
_*بسم الله الرحمن الرحيم*_
*SHAFI NA:3*
_Finale_Ranar girkin amarya ce yau wato Mariya a yau ɗin ne kuma Buba ya mata kaca kaca yayi wucewar sa maɗaɗin ya bata kuɗin cefane sai ya ƙi ya zazzaga mata yayi tafiyar sa,a yau ɗin ne kuma ranar juma'a ranar da ba zai taɓa mantawa da ita ba a rayuwar sa dan yana barin gidan amaryar kasancewar ita gidan ta daban yake da sauran matayen sa su ukun tunda ya aure ta..
Yana barin gidan ta ko rabin hanya bai kai ba Allah ya sauko mai da wata jarabta dan kuwa yana shawo kwanar da zai sada sa da titin da zai miƙe yayi hanyar gidan farkar sa mashin ya ƙwace mai kafin a sani har ya haɗe da wani ɗan a daidaita,sai gashi a ƙasa..
Nan da nan aka taru ana mai sannu amma ina bai san inda kan sa yake ba shi kuwa mai a daidaita yayi gaba abin sa..
Haka jama'an wurin suka ɗauko wayar sa dake yashe gefe suka laluɓo lambar da yayi kira da shi ƙarshe dan ko wayar zamani bai da sai Tecno ta dubu biyar da ɗari biyar itama na hannu ya saya amma farkokin sa waya har ta dubu saba'in sai ya siya masu sutura kam ba'a magana..
Da muntari yayi wayar ƙarshe dan haka aka kira layin aka sanar da shi mai wayar ya sami hatsari yana nan wuri kaza aka mai kwatance...Da hanzarin sa ya nufi inda aka mai kwatancen yana zuwa ya masu godiya ya nemo mai a daidaita suka saka sa ciki aka wuce da shi wata ƙaramar primary health care mafi kusa da hanyar da yayi hatsarin..
Har aka shigar da shi cikin PHC ɗin bai san inda kan sa yake ba,ranga ranga aka shigar da shi aka bashi kujera muntari ya zaunar da shi aka fara ƙoƙarain dakatar da jinin da ke zuba a wasu sassan jikin sa...
Kiran amaryar Buba muntari yayi ya sanar da ita abin da ke faruwa..Allah sarki baiwar Allah sai ta ruɗe girkin da take yi ta rufe har tana ƙonewa da garwashin abin girkin amma bata ji zafin ba ta tashi ta rinƙa kai kawo ta rasa ta ina zata fara sai can ƴar ta ɗaya mai suna Hasiya ta riƙo hannun ta ta ce da ita su je ta sauya kaya su nufi asibitin..
Da taimakon wannan ƴar tata suka kama hanya suka nufi asibitin dan ƴar ma ba ƴar sa bace wacce kafin ya auri uwar ƴar komai ta ce tana so yana mata tun ma kafin ta furta zai mata ga yarinyar da hankali da kawaici dan ta kammala karatun ta har ta fara aiki sannan ya shigo rayuwar su ita kuma ganin mahaifiyar ta na zaune tsawon shekaru goma sha shida babu miji tun bayan rasuwar mahaifin ta sai ta rinƙa tursasa zuciyar mahaifiyar tata akan wannan mayaudarin azzalumin mutumi dan ya nuna ma ɗiyar ya daɗe yana son mahaifiyar ta tun tana budurwa kafin tayi aure Allah bai nufa shi zai fara auren ta ya nunawa yarinyar da gaske yake akan mahaifiyar ta yarinyar kuwa ta dage ta tsaya har sai da ya auri mahaifiyar ta ba wai dan mahaifiyar nata na so ba sai dan ganin ƴar ta ta damu da ita sosai amma bayan wannan basu rasa ci ko sha ko sutura ba,,auren wannan mutumi da tayi sai ya zama kamar farar ƙafa ne a gare ta sana'oin da take yi na siya da sayarwa kamar haɗa kayan ɗakin amarya da siyar da zanuwan gadaje da atamfofi su turaruka da takalma wanda da su suke rufawa junan su asiri ita da ƴar ta haɗe da albashin ƴar in an kai ƙarshen wata duk baƙin cikin ka ba zaka kalli Mariya da ɗiyar ta kace da su matsiyata ba amma auren ta da Buba komai sai ya dawo masu a rikirkice komai ya tsaya cak babu gaba sai baya tun ana karame karame har aka haƙura hatta da albashin ɗiyar ma ba wani isar su yake yi ba suka dawo sutura sai mahaifiyar ta haɗa da satar kuɗin sa suke samin damar yi babu takalmin a zo a gani babu hijabai,godiyar ɗiyar ɗaya tana da tsayayyen saurayin da zai aure ta wanda shi ke mata ƙoƙari toh in ya mata alkhairi ne ma take taimakon mahaifiyar ta su rufawa kan su asiri amma lokuta da dama mahaifiyar ta so kai ƙara kotu akan a raba ta mijin dan zama da miji mazinaci mai zargi bai dace ba amma ɗiyar ke tausa ta akan kamar tonawa kan su asiri ne in suka ɗaukaka abin ta dai ƙara haƙuri watarana sai labari...
YOU ARE READING
GUGUWAR ZAMANI
RomanceHadakar labarai kala kala daga marubutan kungiyar hausa brilliant writers association domin fadakarwa da ilimantarwa.