*⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION🖊*
_{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}_*🌍GUGUWAR ZAMANI🌍* _{ƙALUBALEN RAYUWAR MU A YAU}_
_Daga alƙalamin marubutan zamani da suka yi zarra._
'''TURMI NA FARKO'''
*tittle 001:BAYA DA ƘURA*
_{illar zina akan ƴaƴan mazinaci}♣_
*A TRUE LIFE STORY*_*Daga Alƙalamin:SIYAMAIBRAHIM*_
_*بسم الله الرحمن الرحيم*_
*SHAFI NA:2*Iyami,shine sunan dillaliyar dake safaran matan aure ko ma in ce mai haɗa matayen aure da wasu mazajen auren ta hanyar kai masu hotunan matayen da duk wasu cikakkun tarihin matayen da ya kamata mazajen su sani,kama daga masu faɗa a ji,ƴan kasuwa,ƴan siyasa,masu hannu da shuni da dai sauran su waɗanda duk ke da haƙƙi a kan su amma suka zaɓi tambaɗewa da matayen wasu..
A wata yawon su na tambaɗa ne suka haɗu da wannan mutumi mai mata huɗu wato Buba wanda a wurin wannan mata da sunan Ɗan kasuwa take kiran sa dan kuwa ya nuna masu shi ɗin ɗan kasuwan ne kuma a shirye yake da ya masu tumbuɗin kuɗi dan kuwa ya nuna zalamar sa ƙarara na son lalata da matayen wasu,..
Toh dama abin nema ne ya samu su aikin su shine su tallata kawunan su ita da matayen da ke bin ta dan su sami abin duniya ba dan mazajen su sun rage su da komai ba sai dan wata dalili tasu da su suka san ta..
A wannan halayya na Iyami ne wata rana ta kawo ma wannan mutumi wato Buba wanda take kira ita da farkokin sa Ɗan kasuwa wata bazawra mai suna Hafsat wacce ta kasance cikakkiyar fulani ce sai dai ƴar duniya ce dan auren ta biyu bata zama da mazajen a cewar ta basu bata abubuwan duniyar da take buƙata,bayan rabuwar ta da mijin ta na biyun ne wannan mata wato Iyami tayi hooking nata da Buban dan itama Iyamin bafulatana ce sai dai duk idon ta ya gama buɗewa,a baya takan yi abin tana jan baya sakamakon shakkar mijin ta da take ji sai dai tun da ya auro mata abokiyar zama ta ɓalle ƙofar rashin mutumci a cewar ta ai shima wata yake mannewa dan haka itama zata nemi wani a lokutan da baya tare da ita tun daga lokacin ne take sheƙe ayar ta alhalin ƴaƴan ta na nan huɗu mata dukkan su ƴar ƙaramar ba zata wuce 7years ba babbar kuma zata kai 15 dan tana jss 2 kenan a makarantar gaba da primary amma haka zata tsallake su ta tafi yawon tambaɗar ta wai ta tafi yawon campaign ɗin siyasa wasu lokutan ba'a gidan take kwana ba kuma mijin bai iya tankawa toh shima ɗin haka yake tambaɗewa kafin ya ƙaro mata abokiyar zama amma tun da yayi auren bai kuma komawa ruwa ba sai dai sakkayar dake biyo sa wanda ta ɓangaren uwargidan sa hakan ke faruwa bai taɓa tunanin zai kai har haka ba gashi nan ita babbar ɗiyar tata ta saba da maza ba laifi saboda uba yana gidan amaryar sa uwa kuwa tana yawon bulaguron ƴan duniya da na siyasan marasa kwaɓo daga yaran sai su a gida maƙwabta kuwa babu mai taka masu birku dan an san uwar ba mutumiyar ƙwarai ba ce...
Abu kamar wasa fah wannan mata ta rinƙa introducing ma Buba ɗan kasuwa matayen aure kala kala suna tambaɗewa suna sheƙe ayar su kamar su ke da duniyar...
Bayan waɗannan matayen da Buba Ɗan kasuwa ke mu'ammala da su ta ɓangaren Iyami yana nan da wasu matayen auren da yake lalacewa tare da su dan kuwa ba a iya garin da yake kaɗai yake samin matayen watsewar ba har wasu garurukan samin matan yake yi wasu matayen ma aminan juna ne suke ma ƴan uwan su yankar baya wannan bata son wannan ta raɓe sa wannan bata son wannan ta raɓe sa har ma in suka yi waya akan zasu haɗu sai wata ta tambaye sa shin ko yana jin labarin wance sai ya ce ai kawaia manta da ita shi rabon da ya haɗu da ita ai ya fi watanni,sai wacce ke bugun cikin nasa ta rinƙa jin daɗi sai ta kamo hanya ta zo su kama hotel su yi kwanaki suna aikata alfashar su alhalin dukkan su kowa da iyalin sa har ma da ƴaƴan su ga jikoki...Wannan shine kaɗan daga halin fasiƙancin da wannan mutumi ke aikatawa sannan bashi da ranar dainawa ko sanin zuru ba tsoro bane sai dai ƙyalewa dan kama shi ranae da bai yi tsammani ba..
Kaf matayen sa babu wacce bata san yana aikata wannan alfashar ba sun kuma san yana kashewa wasu matan banzan a waje abin da su nasa halalin baya kashewa sai dai wani abin da yake kasa aiwatarwa shine sai dai in bai ajiye kuɗin sa ba,ba uwargidan ba ba ta tsakiyar ba wato inno ba ta ukun ba duk ya kuskura ya ajiye kimanin kuɗin da zai kai dubu ɗari toh inshaAllahu sai sun zabge dubu saba'in zuwa ƙasa,duk wacce ke da girki kuma ya kai kuɗi ɗakin ta toh sai sun sace ita kuwa innon in zai ajiye dubu ɗari toh haka zata sace kaf in yayi magana ta mai banza in ya ishe ta ma ta hau shi da masifa haka zai yi shiru toh haka ma sauran matayen biyu in sun sace yayi magana sai su ƙyale sa haka zai gama bambamin sa yayi gaba ba zai saka su fasawa ba washegari in ya ajiye su sace ba..
Ita amaryar wato Mariya ita ce mai tsoron Allah bata iya sace mai amma kuma duk ita ya fi yiwa ha'inci dan sam bai son sauke mata haƙƙin sa na shi mijin ta ne bai bata abinci isasshe bare kuɗaɗen kashewa dan dama a ƙa'idar sa shi kam bai ma mace sutura sai dai ta yiwa kan ta da kuɗin ta na sana'ar ta wanda ita kuma wannan Mariyar bata saba da haka ba duk aure auren da take yi bata taɓa haɗuwa da mugun miji irin sa ba duk auren da take yi mazajen na biya mata buƙatun ta wannan dalilin ma ya sa ita bata iya mai zarin satar kuɗaɗen sa ba amma har da haka bai san karar da take masa ba sai daga baya da taga abin ita zai cutar sai ta rinƙa sace dubu ɗaya,ɗari biyar har dai wataran ta sace dubu biyar ya ɗaga mata hankali har yana mata barazanar zata gani,tun daga lokacin ta fara ja baya ta tsaya a ɗauke dubu biyu zuwa dubu uku wanda sauran matayen sa ganin wawiya suke mata basu san ita ɗin bata haɗa mai da asire asiren da su suke mai ba dan dukkan su asirce sa suke yi ta yadda in ma wani abin suka yi sam ba zai iya aiwatar masu da komai ba....
ESTÁS LEYENDO
GUGUWAR ZAMANI
RomanceHadakar labarai kala kala daga marubutan kungiyar hausa brilliant writers association domin fadakarwa da ilimantarwa.