*⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION🖊*
_{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}_*🌍GUGUWAR ZAMANI🌍* _{ƙALUBALEN RAYUWAR MU A YAU}_
_Daga alƙalamin marubutan zamani da suka yi zarra._
'''TURMI NA BIYU'''
*tittle 002:* *Rayuwar Maryama*
_*Daga Alƙalamin:*_ *SAWDA EDRISS*
_*بسم الله الرحمن الرحيم*_
*SHAFI NA:4*
*Last page insha Allah*Ban tashi farkawa ba sai akan gadon asibiti na tsinci kaina cikin wani mawuyacin hali wanda yasani fashewa da matsanancin kuka wata baiwar Allah ce dake kusa dani tashiga bani hakuri tana mun nasiha girgiza kaina nashiga yi ina tirr dame hali irin nawa ada inada kafafuna guda biyu ina tafia ina rausaya a saman Titi amma yanzu na nemi kafafu na guda biyu narasa,
babban tashin hankalin dana kara shiga shine fuskana da tayi dameji ta sauya mun halitta ta nakoma abar gudu da kuma a kyama acikin al'umma bazan iya irga shekaru nawa nadauka ina jinya ba sabida nadauki tsawon shekaru ina kwance dan hatta kashi a kwance nake yinshi fitsari ma haka asibitin da suka gaji danine suka sallame ni toh matar da take dan kulawa danine ta daukeni takaini gidan ta dake cikin abakwai,
dan karamin gida ne sosai kuma ginin kasa talakawa ne sosai daga ita sai jikanta na miji me suna dayyabu,
a gidan matar nan me suna Baba kulu nakarasa jinya ta dan sosai take bani kulawa duk da ban gaya mata asalin labarin rayuwa taba,
Saidai tasha tambayana akan manyan kurajen da suke feso mun a jiki masu fitar da ruwa hade da wari, amma ban taba gigin fada mata ina dauke da cutar kanjamau ba,
bayan wani dan karamin jinya da baba kulu tayi Allah ya amshi rayuwar ta a ranan Alhamis da rana wuraren karfe daya,
Nayi kuka sosai nakuma kara shiga cikin matsanancin damuwa,
A tunanina yan'uwan ta da yaran ta zasu koreni a gidan amma sai naga akasin haka dan mallaka mun daki daya sukayi sukace nazauna sabida har a lokacin cikin jikina bai fita ba amma babu me gane hakan sai ni nayi matukar mamaki sosai da cikin jikina bai zube ba sabida bakaramin faduwa nayi ba tunda harna rasa kafafuna,
Rayuwa na naci gaba dayi a gidan baba kulu har zuwa lokacin da dayyabu yabani jari nafara kulkula su maggi dasu gishiri yan kananan abu dai haka,
haka naci gaba da rayuwa na har zuwa lokacin da Allah yasauke ni lafia saidai abunda na haifa baizo da raiba naso kwarai yazo darai kodan nima naga jinina a dunia,
yan'uwan baba kulu sune suke kula dani har zuwa lokacin da nayi kwanaki arba'in da haihuwa,
a rayuwa na babu wani canji ko cigaba dana gani saima cutar me karya garkuwar dan adam data kara bunkasa a jiki na,
Kada kuji ban ambaci labarin Alh Dahiru ba ko Jibril safana ko mutanan gidan mu dalili kuwa duk bansan ainihin ya suke rayuwar su a yanzu ba,
Dan rabo na da ganin Alh Dahiru tun ranan da nafado daga gidan benan shi, Jibril safana kuwa daman tunda na kwanta a asibiti ban kara ganin saba har ila yau,
Mutanan gidan mu kuwa basu neme niba sabida lokacin da mukayi arziki watsar dasu mukayi nida mahaifiya ta dan haka banga laifin suba kuma naji dadi sosai da basu dawo rayuwa taba sabida ina son nagyara tsakani na da Ubangijina na nemi gafarar sa dan nasan Allah gafurur Raheem ne,
Kullin cikin sallah nake da Azumi hade da neman gafarar ubangiji,
Dayyibu shine yafara koyar dani addini na yakuma koyar dani yanda zanyi sallah hade da wankan tsarki da kuma yin sauran ibadu na.
*Anan nakawo karshen Labarin Maryama wanda na dan yanke labarin ne sabida uzuri da sukasha gaba na*
*Allah yasa Labarin Maryama yazama izina ga masu hali irin nata Allah kuma yasa labarin ya fadakar da Al,umma yakuma ilimantar dasu kura kuren danayi Allah ya yafe mun*
*Dinbun godia ga duk wata member dake cikin qungiyar brilliant Allah yabar kauna yakuma hade ka'wunan mu ya kade fitina a tsakanin mu* *Aameen*
*Sawdaedriss*
YOU ARE READING
GUGUWAR ZAMANI
RomanceHadakar labarai kala kala daga marubutan kungiyar hausa brilliant writers association domin fadakarwa da ilimantarwa.