🌪🌪🌪🌪
🌪🌪🌪🌪
🌪🌪🌪🌪
*GUGUWAR ZAMANI*
Stream B(ci gaba)🌐🌐🌐
🌐🌐🌐
🌐🌐🌐
*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*
Wannan labari ba kamar sauran labarai bane, anyi shi ne domin bada mihimman gudunmuwa, wajen ilmantarwa da wa'azantarwa akan rayuwar da wasunmu suke tsintar kansu a zamanin yanzu, labarin had'in gwiwa ce ta kungiyar brilliant writers association ce dan haka ba muyi shi dan cin zarafin kowa ba.
*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION🖊*
Written by BRILLIANT WRITERS
Story by:FATIMA USMAN
Turmi na farko
Page 002
*Tittle: SANADIN CHATTING*
Zuciyarsa cike da b'acin rai da takaici yayi wankan ya fito, yayi saurin shiryawa cikin k'ananun kaya, ba k'aramin k'yau kayan sukayi masa ba, fesa jikinsa yayi da turarruka masu kamshi sannan ya fice daga d'akin.
Kallon falon ya tsaya yi, ganin komai a hargitsa sam ba gyara.Cike da takaici yaja wani dogon tsaki "mtssss", sannan yasa kai ya fice daga falon, ransa a mutuk'ar b'ace.
Yana isa harabar gidan ya shiga motarsa, ya ja ta da gudu ya fice daga gidan bayan maigadi ya bud'e masa gidan.
Gidan abokinsa mai suna Adam wanda shine mijin aminiyar matarsa Mimi, yana isa yayi horn maigadi ya bud'e masa gate, ya danna hancin motar cikin harabar gidan.
"Mai gidan na nan ne?", ya tambayi maigadin bayan sun gama gaisawa da shi.
"A'a baya nan amma bai jima sosai ba da fita", ya ba shi amsa da fad'in haka.
Wayarsa ya d'auko ya shiga kiran sa, saida ya kusan tsinkewa sannan ya d'auka.
Yana jin ya d'auka yace, "Ina kake ina san ganin ka yanzu nan".
"Ka zo ka same ni a sabon gidana", ya fad'a masa haka.Suna katse kiran ya juya ya fice daga harabar gidan ba.
A falon gidan ya tarar da shi zaune yana jiran sa, bayan ya isa gidan.
Bayan sun gama gaisawa ya shiga fad'a masa matsalar da yake ciki na rashin kulawar da Mimi ke nuna masa "sanadin chatting", d'in da
take ga shi kuma Allah yayi shi mai yawan bukata."Hmmmm!, kai dai bari ai ni da kai duk matsalarmu d'aya, dan nima sam bana samun kulawa wajen Zee, saboda halinsu d'aya da aminiyarta, amma ni tuni nayi maganin matsalartawa", Adam ya fad'i haka bayan ya gama sauraran sa.
"Dan Allah ka fad'a min yarda kayi, nima nayi dan a gaskiya na gaji da irin halin ko in kular da Mimi ke nuna min"
"Ka kwantar da hankalinka zan fad'a maka, yanzu nan kuwa, ba komai bane sai mace na samu wacce ke mutuk'ar nuna min kulawa tare da biya min bukatata a
kodayaushe ba tare
da gazawa ba".Ba k'aramin gigita shi ba maganar ta shi tayi ba, amma da yake a matse yake kuma shaid'an ya k'ara k'awata masa abin a zuciyarsa, ya amince da shawarar tasa.Tun daga ranar ya samar masa wata mace wacce ke biya masa bukatarsa cikin tsananin kulawa, wanda ya kasa samu wajen matanshi ta sunna "Sanadin chatting".
*Bayan Wata uku*
Zaune suke gaban likita zuciyarsu cike da fargabar abin da zai fito daga bakinsa.Aikuwa abin da suke gudu shi likitan ya fad'a.Wani matsanancin kuka dukkansu suka fashe da shi, kuka wiwi suke ba mai rarrashin wani cikinsu, nan take suka fara nadaman abin da suka aikata wad'anda matansu ne silar faruwar komai, wani matsanancin tsanar matan nasu sukaji ya mamaye zuciyarsu.Da k'yar likitan ya samu ya rarrashe su tare da kwantar musu hankali suka tsagaita kukan da suke.
Dukkansu saki uku uku sukayiwa matan nasu dan basu amfanin zama da su ba.Ba k'aramin tashin hankali kowacce ta shiga ba ji sukayi tamkar sunyi hauka, dan dukkansu
masifar san mazajen nasu.Zama iyayensu suka suka sa a gaba suka ce suka gaya musu dalilin daya sa suka saki matan nasu har saki uku.Kwashe komai sukayi suka fad'a musu na rashin kulawa da suke nuna musu "Sanadin chatting", wanda hakan yasa kowanensu ya sami mace ya ajiye a matsayin dadironsa.Ashe basu sani ba dukkansu d'auke suke da cutar Hiv, sai daga baya da suka gudu bayan sun sace musu makud'an kud'i, suka rubuta musu takarda wacce ke a ciki suke sanar da su da suje asibiti dan yin test dan d'auke suke da cuta mai kashe garkuwar jiki wato HIV, har zuwa wajen asibitin da sukayi likita ya gwada su kuma ya tabbatar da suna da cutar a jikinsu wato sun zama positive.
Kuka wiwi dukkansu suka shiga yi, zuciyar kowannensu cike da nadama, Mimi da Zee kuwa sai tsine chatting kai dama Social media suke a zuciyarsu, wanda shine sanadin rushe musu rayuwar aurensu.
Nasiha iyayensu sukayi musu tare da nunawa da kowanensu laifinsa, iyayen Mimi kuwa kansu suka d'orawa laifi dan su suka sangarta ta bata tsawatar mata, duk abin da taga dama shi takeyi ba kwab'a.
Suna suna gani suka zama zawarawa ga kuma ciwon HIV a jikinsu, dan sunje asibiti sunyi test kuma sakamakonsu positive, a kullum cikin nadama suke tare da Allah wadai da social media wanda shine sanadin rushe rayuwar aurensu.
Alhamdulillahi anan na kawo k'arshen wannan gajeran labari nawa, ina fatan darasin dake ciki ya isa ga al'umma, kuskuren da nayi a ciki ina rok'on Allah ya yafe min dan dukkan d'an adam ajizi ne.
Wassalam
Fatinku ce 😘😍
YOU ARE READING
GUGUWAR ZAMANI
RomanceHadakar labarai kala kala daga marubutan kungiyar hausa brilliant writers association domin fadakarwa da ilimantarwa.