XI

890 74 14
                                    

Tunda na kalli hajiya sau d'aya ban sake juyawa ba,zamewa nayi daga Kan kujerar kaina a kasa,kici kici nake na zuge zip Amma Dan sharri yaki zugewa

Tsabar tashin ta Ido na Namiji naji hannunsa a bayana zai rufemin zip din,bansan lokacin da na watsa masa wani kallo ba

Jingina nayi jikin kujera hajiya ta zauna ta kalli Saleh tace

"Jeka daukomin kayana"

Fita yayi Yana waiwayena,Ina nan inda nake Ina jiran me hajiya zata ce,Amma ga mamakina sai tayi shiru ta bawa iska ajiyata

Sum sum na tashi na koma d'aki na gyara rigar jikina na dauro dankwalina na sauko

Abinci na d'auko ma hajiya tayi kaman Bata ganshi ba,tv na kunna na zauna a gefe inata sake sake har Saleh ya dawo

Jan akwatin da ya d'auko yayi ya nufi hanyar bene,kiransa hajiya tayi tace

"Ajiyemin a dakunan dake nan kasa"

Tsayawa yayi Yana kallonta,har saida tace

"A hakan Zan zauna a d'aki dake kusa daku?" Ta fad'a Tana nunamu

Sosa keya yayi ya dawo da akwatin ya kaishi bedroom din dake kasa,tashi nayi na gyara d'akin na d'auko abubuwan da na sanya mata a sama na dawo dasu,tunani na fara da Babu gado a kasan ya zatayi?

Ba tareda na zauna ba na hau Shirin abincin dare,daga Ni har Saleh bamu damu da cin abincin dare ba,Amma na Isa na bar gyatuma da Yunwa?

7:30 na Gama komai,zuba tuwon nayi na fita na kaiwa sultana na Santa da son tuwo

Kaman yanda ta Saba ko girkin Rana batayi ba,tuwon ta fara ci tace

"Dan usmanu ya ce min za'a yiwa hajiya gyara tana gidanki ko?"

"Um" na fada Domin banason magana irin wannan da sultana,haka Nan banajin sakewa dukda tana bani goyon bayanta

"Zanje na daddagota ne ta dawo Nan,Banda abin hajiya ita da ta kayyade muku lokacin yin ciki Kuma zata zo ta sakaku a gaba?Ina laifin tazo Nan tunda nayi nauyi Kuma dukkanmu yayanta ne zata fi sakewa,balle ma Ni ba ruwana abinda naso zanyi a gaban hajiya,Amma ke bazaki iya ba"

Dariya kawai naji ta tasomin da na tuna abinda ya faru dazu,gyaran murya nayi na waske Ashe ta lura

"Me ya faru?"

"Me Kika ga"

"Kin fini sani,Allah akwai abinda ya faru,hajiya taga wani Abu ko?"

Fad'a Mata abinda ya faru nayi ta dinga dariya harda tintsirewa tace

"Allah sarki hajjaju karki taso Mata da tsohon gwaurancinta,zanzo na d'auke miki ita ai ko Kya sake"

Cikin sauri nace

"A'a Dan Allah ki barta,tunda tazo tana son karki ma fara,ki barni mu rabu lafiya karki jamin magana"

"To Naji,Amma dai nasan zamanki da hajiya bazaiyi Dadi ba"

"Maybe Kuma mu samu maslaha ba"

"Hm bakisan wace hajiya ba" ta fad'a Tana girgiza Kai "ki gode Allah Baki had'u da mamata ba ma"

Murmushi kawai na mata na tashi nayi Mata sallama na koma gidana,ban samu hajiya a Palo ba saboda haka na shiga kitchen na fara wanke wanke

Bayan na gama muka zauna a palo muna kallo,Yana kujerarsa daban Ina kujera daban,Amma just muke kaman mu manne da juna,dukda hajiya Bata le'ko daga dakinta ba amma mun kasa sakewa

9:30 Daidai na tashi na leka na ma hajiya saida safe,Tana zaune kan darduma tana Jan carbi,hannu kawai ta dagamin na fice na nufi sama

Kafin Saleh ya hawo na cire kayana na Sanya na bacci,tunda na lura mijina na son ganin kafafuna a waje to duk kayan da zan saka Ina tabbatar da bayyanar dasu

NAYI DACE✔️Where stories live. Discover now