XXXXVI

949 80 9
                                    

Zubawa Hadiyya ido Hajiya tayi domin bata ta'ba tunanin jin haka daga bakin Hadiyya ba, ba ma matsayinta na suruka ba ko dan yarintarta.

Hajiya dai tsit tayi kafin ta d'au waya ta kira Saleh sai gashi ya shigo da sallamarsa, zama yayi a 'kasa ya gaida Hajiya kafin tayi magana ya mi'ka mata plate cile da jollof d'in Hadiyya yace "Hajiya nasan akan na'ki cin abinci ne ta kawo 'karata, ki ci abincin kiji ya yake".

Spoon d'in da ya sako a plate d'in ta d'auka tana kai bakinta ta yamitse fuska a haka dai ta tura abinci, 'kayar kifi ce ta fara mata sallama a bakinta, da 'kyar ta tauna abincin ta had'iye sannan tace "to ai ba wula'kanta abincin ya kamata kayi ba gyara zaka mata".

"Hajiya na gyara mata tun ba yanzu ba amma babu wani canji".

Kafin Hajiya tayi magana Hadiyya tace "kai nifa Hajiya rabu dashi idan bazaici abincina ba yayita zama da yunwa damuwarsa ce, akwai restaurant kala kala a titi idan yunwar ta isheshi yaje can ya ci abinsa ko a jikina, ni matsalata shine rashin bani ha'kkina".

Cikin mamaki ya kalli Hadiyya sannan ya kalli Hajiya, gaba d'aya Hajiya ta ma rasa ta inda zata fara, ganin sunyi shiru yasa Hadiyya dafe 'kirji tace "na shiga uku, kardai ba lafiyayye bane kika had'ani dashi, aikwa bazan iya zama ba wallahi, tabd'i jan".

Jikin Hajiya yayi sanyi shi kuwa ko a jikinsa, maganinta kenan da ta'ki Bilkisu yarinya mai kunya, har take mata sharrin tana yawo tsirara a cikin gidanta, yau gashinan ta samu sirika me kawo mata manyan maganganu.

Da 'kyar ta daure tace "Saleh ya kamata kaji tsoron Allah kayi adalci a kan kanka da iyalinka, idan ka tauye matarka Allah bazai barka ba kuma ha'kkinta zai iya kaika wuta".

"U'hum ko kefa, kaji magana daga wad'anda suka san Allah, to kaji dai kuma wallahi kaci gaba da tauyeni addu'a zan maka balbalin bala'i ya sauka akan 'kannenka suma...." Shiru yayi sannan ta canza maganar tace "Shikenan dai Hajiya ni Zan koma, na tafi da abincin ne ko na bar miki ki 'karashe?".

"A'a jeki dashi".

Bayan ta fita Saleh ya tashi shima, kiransa Hajiya tayi tace ya zauna ta tashi, dawowa tayi da tray da shinkafa akai da miyar kifi sai 'kamshi take ga lettuce ga kuma lemon za'ki me sanyi.

Ajiye masa tayi tace "kaci kafin ka fita, zan sa jumana ta koya mata girki Amma maganar ha'kkinta kaji tsoron Allah ka dena tauye mata, idan matarka kake tunanin zata dawo to tayi aure kuma har abada bazata dawo maka ba". Tana gama fad'in haka ta bar wurin.

Zama yayi ya dinga cin shikafarnan kamar yau ya fara ganinta, saida yaci plate guda da rabi sannan ya kora kunun za'ki ya yiwa Hajiya godiya ya fita, rabonsa da cin abinci mai dad'in na yau kwana takwas kenan, tunda Hajiya ta dena kai musu abinci, gashi ya sayi kayan abinci ya jibge babu abinda babu amma sarrafawa ya zama aiki.

Hadiyya na komawa gidanta ta kira mahaifiyarta "hello ammy"

"Na'am 'yar leleta kina lafiya? Yanzu nake shirin kiranki kuwa yayyenki zasu zo gobe".

"Dan Allah da gaske? Aikuwa nima gobe zanzo".

"To Allah ya kawoki 'yar lelen ammynta, bani labari me dame kikayi?"

"Ammy dan kiji nayi farfesun nama ranar nan sannan kinga yanda nake miya da nama zu'ku-zu'ku? Inanan nayi 'bul-'bul dani ina cin nama ina shan madara".

"Kai lallai 'yar lele kina jin dad'inki, Amma dai bakya mantawa da ammynki ko?"

"Eh mana komai naci sai na tunaki, ai goben ma zan taho miki da abubuwa".

"To ki bo'ye dai kar ya gani yace daga aure kin fara yiwa uwarki guzuri banason haka".

"Kai ammy sai ya fita fa sannan zanzo".

NAYI DACE✔️Donde viven las historias. Descúbrelo ahora