XXVIII

801 78 13
                                    

_guys bear with me, ni kaina inaso naga 'karshen wannan mutane amma zanso na bawa su Hajiya last chance, banaso tenure d'in bilki ta juyo ku fara tausayawa su Hajiya, so ku 'kara ha'kuri komai yana tafiya Kan tsari saura kad'an_ 😉😉

Kasa furta komai nayi yace "hajiya tun ranar juma'a na bata kud'in ta kawo".

"Eh ta kawo ai ga abinda ta kawo nan a hannunka".

Kallona yayi yace "Bilkisu".

Muryata tuni ta fara rawa tamkar mara gaskiya nace "boo-boo wallahi na kai". Na fad'a ta yanda shi kad'ai zaiji, sunkuyowa yayi shima yace "boo idan kinkai yana ina?"

"Nima ban sani ba...." Na fad'a gabana yana fad'uwa, me mutanennan suke shiryamin? Me suke Shirin aikatawa haka?.

"Malama karki raina mana hankali, kina nufin hajiya 'karya zata yi masa ne? Menene zamu ribata idan munyi miki 'karya wacece ke? Me kike dashi da har zamu 'bata lokacinmu muyi miki 'karya ko sharri?"

Dakewa nayi nace "nasani banida wani abu da kuke son rabani dashi bayan farin cikina, akan me zan 'boye kud'innan bayan nasan zaku fad'a idan ban bayar ba? Wannan kud'in ba komai bane a wurina cikin mintina biyar dangina zasu iya had'a min ninkin baninkin wannan kud'in tsiyarku ba komai bace a wurina".

"Bilkisu ya Isa" Saleh ya fad'a tareda d'aura hannunsa a kafad'ata, kallonsa nayi cike da tsoro da firgici da takaici nace "boo kana ganin abinda take fad'a, idan na boye kud'innan me zanyi dasu? Sun fini bu'katarsu akan me zan hanasu? Ko hanasu zanyi ai bazan basu ko 'kwandala ba wannan kawai sharri sukeso su 'kullamin saboda son zuciyarsu, kuma Allah ya fisu Allah yana tare da....."

Saukar mari ce ta dakatar dani daga cigaba da maganata, d'ago kaina nayi naga maimuna, nunani tayi da yatsa tace " 'karya kike ki zauna kina zaginmu da mahaifiyarmu mu 'kyaleki 'karamar 'barauniya, ba dai kinada bakin zaginmu ba? Muje gidan naki a duba, idan har akaga kud'innan duk abinda muka miki ke kika janyowa kanki, idan ba'a gani ba kinada ikon zaginmu yanda kikeso tunda mijinki ya nuna mu danginsa bamuda wata martaba da daraja a wajensa ciki kuwa harda uwar da ta haifeshi, saboda yana tareda matar da Bata san ciwon iyaye ba saboda Bata tashi taga nata ba, kuma Bata haifa taji zafin 'ya'ya ba".

Kallon Saleh nayi da ya dam'ke kud'in a hannunsa da alamu ransa ya gama 'baci, sauke numfashi yayi yace "maimuna bakida ikon ta'ba jikin matata akan abinda bamuda tabbas akai, na san cewa bilkisu bazata ta'ba 'kin kawo kud'innan ba, saidai ko mistake tayi ta bar wasu a gida".

"Boo-boo wallahi tallahi duka kud'innan na kawo Babu abinda na ajiye, suna dai niyyar 'kullamin wani abun ne".

"Saleh, nice na haifeka ko kuma bilkisu?"

Kallonta yayi yace "hajiya...."

"Dakata banaso naji abinda zaka fad'a, nasan cewa zakayi bilkisu batada laifi saboda an tsaface ka an lalata maka zuciya baka ganin  kowa da gashi sai ita, ni uwarka da na tsuguna na haifeka zaka kalla kace ina 'karya matarka ce mai gaskiya ko?"

Shiru yayi ya sunkuyar da kansa, 'karfin Hali nayi nace "Hajiya kiyi...."

'dagamin hannu tayi tace "banason Jin komai daga bakinki".

"Wannan dramar taki da wasan kwaikwayonki ya isheni, har mu za'a yiwa kissa da yaudara? Saleh  zamuje gidanka mu bincika idan har anga kud'innan kai kasan abinda zaka yiwa matarka, idan baa ganiba mun yarda daga mu har mahaifiyarmu ma'karyata ne".

Kafin Saleh yace komai nace "na amince muje, idan kunga kud'innan kuyimin duk abinda kuka ga dama". Na fad'a tareda yin gaba dukkansu suka biyo bayana, bud'e gida nayi muka shiga na tsaya ina kallonsu, wani murmushi naga kursum nayi sannan tace "saimu fara da d'akin ta domin bazai wuce anan ta 'boye ba".
Zama hajiya tayi kan kujera su biyun suka bini a baya,
Banbi ta kansu ba na hau bene tareda bud'e 'kofar kasancewar bana rufe gidan da key idan zan fita, Jan doors d'in kawai nakeyi wataran ma da naja main door ta gidan na saka jamlock shikenan.

NAYI DACE✔️Where stories live. Discover now