XVII

842 80 6
                                    

Zuba mata ido nayi na rasa me zanyi, ban sani ba farin ciki nake ko ba'kin ciki? Tabbas zan fi kowa farin ciki da samun Huda a matsayin 'ya, amma ta yaya dangin sultana zasu kar'bi hakan?.

Runtse ido nayi tare da d'aga kaina sama, 'kwalla ce ta zubomin na goge cikin sauri ganin idon Huda a kaina.

" Kar kiyi kuka ki sanya 'yarki damuwa mana "

Ambaton 'yata da tayi ne ya karyar min da zuciya, kuka sosai na saki, 'kirjina naji yana d'aurewa gaba d'aya na rasa inda zan saka kaina saboda emotions, sultana tayi min ba zata.

Gefena sultana ta dawo tana rarrashina, zubamin ido Huda tayi take idonta ya ciko da 'kwalla.

" Ki dena dan Allah bilki karki saka Huda kuka, kinsan ba'a so kana nunawa d'anka damuwarka ".

Shesshe'kar kuka nake tareda sha'kuwa nace,

" Dan Allah ki bari sultana, ki dena fad'amin haka ba komai zuciyata zata iya d'auka ba ".

'Daukan Huda tayi ta ri'keta a hannunta, mi'komin hannu huda tayi ta fara kuka, d'aukanta nayi tare da danne kukana, kwanciyar da huda tayi a jikina saida na jita daban, na d'auki kusan mintina biyar kafin na dawo hayyacinta, duk hankalinsu na kaina na kalli sultana nace

" Meyasa kika min wannan kyautar sultana? Kina tunanin Zan kar'beta da zuciya d'aya ba tare da gudun faruwar wani abu ba? Sultana kyautar d'a ba 'karamar kyauta bace ko 'yan uwana ba kowa ne zai iya bani ba, kuma 'yarki ta fari? Dan Allah sultana kar mu fara abinda bazamu iya 'karasawa ba, kar gaba kizo kice na baki, sultana ko kin bani danginki bazasu bari ba ".

Tsaki taja tace,

" Bilki idan akwai wadda zance ta haifarmin Huda kece, nasani dole zakiyi kokonto akan hakan saboda abinda 'yan uwana ke miki saboda ni, amma wallahi abinda suke yi ba dan ni bane kawai son zuciyarsu ne, na sani saleh tsohon saurayi na ne kuma na soshi kaman zan mutu ".

Usman ta kalla tace,

" Kayi ha'kuri yayana amma inaso na goge zargina daga zuciyar bilkisu ".

Juyowa tayu gareni tace,

" Bilki nasan 'kaddara na kuma yarda da ita, na amince da auren ya usman ne kawai don huce takaici, amma yanzu na godewa Allah domin dalilin auren ya usman na sami gata da soyayyar da inada tabbacin da saleh na aura bazai bani ba, wallahi bilki da zuciya d'aya nake sonki tunda na tabbatar da zuciyarki a tsarkake take, furucin da nayi kwanaki saboda kawai hankalinsu ya kau daga kanki ne, amma hakan bai samu ba, bilkisu idan ban baki Huda ba cutar da ita zanyi, wallahi kinji na rantse tunda nayi cikin huda bana son cikin, laulayin da nayi takaici ne duk ya cikani, ranar kuwa da na haifeta kamar an rabani da 'kaya, ban san isharar da Allah yake son isarmin ba, amma babu soyayyar huda a raina kaman yanda uwa zata ji ga 'ya'yanta, nayi 'ko'karin naga naso huda kamar yanda sauran iyaye ke son 'ya'yansu amma jinta nake kamar bare, ke nifa banda naji zafin haihuwarta zan iya rantsuwa ba 'yata bace, Huda 'yarki ce tunda na haifeta kike bata kulawa, Huda dake ta dace ki taimaka ki kar'beta dan Allah ko na sami nutsuwa a raina, na miki al'kawari ko zan rasa duk 'ya'yan da na haifa bazan sake kallon huda a matsayin 'yata ba, dangina kuma ki barni dasu ni nasan yanda zanyi dasu, amma naki dangin ki musu shela su fara kiranki da maman Huda, har rubutu ma munyi saboda tsaro gashi zaki sanya hannu a takardarnan ".

Bugaggiyar takarda ta mi'komin a ciki an rubuta,

_ Ni Usman Abubakar, tareda matata sultana jibril, mun bawa saleh abubakar da matarsa kyautar 'yarmu surayya abubakar, kyauta ta har abada, bisa ga sharad'in zata ri'keta amana, bazata cutar da ita ba_.

Wurin signing na iyayen aka bari sannan aka sake rubuta.

_Ni Usman abubakar tare da matata bilkisu Ibrahim munyi al'kawarin ri'ke surayya abubakar bisa amana, bazamu nuna mata banbanci ba bazamu cutar da ita ba, komai wuya komai dad'i bazamu maidata ga iyayenta ba_.

NAYI DACE✔️Where stories live. Discover now