XXXII

812 69 5
                                    

Ina tashi daga bacci na turawa sultana message akan ta shiga gidana ta tattaromin kayan Huda, ko breakfast na kasa yi ina zaune jiran zuwan Huda, jikina yana bani wani abu zai iya faruwa domin na tabbata indai hajiya taga Huda baza a kawomin ita ba, fatana Allah yasa Kar su had'u da hajiya duk laifina ne da ban tsaya na d'aukota ba.

Tunda naga 11 tayi jikina yayi sanyi, kiran sultana nayi tacemin ai tun 8:30 Usman ya fita da Huda, "Anya hajiya bata gansu ba?" Na fad'a a hankali "eh to sai ta yiwu hakan amma bari na kirashi, hajiya ba tace ta fita daga harkar Huda ba? Kai Hajiya tanada matsala wallahi".

Tana gama maganar ta katse kiran, bayan mintina ta kirani tace "na kirashi yace Hajiya ta kar'beta, amma Bilkisu dama sakinki Saleh yayi?"

Shiru nayi na kasa amsa mata, "kai amma Saleh yayi kuskure babba, inada tabbacin Hajiya ce ta tursasa shi banda haka Saleh bazai ta'ba sakinki haka nan ba".

Girgiza kai nayi nace "sultana salen da kika sani a kullum ba shine a jiya ba, babu tilas a sakin da yayi min ra'ayinsa ne, saidai kawai nace Allah yasa hakan ne yafi alkhairi".

"Ameen Bilkisu, insha Allahu ma komai zai koma dai-dai ki dawo domin nasan babu macen da ta Dace da Saleh sai ke Bilkisu".

Dariyar takaici nayi nace "mu dena wannan magana Sultana, yanzu shikenan ni da Huda har abada?" Wani hawaye naji ya tahomin, dama me neman kuka.....

Tsaki sultana tayi tace "meye kuma na kuka? Ba dai nace na bar miki ita ba? Huda Taki ce insha Allahu zata dawo wurinki, ko bata dawo ba zata dinga zuwa miki akai akai kar nayi miki al'kawari na kasa cikawa, bari naje wajen hajiyan nagani".

Sallama mukayi muka rabu na sake bin gado na kwanta na fara tunanin abubuwan da suka faru jiya, a dai-dai wannan lokacin aurena ya fara rawa gashi 24hrs kamar ba'a yi ba, Allah abin tsoro wannan duniyar ba komai take ba.

Sallamar mama naji na tashi na zauna tareda amsawa, kallona tayi da ta tabbatar babu alamun kuka a idona tace "baki fito kinyi breakfast ba, yayanki ya shigo kuyi sallama bai ganki ba ya fita".

"Waya muke ne da Sultana, tace za'a kawomin Huda yau kuma wai Hajiya ta hana".

Tashi mama tayi tace "to tunda ta hana ai shikenan karki d'aurawa kanki damuwa akan hakan, kiji da wannan d'in kawai ya isheki yarinya kuma ki bar musu kayarsu, hakan ya nuna ita hajiyar ta fara datse duk wata ala'ka dake tsakaninku, ki fito kiyi breakfast". Tana gama fad'in haka ta fita, tashi nayi na bita a baya nasha kunun gyad'a na koma d'aki, mama Bata takura min ba bata kuma le'ko ta dubani ba ko sai d'aya, da alamu ta lura ina bu'katar space ta kuma bani, hakan kuma yayimin dad'i.

Gani nake tamkar duk matan duniya babu marar zuciya kamar ni, duk wannan abun da ya faru tsimayin muryar Saleh nake, so nake ya kirani a waya ko naji sallamarsa kai ko aike ne yayi domin nasan cewa yana sane da zamana, saidai babu alamun ko d'aya daga cikin wannan zai iya faruwa.

Hawaye ne ya zubomin da na tuna lokacin da na fara son Saleh ta dalilin allurar da nayi masa, tunawa nayi da kalamansa lokacin da Abdul yake wula'kantani, yanda ya nunamin Abdul bai Dace da ni ba, yace "duk Wanda zai sakaki kuka to ki sani baikai matsayin ki zubar masa da Hawaye ba, kinfi karfin haka Bilkisu" meyasa a yanzu na kasa dena zubar da hawaye akan kukan da ka sanyani Saleh? Meyasa kayi iya 'karfinka ka rabani da Abdul amma ka kasa koyamin jurewa rashinka?

Kuka na fara sosai na kifa kaina a cikin pillow, tabbas Saleh bai kai matsayin na zubar masa da Hawaye ba domin ya sakani kuka, amma ta yaya zan tsaida wad'annan emotions d'in da nakeji? A lokaci guda raina na 'kunar an wula'kantani, an tozartani, an kunyatani, ba'a d'aukeni da muhimmanci ba, amma mafi ciwon hakan babu wanda nakeson gani kamar wanda ya aikatamin hakan, zama da dangin Saleh babban hatsari ne, domin a wannan lokacin banida kowa sai shi, shi ya zamemin gatana a kullum yana sake koyamin 'kaunarsa domin dashi kad'ai na dogara, lokaci guda ya janye kafad'arsa ya barni a 'kasa nasan yaya zanyi da kaina, why is love so cruel? Tambayoyi ne a kaina babu adadi da nakeso na yiwa Saleh, meyasa? Meyasa? Meyasa?....shine abubuwan da nakeso na tambayeshi amma Sam babu Hali, yana can yana celebrating rabuwa dani tareda danginsa.

NAYI DACE✔️Where stories live. Discover now