labarina 1

811 32 6
                                    

*☪💗 LABARINA💗☪*

*By*
*SHAMSIYA ABDULLAHI (Mrs Yahaya)*

Wattpad *@UMMUDILSHAD*

👩‍👩‍👧‍👦Muna Tare🤝 Writers Association ✍

✨M.W.A✨

Motto: we stand and Fall together

Dedicated To my lovely mom, thanks for your support, l love you so much mom😍🥰😘dis pages is yours only mom.

Tuna tarwa, Dan Allah mukasance masu kokarin gabatarda azkar din da manzon Allah (S.W.M) Yayi mana umarni, shin kokunsan suratul Ahad tana daya daga cikin nasafe da yamma Kuma ana karanta ta kafa 3?, Allah yabamu ikon Aikatawa Ameeeen🤲.

New Writer........✍

*BISSMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM*

🅿__ 1⃣&2⃣

Tsaye suke da uniform ajikin su na makarantar secondary din dake kantitin cikin makarfi road dake Rigasa,

cikin layin dake kusa da makarantar tsaye suke akofar wani gida, 'yan matane guda biyu dogaye kansu daya, daya daga cikinsu sunanta *Arwa* black beauty ce, round face, kyawawan kwayar ido, yalwataccen gashin gira Dana ido take dashi.

Sannan dayar itakuma farace siririya me kyangaske, doguwar fuska gareta dauke da manyan idanuwa da kwayar ido masu launin Brown, tsararren gashin gira Dana ido kamar wacce akaimata kari Dana kanti, karamin baki gareta dauke da jerarrun hakora fararetas hade da siririyar wushirya a tsakani agefen kumatunta Kuma dimples ke bayyana aduk sanda tai dariya,

sannan gashinta hargadon bayanta yake sauka baki me laushi ga sheki *Khaleesat* kenan

Dariya tayi tace Hummmm kawata kinki barina intafi gida tundazu, gashi yanzu har karfe nawa?

Arwace takalli agogon dake wayar hannunta tace karfe 3:30pm fa kawai,

😳Kai zare ido tayi kafin tace yauna shiga uku agurin *Alaja* wallahi danasan ruwan baze tsagaita da wuriba Dana tafi acikin shi,

keda kikasan matsalarki sannan saboda fadan da Alaja zata Miki sekije ruwa yamiki dukanda se yajamiki zazzabi ko cab!😏 Tabe baki tayi sannan tacigaba da cewa yakamta yanzu ace kinsaba da fadan wannan matar kidena cutar da k

Murmushi Khaleesat tayi sannan tace bazaki taba ganewaba nidai yanzu zoki rakani bakin titi ko achabane inhau inwuce gida Dan wallahi yanzu innace zantafi akafa zankara bata wani lokacinne da setasa andakeni tafada cikin damuwa,

Arwa tace to muje tsaya! tsaya! Kinama da kudin mota kuwa?

Tace inafa kezaki bani kinsan jiya banyi mata cinikin shago yakai 2k ba balle tabani kudin mota yauma akafa nazo,

Arwa tace to jirani inje indakko Miki kokuma kizo mukoma gidan tare inba hakaba Kisha jira danni senama cire wannan uniforms din Dan bazan iya karasawa titi dasu ajikina ba,

To da wani munafuncinne yahanaki cirewa tuntuni?

Khaleesat tafada tare da hararar Arwa, dariya sukayi suduka alokaci daya,

sannan Khaleesat tace Dan Allah jeki fito karki Dade Ina nan Ina jiraki

Shigar Arwa cikin gida keda wuya sega wata katuwar motar kirar Range Rover melaunin ruwan toka ta taho da gudu............ batayi auneba sejin ruwan tabo tayi ya wanke mata fuska tare da uniform din dake jikinta gashi kiris yarage ma yabigeta tai saurin matsawa da harseda takai da tafadi kasa......

Kafin kace meye wannan mutane harsunfara taruwa,.

Bayan yadan Kara gaba kadanne da motar yayi parking. Futowa da gudu yayi ya nufi inda take matsar da mutane ya shiga yi cikin sauri, Kai jama'a abunkallo ba ya kadan gun mutane yafada acikin ransa.

A zaune yaganta, sannu baiwar Allah yafada anatse, yauwa ta amsa dashi dai dai lokacin da take dago kanta sukayi 👀biyu da juna,. Mummunan faduwar gaba ta tsinci kanta tare da shiga wani bakon yanayi daganin irinwannan mayatattun idanuwa nashi,,,,, shima a bangarenshi irin yanayi daya suka shiga...... Sunkai gurin minti daya ahaka suna kallon junansu.

Muryar Arwace tadawo dasu daga Duniyar kallan kallon da suka shiga! Nafadin Subhallahi Khaleesat meyasameki?

Tana magana cikin rudewa,. Amsamata yayi da no bawani abu bane in Sha Allah ba'abunda zesameta tashi kinji sannu, mikewa tayi tareda fadin ba komai Arwa.

Hannu yasa acikin aljihun shi yafito da wani kyalle fari tass yamika mata yace gashi kigoge danttin fuskarki,

sannan yakara da tanbayar Allah yasa dai bakiji ciwoba? Kai kawai ta daga mishi alamar eh.

Dadai yaga lafiya_lafiya kuma jama'ar dasuka taru sunwatse seyacemata sannu Allah yatsare nagaba,.

Se anjimanku nagode, tunda ya wuce bekara ko wai gowaba yaja motarshi yayi gaba.

Abangaren su kuwa Khaleesat ce kemagana tana fadin nikam yau nashiga uku yazanyi? Sannan tawaiga ta kalli Arwa tace ni bani kudin motar inkindakko min inwuce gida

Mene😲? Arwa ta tanbaya tareda bude baki dazare ido😳, aiko kinsan dai bawanda zedaukeki akan mashin dinshi da wadannan kayan masu dattiko.

Dan Allah yakikeso inyinewai Khaleesat ta tanbaya,

Arwace ta amsamata da aiko zuwa za kiyi mukoma cikin gida kiyi wanka inbaki kayana kisa sannan kiwuce gida,

Wai ba kya ganin irin sabon hadarin dake sake haduwane, Kuma kinsani sarai indai bada wannan dattin najema da Alaja ba bazata taba yadda daniba kome zance mata,

karki damu muje Dan gaskiya bazan iya barinki dawannan dattin duk inda kikabi adinga kallonkiba please👏muje nasan in Sha Allah kafin kigama shiryawa yaya *Aahil* yadwo seyakaiki har gida tafada dai dai lokacin datakalli agogon dake daure a hannunta sannan tacr nasan yana hanya yanzu.

Jan hannunta tayi tare da bude gate din gidan suka shige.
~~~~~~~~~~~~~
Direct Fallon kasa suka nufa *Hajiya Asma'u* suka tarar zaune kan kujera tana latsa remote, waigowa tayi takallesu fuskarta dauke da farin glashi sannantace,
A'a Khaleesat dama baki wuceba?....................

Senaji daga gareku sannan zan cigaba da typing🤪 Ina saurare Kuna ganin zeyi dadi kuwa?

*Comments & share*

SHAMSIYA ABDULLAHI (ummu dilshad, Mrs Yahaya)...✍✍✍.

LABARINAWhere stories live. Discover now