LABARINA 8

283 14 0
                                    

*☪💗 LABARINA💗☪*

*By*
*SHAMSIYA ABDULLAHI (Mrs Yahaya)*

My social Accounts👇

Facebook *Shamsiya Yahaya*

Facebook group *Ummu dilshad Novels*

Instagram *@Official ummu dilshad*

WatsApp *07013872581*

Wattpad *@UMMU_DILSHAD*

OkadaApp... coming soon....

👩‍👩‍👧‍👦Muna Tare🤝 Writers Association ✍

✨M.W.A✨

Motto: we stand and Fall together.

*Tunatarwa*

*Allahumma inni amsaitu ushhiduk, Wa ushhidu hamalati Arshik, Wamala'ikatik , Wa jami'a kalQik, Annaka Antallahu laa'ila ha illa'antah Wahadaka laasharikalak Wa'anna Muhammadan Abduka Warasulak*

Wannan addu'ar daya take daga cikin addu'oin mu na azkar din yamma, akwaita a azkar din safe Amma banbancin shine aduk inda kalmar *yammaci* tazo to ta *safiya* ce zata maye gurbinta, Allah yabamu ikon aikatawa Ameen🤲

Dedicated to dukkan mutanen dake cikin group din 
*👩‍👩‍👧‍👦Muna Tare🤝Fans club*love you so much guys😘*

New Writer✍

*BISMILLAHIRRAH MANIRRA HEEM*

🅿_2⃣1⃣to2⃣5⃣

Itadai Khaleesat duk abun duniya ya isheta shiru kawai tayi kanta akasa idanuwan ta cike fal da hawaye, da gudu tamike tashige cikin gida, tana shiga kukane me karfi ya kwace mata tare da jin wani irin radadi acikin ranta.

Bayan taci kukanta ta koshine duk abubuwanda suka faru suka dinga dawowa cikin gwagwalwarta tare da tunani dayima kanta tanbayoyin da basu da amsa, shin wai meyasa Alaja kemata irin wadannan abubuwan, taga dai ita ba Yar farkoba balle ace anamata hakane domin Kara to Kuma ai irin wannan karar ta hausawa ce, Kuma sukansu hausawan sundena kyarar Yaransu wai Dan kawai suna nafari, acikin ranta taketa wadannan tanbayoyin tareda zubar da zafafan hawaye, hakan yayi Dede da fadowar da khalid yayi aranta, nanma tashiga duniyar tunani me zurfi game da irin rayuwar da sukayi a school, da duk wata irin kulawa daya dinga bata, Amma yau taganshi alayinsu Kuma ta tabbatar da yaganta Amma se yanuna bemasan Allah yayi wata halitta mesuna Khaleesat awurinba, to ko me hakan ke nufi?😔.

Wunin ranar haka tayi shi cikin rashin sanin meye abunyi gameda abubuwan dasuka faru, hakanan ma ta kwanta cikin wannan yanayin Kuma tawayi gari ahaka, idanuwan ta duk sun kunbura sakamakon kukan data kwana tana sha sannan gashi bawani baccin kirki tayiba.

Bayan kammala duk wasu abubuwan da sabayine kowace safiya, yauma shago tashiga kamar kullum, alokacin Alaja nacikin gida tana wanka, awannan Ranar Khaleesat tasamu Allah ya temaketa tayi ciniki dayawa, don duk bread din da aka sauke musu jiya ya kare, ga suger duk wacce aka kulla ta kare, dadin dadawa itacen suma ansiya sosai, sakamakon duk unguwar su babu mesaida busheshshen ice inba Alaja ba, duk da ana daminane Amma ita bata bari ruwa yadaki icenta cos ta siya irin manyan yadin tenfol dinnan ne tana rufewa dashi, *Hausawa nacewa duk wani Wanda yasha inuwar gemu tofa baya ga makogwaro yake* to haka dukwani Wanda zeyi murna da cinikin Khaleesat to bayaga Alaja yake, Haka ko tafaru, Alaja nashigowa shagon neman guri tayi tazauna tana zare idanuwa tana neman abunda zatayi fada akai, dade taga bata samuba setace *Ina siniki?* Tafada tana mazurai, jakar kudin Khaleesat tamikamata, tana karba ta kirga taga anyi ciniki me tsoka har 5,500 dasafe kawai, haba baseta Mike tafara rawa tana wakokin yarbawa ba tanata juya duwaiwaka, seda tagama cashewa abunta sanann ta zauna tana fadin, *Ah😲 kheleesah ase kafara samame wayo sose, kene kayi wannan siniki, Ah kafadi kome kakeso yau sanyi maka si mano A'a* tafada tareda Dan zungurin Khaleesat da jakar hannunta, murmushi kawai tayi tadanyi shiru tana nazari, take seeabara tafado mata, ta anbaci sunan Alaja sanan tace abu biyu kawai nakeso, *fada Mona ah* tace nafarko de Ina so Dan Allah kibar maganar doramin talla kokuma kaini shagon iyawo, shiru Alaja tayi batace mata komai ba, sena biyu Kuma inaso kibarni inje gidansu Arwa kawata, *Ah jeka mano kagesesu, yausene saka tafi?* Ni ko zuwa gobene, *No sekatefi yansu mano* , mikewa Khaleesat tayi cikin murna dukda dai Alaja bata amsamata rokonta nafarkoba Amma hakan bewani dametaba tunda zataje gun kawarta  tasan in Sha Allah inde taje zasu samu mafita zakuma ta bata shawarwarin dazasu amfaneta.

Shiryawa tayi tsab cikin Riga da skirt na atamfa fara me ratsin green da Dan baki kadan se gyale fari data yafa, tasa bakin takalmi sannan ta rataya madaidaiciyar jaka baka wacce Arwa tasemusu iri daya, shigar tamata kyau sosai, sannan afuskarta Kuma tayi make up dinta bana haukaba Dan dedetayi Kuma tayi kyau sosai tsantsar kyanta dakuma tsarin halittarta suka Kara bayyna, ba namijiba hatta mace Yar uwatta dazata ganta seta yaba da irin kyandatayi ta tsaru ta fito tas.

Yanzu kam ta kofar gida tabiyo bata kofar shagoba, fuskarta asake tayima Alaja sallama sannan tace zantafi, amsa mata tayi da *toh kheleesah sekadawo do Allah kase muna gesuwa* sanan ta dakko 200 tabata tahu mota, karba tayi tareda yin godiya.

Tana karasawa bakin titi kuwa taci sa'ar samun acaba ta haye se gidansu Arwa.

Tana Kai wa kofar gidansu Arwa dinne bayan ta sauka tana bashi kudi sega Aahil yafito daga gida da alamade banisa zeyi ba Dan akafa yake, juyowarda zatayine suka fuskanci juna kiris yarage suyi karo *Subhallahi* Khaleesat tafada tana kokarin kaucewa, shima kaucewar yayi tare da zuba mata ido kyar yana kallonta gani yayi tayi wani irin masifaffan kyau jiyake kamar ace gobe za'a daura musu aure, wani irin yanayi yashiga me wahalar fassarawa, be ankaraba tsintar kanshi yayi cikin duniyar kallon kallo tare da shiga duniyar tinanin San kasancewa da ita arayuwar shi ta har abada, kasa kauda kanshi yayi, gashi tana magana yana kallon pink lips dinta Amma besan metakecewa burgeshi komai nata yakeyi yakasa controlling kanshi, Yaya Aahil yi hakuri wallahi banganka bane!!! Tafadi haka yafi 5× kafin yadawo daga cikin duniyar tunani, na'am Khaleesat yakike, Eh  Arwa naciki momi ma tana nan, yana gama fadin haka cikin jin nauyi yayi sauri yajuya yatafi batare da ya Kara ko kallonta ba, binshi tayi da kallo sannan mamakin shine yayi matukar kama Khaleesat ganin yadda yayi behaving yanzu bahaka yakeba, ummmm Allah dai yasa lafiya, tafada tareda bude gate din tashiga ciki.

Zaune ta tarar da Arwa a tsakar gida kan farar kujera hannunta dauke da waya,

Sallamar da Khaleesat tayi ne yasa taisaurin dago da kanta tareda amsa sallamar, tana ganin itace ta taso da gudu tana fadin oyoyo sister rungumeta tai niyyar yi, tureta Khaleesat tayi tana fadin ni dalla matsa karki yaddani inda kindamu da kiganni da baki biyoniba.

Allah sarki wallahi Kinga nan da kika ganni azaune pics dinda muka dauka a school nake kallo Ina hirarki araina, Kuma wallahi kitanbayi yaya Aahil makiji dazunnan da sasassafe yazo yake tanbayata wai shiko tunda muka gama exam be kuma ganinki agidannanba wai inbashi number ki yakira kugaisa nace mishi bakida waya, kuma kinzo last week lokacin baya gida.

Ke atakaice dai har mun yanke shawarar gobe ko jibi zamuje gidanku, yanzunnan ma ya fita wai ze tsallaka bakin titi wancan shagon seda wayoyin ya semiki waya inkuma be samu irinwacce tadace ba to gobe zeje kasuwa, Dan yau yace ba inda zeje da mota wai hutawa zeyi.

Ke haba naji Ni duk kin isheni da surutu, ya isa hakanan karki karar da maganganunki tunkafin kitsufa zasu Miki amfani nan gaba, dariya suka kwashe dashi dukkan su alokaci guda, tareda rike hannun junansu suka nufi Fallon kasa babu kowa a Fallon, Ina momi? Ina tunanin kamar tana wanka Dan yanzu suka dawo daga dakin motsa jiki ita da dadi, A'a dama dadi yadawo shine kokifadamin, hara rarta Arwa tayi sannan tace ta Ina zan fada miki bayan baki da waya? Itama Khaleesat din hara rar Arwa tayi tana fadin aikin San dayake Alaja bata da wayane.

Yanzu daj kiyi hakuri naji nayi lefi Arwa tafada tareda hade tafukan hannayenta guri guda sannan takara da Afuwan🙏.

Naji na hakura Khaleesat tafada tareda rike hannun Arwa tana janta tareda cewa, zoni kirakani ingaida dadi da momi, kwace hannunta tayi tana fadin ke kamarfa kowannensu yashiga wankane , nizomuje insun fito kwa gaisa.

Bayan sun shiga dakinne sunnemi guri sun zauna, shiru ya ratsa na tsawon dakiku 40 ne, Sannan Arwa tace ya gajiyar ranannan , babu gajiya, sannan tace ke bayan tafiyar ki da kwana 3 base ga Al_Amin Yusuf yakirani  yana tanbayata ba, wai Ina gida? Nace mishi eh bayan mintunan dabasufi 15ba segashi cike da abokananshi a mota mundade muna hira dashi key dinshi yaba abokannashi suka tafi yawo da motarshi, nikuma har tsakiyar gidannan nace yashigo, ke yafara tanbaya na wai kina lafiya, nace mishi kina nan lafiya kalau, sai Kuma yake cemin wai Dan Allah inkina dawaya inbashi number ki Ni Kuma nace baki da ita, secewa yayi wai inkaishi gidanku watarana Mana.

To kekuma mekikace mishi? Cemishi nayi to zannemeki muyi magana inkin amince se inkawo Miki shi,. Cab karkifara wallahi ko hanyar gidanmu ke bama hanyaba ko sunan layinmu bance kifada mishiba balle ma kiwani kwaso minshi haka kawai kijamin masifa gurin Alaja ko kuma kija tadaga waya ta kirawo kaninta *uncle Alfa* mijin *Anty iyawo* me robobi yadakeni, inkuma bansamu dukaba kisa tace zata bama Al_Amin din aurena Kuma gashi dan yaro......

*Comments and share*

*SHAMSIYA ABDULLAHI (ummu dilshad Mrs yahaya)...✍*

LABARINAWhere stories live. Discover now