LABARINA 29

439 18 6
                                    

*☪💗 LABARINA💗☪*

*By*
*SHAMSIYA ABDULLAHI (Mrs Yahaya)*

My social Accounts👇

*Facebook group https://www.facebook.com/groups/703796023429534/*

FB Account *https://www.facebook.com/shamsiya.yahaya.1*

Instagram *@Official ummu dilshad*

WatsApp *07013872581*

Wattpad *@UMMU_DILSHAD*

*OkadaApp... coming soon....*
~~~~~~~~~~~~~

*Dedicated to:
Mahaifiyata Allahu subhanahu wata'ala ya karamiki lafiya da nisan kwana me albarka, uwar Alkairi.
Me gidana angona bbn Islam, Dilshad, da Abubakar sadik (Mr yahaya) so da kauna tsakani da Allah, Allah ya Kara kareminkai ako ina.
Ta hannun dama zeenat, ummu Aslamiyya, sis fa'iza, sis naja'atu, zee musty, my ummu janan, ummu saif & safeena, uwani koko jinjina ta musamman, Asmoo tamu (Asma'u Aswaku), da duk wani masoyin wannan book din dake watsapp, sekuma jama'ata ta Facebook Ina godiya sosai, musamman members din Ummu Dilshad Novels group, da lates hausa novels, innace zan lissafoku duka rubutu yayi kadan gurin bayyana godiyata, da masu comments da masoya marsa comments Amma suna bina suna karantawa duk nasanku Kuma Ina godiya mara adadi.
Thanks once again for your love, care and support.🤝

*🌐AMAZING WRITERS ASSOCIATION* ✍

*✨A.W.A✨*

*we entertaing, educate, stand and fall together, cos your dream is our.🤝*

Seda aka dauki tsawon lokaci suna jijjiga wadanda suka Suma Amma babu Wanda keda niyyar farfado wa acikinsu, Dan hakane Maryam taje ta debo ruwa ta mikama Hajiya Amina, tana karba ta yayyafama umma take ta farfado tana fadin Alhamdulillah!!! Seda tafada ajere yafi so goma Sannan Hajiya Amina takamata ta zauna akan kujera, tayi shiru tana Kokarin tattaro natsuwarta, ita Kuma mom din komawa tayi gurin khalid Wanda kanshi ke tallafe akan hannun Khaleesat tanata famar kuka, tana zuwa shima ta yayyafa Mai ruwa take ya farfado, shima da salati abakinshi yafarka cankuma yafara yima Allah godiya su dad da Abban Maryam ne suka kamashi suka zaunar dashi akan kujera, anan dakin yadaushiru na Dan mintuna.

Abban Maryam ne yayi gyaran murya Sannan ya waiga  yakalli khalid yakoma yakalli matar tashi, yace khalid, anatse khalid din ya amsa da Na'am, menene yajamaka wannan tashin hankalin haka da har seda kasuma, Wanda yajawoma itama Hajiya Hauwwa'u hartakai ga suman itama?.

A sanyaye ya daga kanshi ya kalli Abba yace Abba Dan Allah inaso kafin inbaka amsarka kabani dama inkara neman afuwa agurin Khaleesat na dukkan abubuwan Dana Mata, sannan Kuma komai yafaru tsakanina da ita nahanata tafadama kowa Dan Haka nida Kai na yau zan Fadi komai kowa yaji, shiru dakin ya Kara dauka Babu Wanda yace komai se Abba dayace muna jinka anbaka dama, khalid yacigaba da magana, anan yabada labarin duk wata irin muzgunawa dayadinga yima  Khaleesat Wanda kowa awurin seda ya tausaya Mata to Amma Banda Maryam, ita murna ma kawai takeyi tana ganin cewa saboda ita Khalid din yayima Khaleesat din haka, seda taga khalid din ya duka kasa gaban Khaleesat Yana kuka Yana fadin Dan Allah Ina rokonki da kiyafemin dukkan abubuwan danamiki domin kuwa kece wacce nake nema kece wacce kullum nakwanta senayi mafarkin rayuwar mu tabaya dake Wanda bada wannan fuskar taki ta yanzu nake ganinkiba shine babban dalilin dayasa bangane kebace Kenan, anan fa Maryam taji wani irin mugun bakin ciki da ta kaici, tamike tabar Fallon, tashige daki tanata kuka. Khalid yacigaba da magana Yana fadin,
Kuma Khaleesat bashine asalin sunankiba, Sunanki na ainihi *Maryam (jummai)*.

Khalid Yana zuwa dedenan a maganar shi, Kan Khaleesat yakara kullewa, rike mishi hannutayi cikin yanayin kosawa tana fadin nayafe maka tashi kamin bayani domin awannan maganganun dakakeyi ban fahimci komai daga cikiba, tashi yayi ya zauna kan kujera yace muga gwiwar hannunki, be tsaya tayi magana ba yakama hannunta na dama, ya daga hannun rigar Sega wani makeken tabo ya bayyana, da sauri ya waiga ya kalli su mom yace wallahi itace, anan Khaleesat takara shiga rudani tana fadin Dan Allah kuyimin bayani Mana Kuna nufin kunsan suwaye iyayena kenan?, Shiru kowa yayi se khalid ne keta cigaba da fadin itace ga tabon ciwon da taji Nan ana igobe za a tafi da ita.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Dec 09, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

LABARINAWhere stories live. Discover now