LABARINA 16

266 13 0
                                    

*☪💗 LABARINA💗☪*

*By*
*SHAMSIYA ABDULLAHI (Mrs Yahaya)*

My social Accounts👇
FB Page *https://www.facebook.com/UmmuDilshadSmilebeauty/*

FB Account *https://www.facebook.com/shamsiya.yahaya.1*

FB group *Ummu dilshad Novels*

Instagram *@Official _ummu _dilshad*

WatsApp *07013872581*

Wattpad *@UMMU_DILSHAD*

*OkadaApp... coming soon....*
~~~~~~~~~~~~~

*Dedicated to my fans Love you all😘😍*

*👩‍👩‍👧‍👦Muna Tare🤝 Writers Association* ✍

*✨M.W.A✨*

*Motto: we stand and fall together .*

*BISMILLAHIRRAH MANIRRA HEEM*

*Tunatarwa*

*Allahumma innee A'uzubika minal kufri, Wal faqar, Wa A'uzubika min azaabil qabir, Laa'ila ha illah Antah*

Wannan addu'ar daya take daga cikin addu'oin mu na azkar din safe da yamma ana karantata kafa 3 safe da yamma koyarwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad sallallahu Alaihi Wasallam, Allah yabamu ikon aikatawa Ameen🤲

🅿__6⃣1⃣To6⃣5⃣

Dole Alaja ta hakura da aiken da tayi niyyar yima Khaleesat, sakamakon matsanancin zazzabi da ciwon kan da ta tashi dashi, harseda takaita chemist Amma 1k din data bata takarbe, duk da masifa irin ta Alaja seda ta tausaya mata, yana yin yadda taga jikin nata,  Dan koda Tasha magani be saukaba harseda tayi 3 days ahaka, sannan tasamu ta warware, a day 4 ranar Monday da sassafe ta kuma bata 1k, sannan ta hada mata da wasu takaddu guda biyu, daya direction din Address din inda zatane, dayan Kuma card dauke da sunan Alhaji Isma'il Sulaiman dakuma number waya ajiki.

Karba tayi tareda tanbayar Alaja da cewa wannan namenene? Setace mata *katefi mono ah, saka sigaba da karatu mano, ko bakasone?* Inaso, ta amsa atakaice, *to tasi katefi, inkaje seka nuna wannon card kafin saka samu kasiga gidan, sakayi wanke wanke musamu kudi kayi karatu, masu kudine sose, kayimusu biyya fah toh*.

Wani irin mugun faduwar gaba Khaleesat ta tsinci kanta aciki, Kai jama'a wanke wanke Kuma,wato shine maganar danaji sunayi kenan da me koko?. gaskiya Kam muna bukatar kudi, musamman kodan saboda karatuna Dana kanwata Raliyat, tunda shide Wasiwu yaki karatun, kuma inde banyi abunda taceba tabbas seta doramin talla, kokuma zaman shago nikuma gaskiya bazan iya kodaya daga cikiba, gara gara wanke wanken hakanan dole zanje bani da wani zabi, Allah yasa haka shine mafi Alkairi. Acikin ranta take magana.

Masifar da Alaja tacigaba dayine yasa tadawo daga zancen zucin datakeyi, *basaka tasi bane? Inbasaka je wanke wanke ba seka tafi tallan biredi ko sagon iyawo, Ah*.

Jiki Babu kwari tawuce, tabi kwatancen dake jikin takaddar, yanayin yadda go slow yayi yawa yasa bata samu ta isa da wuriba, hartakai misalin 9Am, tana zuwa ta tarar da wani mutum abakin gate din gidan, gidane babba Kuma na sama gate din ma abin kallone, Allahumma Arziquna rizqan thayyiban, tafada afili sannan tace Allah kabani ikon ginama Alaja irin gidannan Dan tunbayan rasuwar mahaifin mu ita taketa dawainiya damu, sannan ta kwankwasa, wani matashin dattijo ne Wanda be wuce 39 years ba tanbayeta, yarinya lafiya? Kallon card din hannunta ta kalla sannan tace Ina neman gidan Alhaji Isma'il Sulaiman ne, yace ba nan bane, wancan ne, ok nagode.

Seda taje kofar dayan gidanne sannan taga Ashe itace bata kalla number da kyauba, tana bugawa Sega wani dattijo yafito kanshi yasha nadi irin na buzayen Niger, yana hausa irin tasu, yarinya mekikeso? Take ta dakko card din tabashi ya karba ya duba sannan yace kece wacce namiji yace min Zaki iya zuwa acikin wannan makon kenan, bude mata gate yayi sannan yace shigo Amma gidan Babu kowa se Amrat tana ciki, karbar card din tayi tashiga tareda amsawa da toh nagode.

LABARINAWhere stories live. Discover now