*☪💗 LABARINA💗☪*
*By*
*SHAMSIYA ABDULLAHI (Mrs Yahaya)*Wattpad *@UMMUDILSHAD*
👩👩👧👦Muna Tare🤝 Writers Association ✍
✨M.W.A✨
Motto: we stand and Fall together.
*Tunatarwa*
*Allahumma Anta Rabbee laa ilaha illaa 'antah, kalaqtani wa'ana abduka, wa'ana alaa Ahdika wa'wa adika masta da'atu, a'uzubika min sharri maa sana'atu, abuu'ulaka bini'imatika alayya, Wa'abuu'u bizanbee, Fagafirlee fa innahuu laa yagfiruzzunuba illah Antah*
Wannan itace sayyadil istigifari👆tana daya daga cikin azkar nasafe Dana yamma Wanda fiyayyen halitta (S.W.M) yayi Mana umarni da yinsu, Kuma wannan addu'ar warakace daga kowace irin damu, cuta, talauci, rashin haihuwa, da dai sauransu indai mutum ya lizimci yinta in Sha Allah, zesamu duk abun da yaroki Allah indai Alkairi ne Agareshi, Allah yabamu ikon aikatawa.Ameen🤲
Dedicated to, my lovable children, Anty Islam babbar kawata(Halimatu),. Anty dilshad (Hauwa'u),. Yara masu sunan iyayen mahaifansu🥰😍😘 sannan karaminsu babbansu Sadauki Abubakar siddeeq, love you all🥰, Allahu subhanahu wata'ala yakareminku yarayaku yamuku Albarka, Ameen🤲.
New Writer.......✍
*BISMILLAHIRRAH MANIRRA HEEM*
🅿__7⃣&8⃣
*WACECE ALAJA ATAKAICE*
*ALAJA* bakace me matsakaicin tsawo, bayerabiyace fuskarta dauke take da tsage irinna kabilarsu *YARBAWA*,
Tana da yara guda biyu mace da namiji sunan namijin Abdul'wasiyu Amma anakiranshi da *wasiwu* Dan shekara 21 ne ayanzu.
Macen Kuma sunanta *Raliyat* Yar shekara 12.
Namijin shine babba tahaifeshine awani gidan ma'ana shi Dan mijinta nafarko ne *Alhaji Abdul- Fatah* kasancewar ya aureta lokacin bashi da komai ta matsa mishi seyarabu da ita bayan Allah ya azurtasu da *wasiwu* yana sonta ahaka ya hakura yarabu da ita domin bazata taba bari yasamu kwanciyar hankaliba saboda ita macece me kwadayi shikuma bashi da komai,
Bayan rabuwarsu da wasu Yan lokutane Kuma se Allah ya azurtashi, taita kokari takoma shikuma yaki tunda yariga yasan baza a taba zaman lafiya da itaba domin bashi takesoba Dukiyarshi takeso.
Ana hakane tasamu ta auri want me kudi *Alhaji Abdul-Hakeem* mekudine sosai domin Dan kasuwane yana saro atamfofi a kasashen waje, bayan daya aureta har wasiwu yakai shekaru 6 Kuma tazo dashi gidan yana da shekaru 3 ne, Amma ko bari bata tabayiba shikuma Alhaji yakasance mutumne me son yara, yanata addu'ar Allah yabashi haihuwa Amma shiru dayake lokacin beyiba, kwatsam Ranar wata jumma'a yadawo daga masallaci yana tafiya akafa yaga wata jaramar yarinya acikin layin lokoja road tanata kuka Wanda a shekarunta bazata wuce 3ba dauke da wata jaka karama ahannunta yadauketa yatafi daita gidanshi yakaima Alaja ita, bayan isarshi da ita gidane suka tanbayeta sunanta tace *Khaleesat* tundaga wannan amsar databasu duk tanbayar da akamata bata saniba, inkuma aka tanbayi sunan iyayen ta setace dady da momy, bude jakar Alhaji Abdul-Hakeem yayi seyaga ribbons ne da bit masu kyau se mankitso da Kuma wani hoto guda daya medauke da mutum biyu ajiki namijine da baze wuce 11years ba rike da hannun Khaleesat dukkansu sunyi dariya se sukayi kyau sosai a hoton, daya tanbayeta setace yaya, nantake Alhaji Abdul-Hakeem yai ma Allah godiya yacigaba da riketa tareda Dan Alaja wasiwu, shike musu komai nakaratu da dukkan bukatun yau da kullum.
Ikon Allah !!! Bayan samun Khaleesat da shekara 1 Allah ya azurtasu da samun ya mace wato Raliyat.
INNAA NILLAHI WA INNAA ILAIHIRRAJI'UN, 😢😭 Ranar wata litininne daya ga cikin abokan kasuwancin Alhaji Abdul-Hakeem yakira lambar telfon din gidan Alaja yana sanar mata sakon mijinta yayi hatsari yana nan a *Yusuf Dan tsoho hospital (Asibitin dutse)* atake tafadi kasa a sume, wasiwu ne yaje yadebo ruwa ya yayyafa mata, bayan ta farfadone taga wasiwu da Khaleesat a kanta sunata kallon ta alokacin Raliyat tana bacci bamatasan abundake faruwaba Dan bazata wuce 2years ba.
Bayan kwantar da Alhaji da kwanaki 8ne Allah yadauki rayuwar sa😢, Allahu Akhubar, Allah kaimana kyakkyawan karshe.
Haka Aka gama zaman makoki aka tashi, shikenan yanzu babu Alhaji, me daukan nauyin gidan shi dama Wanda banashiba, harma da jama'ar unguwa Dan asanda yake raye hatta makota suna shaidawa da kyauta da kyautatawa irin tashi.
Bayan 40 darasuwarshi sega masu binshi bashi kama daga kan bankuna, abokan sana'arshi dama wadanda ba'asandasuba duk sun yunkuro, kilama wasu karya sukeyi, ahaka duk aka kwashe kaso masu yawa daga Dukiyarshi sekadan aka barma, Yan uwanshi, matarshi, da yarshi, suka raba gado, Alaja da yarta Raliyat sunsamu gadon babban gidan saman dasuke ciki Wanda daga baya bukatun yau da gobe yajawo suka saida mafi kyau daga bangaren gidan.
Wanda ayanzu a bq suke tai mishi gyara, ta ja jari da ragowar kudin tabude shagon provision da Kuma saida itace akofar shagon, domin cigabada daukar nauyin karatun yara.
Daga sanda aka tsinci Khaleesat zuwa yanzu shekara 15 kenan Dan ayanzu tana da shekara 18.
*Comments and share*
*Shamsiya Abdullahi (ummu dilshad Mrs yahaya)........✍✍*
YOU ARE READING
LABARINA
Teen Fiction*LABARINA* kagaggen labarine gameda wata baiwar Allah, mesuna Khaleesat, wacce ta bace tuntana da shakara 3 ba'agantaba sebayan shekaru 17 bayan tayi aure, kubiyoni kusha labari.