LABARINA 7

226 17 1
                                    

*☪💗 LABARINA💗☪*

*By*
*SHAMSIYA ABDULLAHI (Mrs Yahaya)*

Wattpad *@UMMUDILSHAD*

👩‍👩‍👧‍👦Muna Tare🤝 Writers Association ✍

✨M.W.A✨

Motto: we stand and Fall together.

*Tunatarwa*

*Radiitu billahi Rabba Wabil Islami diinah Wabi Muhammadin Sallallahu Alaihi Wasallam Nabiyya*

Wannan addu'ar daya take daga cikin addu'oin mu na azkar nasafe Dana yamma ana karantata kafa 3, koyarwa fiyayyen halitta manzon tsira Annabi Muhammad sallallahu Alaihi Wasallam, Allah yabamu ikon aikatawa Ameen🤲

Dedicated to, dukkan Masoya wannan littafin na LABARINA aduk inda kuke a fadin duniya, Ina godiya sosai. Allah yabarmu tare.

New Writer✍

*BISMILLAHIRRAH MANIRRA HEEM*

🅿_1⃣6⃣to2⃣0⃣

*WANENE KHALID A TAKAICE*

*Alhaji Isma'il Sulaiman* shine mahaifin khalid sekuma *Hajiya Amina* itace mahaifiyarshi , Allah ya azurtasu ne da yara guda 2ne dashi khalid din sekuma kanwar tashi Amrat Wanda akwai tazarar shekaru 11 atsakaninsu.

Alhaji Isma'il Sulaiman babban dankasuwane me sana'ar gwanjo agarin kaduna Wanda sunkafara shida abokin shi mesuna *Alhaji Usman Aliyu* Wanda sunkafara sana'arne a baro tunbayan da suka gama karatu amma dayake Allah ya albarkaci sana'ar tasu yanzu kaf fadin garin kaduna sune suke rabama duk Yan kasuwar bacci data kawo dama dukkanin kasuwannin da ake cin abinci da sana'ar gwanjo agarin kaduna.

Tsananin shakuwar dake tsakaninsu yasa sukayi ginin gidajensu iri daya Kuma kusa da juna dahaka Yan unguwa ke Kiran gidajen nasu da sunan Tagwayen gida.

Alhaji Usman Aliyu Kuma yana da mata dayane mesuna *Hajiya Hauwwa'u* Allah ya azurtasu da haihuwar yara ukune Amma yanzu biyune kawai ke raye a gabanta, babbar mesuna *Maryam* sekuma mebinta *Umar*.

Hajiyoyin biyu matan Alhazan biyu suna rayuwa ne cikin zaman lafiya, zumunci da kuma kaunar junansu, kamar yadda muslumci yayi umarni, sannan suna gudanar da sana'ar gwanjo ne irin ta mazajensu acikin gidajensu.

Haka mazajen kesa asauke musu dilolin gwanjo afarfajiya gidajen biyu, haka gidan ke cika aduk sanda aka sauke musu kaya, wani lokacin asauke agidan Hajiya Amina, wani lokacin Kuma asauke agidan Hajiya Hauwwa'u, aduk lokacin da aka sauke gidan Hajiya Hauwwa'u sunfi saurin karewa saboda tafi saukin Kai dakuma hakuri, itako Hajiya Amina tafi tsawwalawa Kuma gata da masifa, sedai duk masifarta Allah besa tana da hassada ko bakin ciki ba, suna tare kansu ahade yake ita da kawarta, matar abokin mijinta, Kuma makociyarta, abokiyar kasuwancinta, sannan Kuma aminiyarta, da irin wannan dangantakar tasucema yasa Hajiya Amina bata da wani buri daya wuce taga tahada tsatso da Hajiya Hauwwa'u, har rokonta tayi dacewa Dan Allah in yarta Maryam tagama secondary School tayadda tabama danta khalid inyaso seta cigaba da karatu agidanshi.

Babu wata matsala Allah ya tabbatar Mana da Alkairi, Amsar da Hajiya Hauwwa'u kawai tabayar kenan.

Sedai abangaren goganna ku kwata kwata shawarar mom din tashi bata mishiba ko kadan baya so, cemata yayi shifa gaskiya tayi mishi kankanta, tayama za'ayi ya auri Yar 15, duk sanda khalid din yafadi haka se mom din tamaida maganar wasa tana dukan kafadarshi tana fadin karfa nangaba kaga yartawa Maryam takara zama Yan mata kace kanaso Dan bazan bakaba, shikuma se yace Allah ya sawwake mezanyi da kwaila, nifa akalla inasone ace ayanzu budurwata takai 18, se hajiyar tabashi amsa da cewa to ai bayanzune za'ayi aurenba inbanda abunka senanfa da shekaru 4 kaga lokacin bama 18 ba 19 zatakai, tunda kaga yanzu tana j.s.s 2 going to 3, aduk sanda mom din tace haka, ko Abinci yakeci tofa yabarshi kenan, in mom din taga ya matsa baya so sedai tayi dariya sannan ta Kara da yaro yarone, Dan tasan ko kadan bayaso ana mishi maganar Maryam, itakuma yarinyar data ganshi harwani boyewa take wai ita alamar kunya🙈, in yaga haka wani lokacin tabashi dariya wani lokacin Kuma tabashi haushi sedai yayi tsaki ya wuce.

LABARINAWhere stories live. Discover now