*☪💗 LABARINA💗☪*
*By*
*SHAMSIYA ABDULLAHI (Mrs Yahaya)*My social Accounts👇
Facebook *Shamsiya Yahaya*
Facebook group *Ummu dilshad Novels*
Instagram *@Official ummu dilshad*
WatsApp *07013872581*
Wattpad *@UMMU_DILSHAD*
OkadaApp... coming soon....
*👩👩👧👦Muna Tare🤝 Writers Association* ✍
*✨M.W.A✨*
*Motto: we stand and fall together .*
*BISMILLAHIRRAH MAANIRRA HEEM*
*Tunatarwa*
*Allahumma Bika'amsainah Wa Bika'asbahanah, Wabika'nahaya Wabika'namuut Wa ilaikalmaseer*
Wannan addu'ar daya take daga cikin addu'oin mu na azkar din safe da yamma, ana karanta ta kafa 1, koyarwa fiyayyen halitta Annabi Muhammad sallallahu Alaihi Wasallam. Allah yabamu ikon aikatawa Ameen🤲
Dedicated to *zaituna* *(ummul Aslamiyya)* kawa Yar uwa tun ana secondary School, inajin dadin yadda kike nunamin so da kauna, kamar yadda nake burgeki nima haka kike burgeni ta yadda kike nuna so da kauna ga wannan littattafan nawa, har tanbaya kikayi ko zaki iya samu akasuwa🤣😂 agaskiya dai babu shi akasuwa saboda yanzu ne nake kan rubutawa, Amma nan gaba kadan zaku samu littattafan dazan fitar dasu kasuwa wadanda sukafi LABARINA dadi, Ina yinki sosai sis😘.
New Writer✍
🅿__4⃣1⃣to4⃣5⃣
Allurar bacci likita yayima Aahil domin ya huta dankuwa tashin hankalin daya shiga yaja mishi jinin shi ya Dan hau Kuma bazeyiwu adiba komai daga jikin Shiba yana cikin irin wannan yanayin.
Bayan yasamu awanni ukune yana bacci, daya farka se aka mishi aune aunen daya kamata komai nashi lafiyalau yake don haka ba'a tsaya bata lokaci ba aka aiwatar da komai, jini aka fara samata, sannan daga baya akayimata dashen kidney, kamar yadda ZulfiQar yayi ma doctor umarni haka ya aiwatar yakirashi yafada mishi bill take yayima doctor transfer, More than abundayayi requesting 5millions yadora akai yace aba iyayen Rabi'a 4 million su cigaba da kulawa da ita shikuma doctor yadauki 1 million, godiya doctor yayi sannan ya shedama iyayenta, anyi sa'a Aahil baya kusa sakamakon yana dakin hutu, Amma duk da haka Nuruddeen yace baza'a karba kudinba mezasuyi da kudinshi cemishi akayi basu da kudin dazasu kula da itane, hakuri doctor yadinga basu da kyar suka karba.
Bayan kwana 2 ne Rabi'atu ta farfado tana bude ido da salati abakinta, sannan sunan Aahil yabiyo baya yadda kukasan yaji Kiran datake mishi segashi yafito yana tafiya yana tangadi da giving set ahannunshi jijjige wa yayi daga bakin drip din yabarshi yanata zuba, yana tafiya igiyar nabinshi, yana shiga dakin momi yatarar abakin gadon takama Rabi'a tasamata filo abaya tana gayara mata zama yana shigowa shima gefan gadon yasamu ya zauna yana fadin sannu Rabi'a, daga mishi Kai tayi alamar yauwa, sunma manta momi na wurin gaba daya idanuwan su sunrufe kallon junansu kawai suke dauke da wani irin yanayi na tsananin so da shakuwa, tareda shiga irin yanayinnan na inba daya tofah daya baze rayuba, suna ahaka har momi tafita taje takira doctor duk basuma saniba.
Sannu Rabi'atu yajikin!!! seda doctor yafadi haka so 4 cikin na 5 dinne yasa suka dawo daga duniyar kanlan kallo me tattare da tsananin shauki da soyayya me tsanani, Kai Kuma Aahil yakamata ka Kara hutawa, meyasa kataso kafito,? Tashi muje maida maka ruwan, Kai ya girgizama doctor alamar No, sannan yace doctor please adawomin da nawa gadon nan kusa Dana Rabi'a ta Inaso inkula da itane, sosai momi kejin tausayin dannata, doctor ayimishi yadda yake so Mana inde zeyiwu nida momi se mudinga kula dasu, Inna wuni se momi ta kwana dasu, Nuruddeen yafada tareda shigowa dakin, yes doctor please ayi haka banaso inyi nisa da itane Aahil yafada cikin yanayi meban tausayi, momi dai kallon shi kawai takeyi tareda mamakinshi kamar bashine yaketa fizge fizge akan cewa Shiba son Rabi'a yakeyiba.
YOU ARE READING
LABARINA
Teen Fiction*LABARINA* kagaggen labarine gameda wata baiwar Allah, mesuna Khaleesat, wacce ta bace tuntana da shakara 3 ba'agantaba sebayan shekaru 17 bayan tayi aure, kubiyoni kusha labari.