NO 1-9

4.6K 153 3
                                    

[10/28, 15:27] Lovly tah 1: *SANA'UL HUSNA*







®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼



*NA*



*UMMU NABIL*

*_Sadaukar wa ga Miss xerks🌺_*



*_ALHMDULILLAH GANI NA SAKE DAWOWA DA WANI LABARIN WANDA NAKE MA ALLAH GODIYA DAYA BANI IKON SAKE DAWOWA ƊAUKE DA WANI LABARIN,INA ROƘON ALLAH YA YAFE MIN KURA-KURAINA DAYA BANI IKON TAFIYAR SHI YADDA YA KAMA TA_*




*NO.01*




Fuskar ta rufe take da mayani baƙi wanda ake kira da niƙab sai rawa take a gefe guda kuma wata mata ce take yin kiɗa yayin da ita kuma take rawa sai wasu yara guda uku ɗaya daga ciki zata kai shekara goma sha biyar ɗaya zata kai shekara goma ɗayar kuma zata kai shekara bakwai.ko wanne kuwa duk fusko kin su rufe take da niƙab hatta ita babbar matar.

Haka take ta faman wannan rawa yayinda sauran yaran da babban macen suke mata kiɗa, gaban wasu mutane maza manya wanda ko wanne daga cikin zai kai shekara arba'in haka kuma acikin su akwai wanda zai ɗara haka da wanda zai wuce haka.sai dariya suke suna shan giya abin su.


Wani kyakykyawan saurayi ne ya fito sanye da suit baƙi,yana tafiya tamkar bazai taka ƙasa ba,har ya karaso inda suke,da zuwan shi ta canja salon waƙar saboda ƙaida ce hakan daya fito ake canja waƙar.



Wata sassanyar murya ta canja mai cike da tausayi ko waye idan yaji waƙar sai ya kusa kuka.shikam shi saurayin kullum idan ta fara wannan waƙar sai ya tuna da wani lokaci na rayuwar sa.


Haka suka gama wannan rawa,ƙarfe biyar saura suka tashi don koma wa gida.


Suna tafe da ƙyar take taka ƙafafun ta wanda suka yi mata nauyi saboda gajiyar da tayi,Ammi ta kalle ta tace,



"Sanah baki da lafiya ne?".


"Ammi wallah gaba ɗaya jiki na ciwo yake banji daɗi ina jin gobe bazan fito rawa ba,zan kwanta na huta inyaso sai ku fito da Widad dasu Samah".ta ƙarashe maganar cike da ƙosawa.



"Ayya ai ko ni da kika ganni nan wallah ƙoƙari nake,toh ya zamu yi,tunda haka Allah ya ɗora mana idan bamu fito ɓa,a ina zamu samu abinci kinga dai ta nan muke samun ci mu samu sha kekam kiyi haƙuri yanzu idan mun ƙarasa idan kinyi sallah sai ki huta".


Widad tace"Ammi wallah da gajiya ai ina ganin Dole ta fimu gajiya ni gaba ɗaya ma nafi tausayin Fidda,ƙarama da ita ama zata taso da wannan mummanun sana'ar irin wannan"Samah ta kalle ta tace,


"Wallah Kuwa bari kekam Allah ya fito mana da wata sana'ar kawai mubar wannan".

Wani zazzafan hawaye ne ya zubo ma Ammi tayi saurin gogewa gudun kar yaran nata su gane halin da take ciki.


Haka da jan ƙafa da komi,suka ƙarasa gida saboda idan suka ce zasu yi kuɗin mota daga inda suke aikin zuwa gida ma kaɗai ya ishe su,sai kuɗin da suka samu kaf ya ƙare basu zo gida ba,shisa suke tafiyar ƙafa.




Sai da suka gaba aikin gida tukun saboda ma suna da yawa nan da nan wannan yana wancan yana wannan shisa suka yi saurin gama wa.

Ita kam Sanah bata tsaya cin abinci ba,sai ds tayi wanka tukun ta shirya cikin riga da wando na pakistan tukun ta zo suka ci abincin suna gama wa kuwa ta shige ɗaki nan take bacci yayi gaba da ita.

SANA'UL HUSNAH          {COMPLETED12/2019}.Where stories live. Discover now