No 10-12

1.1K 53 0
                                    

[10/30, 18:51] Lovly tah 1: *SANA'UL HUSNA*





®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼




*NA*




*UMMU NABIL*

_Sadaukarwa ga Miss xerks🌺_.

*NO.10*




_________📖Hankaɗata yayi ta zube ƙasa,da sauri ta miƙe tsaye tana cigaba da rusa mishi kuka.

"Sai yaune na ƙara tabbatar da cewar baki da hankali, daƙiyaya kawai shashasha ashe rashin hankalin ki har ya kai har haka,yanzu ya kike so nayi da abubuwa masu amfani da nake dasu ciki,ki tabbata idan har nayi loosing wani abun koda guda daga ciki toh kina da kason hukuncin da zanyi maki,kuma bazan barki ki tafi a banza ba,yadda nace zaki yi tsallen kwaɗo nan to saifa kinyi shi"

cikin daka tsawa yace, "shige ki wuce muje" ya ƙarasa faɗa cike da masifa.

Turo baki tayi gaba tare da sharce hawayen dake anbaliyar fitowa daga idanun cikin tsiwa tace,

"Taɓ tsallen kwaɗo kuma sai kace wata kwaɗuwa ko kuma mai zaman barack".

"Me kika ce?".

shiru taƙi basa amsa sai faman murguɗa baki da take ta cikin niƙab, tai ƙiƙam ta tsaya mishi akai taƙiyin abinda kuma ya bata umarnin yi.

kallota yayi yay kanta, ganin yana tunkaro ta yasa tayin baya har sai da ya kaita bango.

Dake zuciyarta tayi don tagama tsorata da yanayinsa, fuskar nan tayi ja ranshi ya gama ɓaci tunanin shi bai wuce wani irin hukunci zaiyi mata ba saboda tsantsar takaici.

goge gefen bakin shi yayi ya kalli yadda jikinta yake rawa tamkar mazari yace,

"Sai rashin ji da ɓarna amma a ɓangaren tsoro kece master yau sai na gyara maki zama yadda ko wani ne bazaki ƙara yima sha'awar ɓarna ba, zan faɗi ma Ammi laifin da kika yimin yadda zan samu damar casaki yadda nake so wuce muje"

tsantsar takaice ne ya rasa ma wata irin kalma zai faɗi mata wadda zata sosa ranta tadaina yi mashi abinda take,tunda ta fara yi mashi ko sau ɗaya basu taɓa shiri ba kullum da abinda zata yi mashi.

Haka ya sata a gaba,har zasu fita da taga dai da gaske ne faɗi ma Ammi zaiyi yasa ta dawo da baya taƙi fita.

kallo yabita dashi yace, "to! ikon Allah, sabon rashin mutunci zaki min, miye na tsayawar?"

ta maƙale kafaɗa tace, "nidai bazani ba, kawai ka hukuntani da kanka"

yace, "to ko sai dai ki zaɓa, wankin mota?tsallen kwaɗo ko kuma kneelling down?"

tace, "ba gwara na wanke mota ba"

yace, "inaaa ai ɗaya yayi kaɗan,biyu zaki ɗauka"

tace, "to naji idan na gama wanke motan zanyi kneelling-down a tsakiyar rana ma"

yace, "better, oya لنذهب"

haka ya tisa ƙeyarta gaba, yasa aka jide mata kayan wankin mota, tako zage tana wankewa haka har ta gama kuma ta fita tai ƙal kace namiji yay aikin.

shiko yana daga zaune gefe can kan resting chair yana kallonta sai faman barƙale baya take alamu na gajiya.

bayan ta gama harta nufi hanyar cikin gida ya ƙwala mata kira yace, "wa kika bari yay maki ɗayan purnishment ɗin?"

SANA'UL HUSNAH          {COMPLETED12/2019}.Where stories live. Discover now