27

634 31 0
                                    

*SANA'UL HUSNA*
   *1441H/2019M.*




®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION*.✍
{  _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira_.}

        '''🎐G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN K'ARFE•🏇🏻*_


*NA*



*UMMU NABIL*


*_Sadaukarwa ga Miss Xerks🌺_*


~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad~@
~GaskiyaWritersAss~.






*NO.27*



*__________*📖Yana buɗewa yagan ta tsaye kamar marar gaskiya,sai da yagama ƙare mata kallo yaga gaba ɗaya kamar a tsorace take yace,

"Bismillah".

Ya bata hanya don ta wuce,ciki ta shiga bata zauna ba ta samu gefe guda ta tsaya.

"Ya dai".

Turo baki tayi tace,"Babu Adda Amina ce tace wai anan zan kwana".

Wani sanyi ne ya ziyarci dukkan sassan jikin shi tare da zuciyar shi,ya kalle ta tare dayin wani ƙayattaccen murmushi yace,

"Okay ga wuri nan".

Kallon gefen da ya nuna mata tayi bakin gado yana nufin anan zata kwanta kenan.

Ɗan gyara muryar ta tayi saboda jin wani yawu daya tsaya mata maƙogwaron ta tace,

"Kai kuma fa".

"Akan kujera".

Kallon kujerar tayi tasan dai bazata ishe wannan jikin nashi ba,ko iya ƙirjin shi ma ai zai kusa cinye kujerar bare ace anan zai kwanta.

"Okay to"ta faɗa tare da zama bakin gadon.

Babbar rigar shi ya cire yace mata,

"Kina da alwala?".

"Eh nayi sallah tun bayan da lokacin ta ya shiga".

"Okay"yana faɗar haka yayi hanyar toilet yayi alwala ya fito ya iske ta inda ya barta.

Sajjada ya shimfiɗa yace ta tashi suyi sallah,tace mashi ita fa tayi sallah.

"Nafila zamuyi mu godema Allah,daya nuna mana wannan ranar"jin haka yasa ta miƙe yaja su sallah.

Suna idarwa ya dafa kanta yayi addu'ar da manzon Allah ya umarci duk wani wanda yayi sabuwar amarya yayi,sannan yace,

"Kiyi mana addu'a".

Ita ma addu'ar tayi.
Miƙewa yayi ya ɗauko wasu ledoji ya ajiye a gaban ta,

"Gashi babu flat kuma".

"a kitchen naka baza'a samu ba".

"Ayya na manta akwai kitchen ma".

Miƙewa yayi ya nufi hanyar kitchen ya ɗauko  Da kofi guda biyu ya dawo.

Juyo kazar yayi da tare da zuba lemo masu daɗi acikin kofinan ya miƙa mata guda yace,

"Bismillah".

"Tun ɗazu naci abinci fa".

"Wannan ai ba abinci ne,kuma shiɗin na daban ne".

"Kamar ya na daban?dama akwai wani abinci na daban?".

"Eh baki sani ba dama?to yanzu kin sani,kuma ki buɗe cikin ki kici da kyau".

"Allah na ƙoshi banjin yunwa".

"Kinsan Allah sai kinci ko baki so bare ma kina so wai irin fulakon nan ko?".

"Hmm bawani fulako na ƙoshin ne kawai".

"Haka zakice kinason na maki ɗura kawai".

"Sai kace wata ƴar baby".

"Dama ai Babyn ce ko baki sani ba?".

Haka a hankali har ya samu taci ama bawani mai yawa ba,bayan sun kammala ta miƙewa ta gyara komi sannan ta dawo ta zauna bakin gadon.

"Ki kwanta mana".

Ita kam ba wani a sake take ba,da an barta tayi baccin ta acan da zai fi mata a rayuwa,ama ance sai ta kwana da ƙato a ɗaki.

"Nikam banson kwanciya anan Allah".

"To ya kike so nayi maki ko na fita a ɗakin?".

Da sauri ta ɗaga kanta alamun Eh.

Ɗan murmushi yayi yace,"To babu damuwa ki kwana lafiya"yana gama faɗar haka ya fita.

Ganin haka ya sata kwanciya tayi addu'ar bacci tare da cire Hijab nata,sosai ta gyara tayi kwanciyar ta.

Can wurin ƙarfe sha biyu na dare ya buɗe ƙofar a hankali gudun kar ta tashi,yayi sa'a kuwa ko motsi bata yi ba.

Bakin gadon yaje ya tsaya tunanin shi kar ya hau ta tashi,a hankali kamar ɓarawo ya hau kan gadon ya kwanta.

Janyo ta yayi jikin shi,yana son yayi bacci ama sam ya gagara tunda yayi ido huɗu da kyakykyawan jikin ta sai yaji hankalin shi gaba ɗaya ya tashi.

Musamman yadda ɗumin jikin ta yake ratsa mashi ko ina na jikin shi.

Hannun shi ya zura cikin kwarmin bayan ta yake shafawa a hankali,wani farin ciki ne yake ziyartar sansanin jikin shi,cikin bacci taji kamar abu yana mata yawo a jiki,baki ta buɗe zata sharara ihu yana ganin haka ya rufe bakin shi da nata.


Wani tsoron ne ya kuma ziyartar zuciyar ta,iya ƙarfin ta ta saka take ture shi ama kamar ba yi take ba,.

Da ƙyar ta samu ya rabu da ita ta shiga rera mashi kuka daƙyar ya rarrashe ta tayi shiru ya shiga bata baki har mai afkuwa ta afkuwa.

Ganin haka yasa nayi waje tare da yi masu fatan alkhairi.....



*BAYAN WATA BIYU*


AYI HAƘURI DA KAƊAN.

#Vote
#Comment
#Share

*UMMU NABIL*

SANA'UL HUSNAH          {COMPLETED12/2019}.Where stories live. Discover now