18

659 43 0
                                    

*SANA'UL HUSNA*








®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION*.✍
{  _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira_.}

        '''🎐G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN K'ARFE•🏇🏻*_




~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad~@
~GaskiyaWritersAss~.





*_Sadaukarwa ga Miss Xerks🌺_*



*NA*




*UMMU NABIL*




*NO.18*




*_________*📖Daƙyar aka samu Hafiza ta bama Ammi baki tayi shiru sannan ta kalle ta tace,


"Haƙuri shi ya dace ga duk bawan da haka ta same shi,Allah yana sane da hakan baya bacci ki kai kukan ki gareshi zaki ga sakayya,kuma ni a gani na kiyi ma Badamasi magana kiji mai zaice shima mamacin rage mashi nauyi ne saboda haka ki tuntuɓeshi kiji yadda zaice maku".

Haka Hafiza tayi ta bawa Ammi shawarwari masu daɗi da sanya nutsuwa a cikin rai har ta samu hankalin ta ya kwanta.

Da yamma bayan tayi sallahr la'asar ta ɗauka hanyar gidan ta.


*BAYAN WATA BIYU*


Tun asuba ko sallah basu ida yi ba,Su Badamasi suka iso gidan gaba ɗaya a gaggauce suka cema su Ammi su shirya zasu yi tafiya,ba ƙaramin mamaki Ammi da ƴaƴan ta suka yi ba ama haka suka tusa su gaba suka shirya.

Basu wani ɗauka kayan kirki ba gaba ɗaya suka azazzalesu,a mota Ammi ta kalli Badamasu tace,

"Bangane ina zaku kaimu ba tun ɗazu nake tambayar ka ama ka gagara bani amsa nifa banson irin haka Badamasi ka faɗi min mana ka ɗebo mu nida yara sai sharara gudu kake damu".

Banza yayi da ita,ya cigaba da tsuga gudun sa babu ruwan sa,har sai da suka isa Airport abin ya basu mamaki Widad ta kalli Sanah,Sanah ta kalli Ammi gaba ɗaya suka yi ta kallon juna.

"Ai dama surprise naso baku kuma gashi kun gani yanzu ku jira anan kafin a kammala komi".

"A kammala Komi kamar ya ina zamu tafi?".

"Zaku koma ƙasar larabawa da zama abin ku nason hakan zai fi maku daɗi sosai".

Gaba ɗaya Ammi ta kasa magana ta rasa ma abinda zata ce mashi,Widad kam sosai taji daɗin hakan ita kam Sanah hankalin ta bai kwanta mata arai ba,haka ma Ammi shiru kawai tayi can tace,

"Ban fahimta da zamu fi jin daɗin can mu dawa iya ka mu kaɗai kake nufi ko kuwa?".

"Ahh akwai wani abokina,kekam ki kwantar da hankalin idan kun sauka akwai wani wanda zaiso ya ɗauke ku mun gama magana hatta gidan da zaku zauna acan ɗin,saboda acan zasu cigaba da zuwa makaranta an riga anyi komi".

Yana cikin yi masu bayani aka fara sanarwa,cikin hanzari ya miƙa mata wata jaka kuɗi ne a ciki dam irin na nan,dubawa tayi tace,

"ban fahimta wannan kuɗin ba ƙasar da zamuje ai ba da irin su suke amfani ba ko kuwa ka manta ne".

"Ohh ban manta ba kekam kuje kawai idan kunje shi wanda na haɗa ku dashi zai san yadda za'ayi kuje abinku"zata ƙara magana da sauri ya figi hannun Samah da Fidda a dole suma suka bishi,suna gama hawa sai ga su Haladu da Halilu ɗaga masu hannu suka yi wani zazzafan hawaye ke bin kumatun Ammi,ita kam bata gane meye hakan yake nufi sam.

SANA'UL HUSNAH          {COMPLETED12/2019}.Where stories live. Discover now