24

715 38 0
                                    

*SANA'UL HUSNA*





®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION*.✍
{  _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira_.}

        '''🎐G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN K'ARFE•🏇🏻*_

*_Sadaukarwa ga Miss Xerks🌺_*


~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad~@
~GaskiyaWritersAss~.



*NA*



*UMMU NABIL*


*NO.24*

Washe gari suna zaune da Ammi suna hira yayin da Sanah gaba ɗaya hankalin ta baya tare dasu,tunanin yadda zata zauna da mutumin bata so shi kawai take,kai ina ma ita akwai wanda take dashi da babu yadda za'ayi ta auri wannan Deen ɗin.

Widad ce ta taɓa ta tace,"Habibty daga yanzu ya kamata mu fara shirin abinda zaki sanya fa a bikin ki"ta faɗa cike da zolaya.

"Aikuwa dai ai wallah Ammi ba ƙaramin tunani tayi ba wallah hakan yayi sosai"inji Samah.

"Hmm yaran nan bakujin kunya agabana kuke maganar abinda ma Sanah zata saka ku tashi ku bani wuri"Ammi tace.

Fita sukayi suna dariya yayin da Sanah ta cika tayi maƙil jira take kawai a taɓa ta fashe.

Ammi ta kalli yanayin ta tace,"Saboda na haɗaki da Deen shine tun jiya baki ci komi ba aikin da kike ma kika bari saboda baki son lada ko?".

"A'a ni babu komi".

"Akwai komi tunda rana ɗaya kin canja abinci ma baki ciba hira cikin ƴan uwan ki wanda ada ba haka kike ba shima kin bari idan baki son shi sai ki faɗi min inyaso sai na kuma tarasu nace kince bakiyi daga nan kuma kinga sai su ɗauke ni maƙaryaciya ko kuwa?".

Kuka ta fashe dashi tace,"Kiyi haƙuri Ammi ama niba haka nake nufi ba wallah bazan so nakance wanda bazata yi maki biyayya akan duk wani abu dakika umarce ni ba,duk abinda kikayi dai-dai ne a gare ni kuma abinda kike nima ina son shi na amince da abinda kika ce".

"wannan kuka babbar alama ce wanda take bada bayani daga wani ɓangare na zuciyar ki baki aminta da abinda ni nake ganin shine maslaha atare dake ba,gani kike kamar na takura ki idan har kina ganin zan shiga haƙƙin kine to sai a fasa ba wani abu bane".

"Ammi ni bance bana so ba nace na amince Allah yasa mudace".

"To shikenan Allaha yasa har zuciyar ki,yanzu tashi kije kici abinci".

"Bana jin yunwa ne Ammi".

"Ƙarya dai babu kyau yana ɗaya daga cikin abinda Allah ya tsana ki tashi kije kici abinci banson na ƙara magana".

Haka ta miƙe ta fita babu kowa a parlourn kan ta tsaye ta nufi kitchen abinci gaba ɗaya taji bazata iya ciba frij ta buɗe ta ɗauki apple guda ta fito parlour ta zauna tana ci.

Ƙamshin turaren Deen taji gaf da ita ɗagowa kai tayi suka haɗa ido tayi ƙasa da kanta tace,"Ina kwana".

"Lafiya".

Wai lafiya aikuwa bazata ƙara gaishe shi ba indai zai cigaba dace mata lafiya sai kace ta takura shi.

"Kin tashi lafiya?".

"Alhmdulillah".

"To Masha Allah,kar kice min wanan shine abincin da kike ci amatsayin breakfast?".

"Eh naci abinci na haɗa dashi ne kawai".

"Iuhm mai ƙarya dai yasan makomarshi".

"Dagaske naci abinci".

SANA'UL HUSNAH          {COMPLETED12/2019}.Where stories live. Discover now