26

707 28 0
                                    

*SANA'UL HUSNA*
   *1441H/2019M*.




®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION*.✍
{  _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira_.}

        '''🎐G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN K'ARFE•🏇🏻*_

*NA*


*UMMU NABIL*

*_Sadaukarawa ga Miss Xerks_🌺*

~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad~@
~GaskiyaWritersAss~.






*NO.26*



*__________*📖Da dare kuwa,bayan tayi sallahr isha ƙur'ani ta ɗauka tana karantawa Fidda ta shigo da gudu da sweet a hannun ta, Widad ce ta kalle ta tace,

"A'a Auta a ina aka samo wannan kuma zo na buɗe maki".

Miƙa mata tayi ta buɗe ta bata"Ya Shams ne ya bani kuma yace na kira mashi Habibty Sanah".

Ɗago kai Sanah tayi ta kalli Fidda bata ce mata komi ba ta cigaba da karatun ta Ammi tace,"Sanah baki ji ana kiran ki ba hala".

Ɗan ɓata fuska tayi tace,"Ammi karatu fa nake,ke Fidda je kice ina aiki ne".

"A'a ni baza'a ɓata min yarinya da ƙarya ba tun bata iya ba,ki tashi kije kiji mai zai faɗi maki".

Miƙewa tayi ta ajiye ƙur'anin a gefen gado hijab nata ta ɗauka ta sanya kafin ta fita.

Har ɗakin shi taje baya nan zata fito kenan sai ya buɗe ƙofar toilet ya fito,sanye da farar jallabiya,suna haɗa ido ta kuma tamke fuska har inda take ya ƙaraso yace,

"Dama inason tea ne".

"To ai kason hanya kaje kasha mana".

"Uhm ai da bansani ba bazance inaso ba,ke nake so ki haɗa min ki kawo min".

"Ni yanzu karatu nake yi gaskiya bari na saka Widad ta kawo maka".

"Bana son nata naki nake so idan kuma rashin kunya zaki min sai ki faɗi min,naga dama tun muna mota sai wani cin magani kike ke kuma kin gagara faɗi min meye dame ki".

Kawai sai ta fara matsar hawaye kukan gaske take,abin sai ya ɗaure mashi kai,to meye dame ta ko bata da lafiya ne,

"Kinga zauna anan kimin bayani mene".

"Bakai ne ba ɗazu".

"Ikon Allah ni kuma mene nayi maki".

"Kaine kayi hoto".

Abin yaso bashi dariya ama sai ya maze yace,"Na ɗauka hoto yaushe kuma".

Kuka ta kuma fashewa dashi wannan karon harda buga ƙafa tace,"Da mukaje park mana kai da wannan ƴan matan".

Dariya yayi sosai yace,"Ayya shine ya baki haushi ke kuma banyi dake ba ko?".

Gyaɗa mashi kai tayi alamun eh.

"To tashi muyi yanzu".

Babu kunya ta miƙe tsaye ya ɗora hannun sa akan kafaɗar ta suka ɗauka hoton sunyi kyau harda guntun hawayen ta agefen fuskar ta.

"Wannan baiyi ba ka kalla hawaye ya fito a fuska ta".

"To shikenan a sake wani".

Wani suka ƙara ɗauka haka sukayi tayin shirmen hoto,murmushi kwance a fuskar shi ya kalle ta yace,

SANA'UL HUSNAH          {COMPLETED12/2019}.Where stories live. Discover now