No 13-15

1.1K 35 0
                                    

[11/4, 11:20] Lovly tah 1: *SANA'UL HUSNA*







®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼


*_Sadaukarwa ga Miss xerks🌺_*





*NA*





*UMMU NABIL*





*NO.13*



________📖Cike da mamaki da al'ajabin kalaman su su Abiy,Ummi,Mahek,Manal suke binsu da iko,Abiy ne yayi ƙoƙarin cewa,



"Dama kunsan juna ne?"ya tambayi Shams.

"Eh Abiy gaba ɗayan mu nan ƴan Nigeria ne,babu wanda acikin mu aka haifeshi a ƙasar Dubai"Abiy ne ya kalle shi bayan ya samu wuri ya zauna yace,


"Zamu so muji tarihin ku gaba ɗaya".

Nima wuri na samu na zauna don jin meye asalin labarin su.

*LABARI*



"Dada kace Habibty tayi sauri kullum ita ne ƙarshen shiri ni wallah Dada indai bata daina mana haka ba,Allah zamu riƙa tafiya muna barin ta".


Dada ya kalli Widad yace,"Toh Naji sarkin ƙorafi kekam da ita ne bazata ce zata tafi ta barku ba ama ke gashi kince"ƙwala ma Sanah kira yayi da sauri tare da haɗawa da ɗan gudu ta ƙaraso tana littafan ta a hannun ta tace,

"Sorry Dada ban fito daga wanka da wuri ba,gashi kuma banyi break ba".

Ammi ce ta fito daga kitchen tana cewa,"Sanah ur breakfast is ready"tsayawa tayi don ganin su a parlour ta gama ƙare masu kallo sanan tace,

"A'a karku cemin har kun gama shiri ba?Sanah ko abinci bata ciba".

"Ammi just forget about her,mun riga mun makara idan taje skul ɗin ta duba abinda zata ci"Inji Widad ita kam Sanah gyaran rolling nata take ko magana bata yi mata ba.


"Ai ke kin ba?".

"Ehba naci".

Ta kalli Dada tace,"Ko ku wuce inyaso sai driver ya sauke naga kaima kamar zaka makara ko?".

"Kinsan fa bana son driver yana kaisu hankali na baya kwantawa gyara ni banje aikin nawa da wuri ba inyaso sai na kaisu zuba mata a lunch box sai taci a mota".

Dariya Widad tayi tace,"Dada sai kace ƴar Baby"ta kuma saka dariya.

Su Samah ne suka fito ita da Fidda,Dada ya kalle su yace,"Kaii Allah ya shirya min yaran nan wallah duk nayi tunanin suna mota ashe suma sai yanzu suka fito".

"Sorry Dada"inji Samah.

"Bata don Allah inyaso idan taci tabar box ɗin a mota kawai yanzu haka ma ɓata lokaci ne"da sauri Ammi ta juya ta samu food flask ta zuba mata ta dawo ta iske sun fita a mota ta same su ta bata daga haka suka yi sallama suka wuce.



Bakwai Da rabi dai-dai suka shiga makarantar su Sanah da ike ita ne a farko,tun a mota Dada ya bata ɗari biyar koda abinda zata siya tana sauka ya wuce ya sauke su Widad sanan ya wuce Office.


Tana shiga zata shiga class kinan bata kalla ma ko akwai mutum a gaban ta sai ji tayi ta bige mutum cikin sauri ta ɗago tare da cewa,

"Sorry please wallah ban kula b.."wanke ta yayi da mari a gigice ta ɗago ta kalle shi tace,

SANA'UL HUSNAH          {COMPLETED12/2019}.Où les histoires vivent. Découvrez maintenant