Epi ~ 4+3 =(7)

707 102 2
                                    

*—••••«•»••@••«•»••••—*

*RUBINA!!!♦️*
_[Rayuwata suke son ɗauka]_

*—•«•Novel series•»•—*
*{SEASON1}*

*Wattpad @Smart_Feenert*
*Be ~ smart*

*_{🌼Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—••••«•»••@••«•»••••—*

*🥀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🥀*
*—••••«•»••@••«•»••••—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—••••«•»••@••«•»••••—*

*Epi ~ 4+3 =(7)*

Bayan shekara7

Misalin Ƙarfe 2:00am; Amina matar Hussain ta tashi da laulayin nakud'a.

Inda a rud'e Hussain ya lalabo number Hassan a waya ya sanar da shi halin da suke ciki.

Kai tsaye Hassan ya ce da shi "Su had'u a Asibitin Udus, za su same su yanzu a can shi da matarshi."

Haka dai Hussain ya kinkime matarshi ya yi Asibitin da ita kamar yanda Hassan ya ce, ya na isa asibitin kai tsaye dakin haihuwa aka nufa da ita.

Ko 5mins ba'ayi ba Hassan ya iso shi da matarshi da dan karamin yaronsu da bai wuce 7years ba.

Cikin 30mins wata nurse ta fito tana tambayar kayan jarirai, a sannan Hussain ya ankaro da ya bar su a mota bai d'auko ba.

A hanzarce ya fita cikin sauri ya nuface wajen da yayi parking din motarsa, sai dai kan ya kai kan motar tuni wata mota ta biyo ta kanshi ta wuce.

A rud'e matukin wannan motar ya fito a hanzarce ya kinkime shi ya yi cikin Asibitin da shi inda direct aka nufe Emergency room da shi, ba tare da an jira isowar Police ba, domin idan aka bar shi a cikin irin wannan mugun halin da ya ke ciki, a take za a iya rasa shi a wajen.

Ko da Hassan ya dawo daga gurin da ya je, dan fitar Hussain kad'ai ke da wuya ya rufa mishi baya, ya cinma har an fito da gawar Hussain daga cikin dakin taimakon gaggawa za'a wuce da ita d'akin ajiye gawa da niyyar safiya na wayewa a dank'a wa muk'arraban shi.

Cikin mugun fita a cikin hayyaci kamar yanda yanayin shi ya nuna, Hassan ya shiga tambayar abinda ya faru da d'an-uwanshi ya same shi a cikin wannan halin.

Ba tare da b'oye-b'oyen komai ba aka sanar da shi k'addarar da ta afka ma shi, a take ya sulale k'asa zaune ya na zuba d'an neman kukan bakincikin rasa kanenshi da ya yi na har abada tamkar wani karamin yaron da ya wuni bai ga mahaifiyarshi ba.

A zahiri kukan gaske yake, amma a badili kukan farinciki yake domin aikinshi na biyu ya ida kammala saura na karshe da yake tunanin shi ma zai samu narasa a kan shi kamar yanda ya samu a na sauran dan ganin ya zama tantirin matsafi wanda ko aljani ba zai nuna ma shi tsafi ba.

Bai soma jin wani hamshakin farinciki ya ida lullub'e mishi zuciya ba, sai da aka sanar da shi cewa "Amina ta haihu kuma ta samu k'aruwar 'ya macce." Domin hakan kuma yana d'ai daga cikin abin da ya ke fata sabida ya na d'aya daga cikin makaman aikinsa da Wizgiri ya fad'a masa, amma sai bayan shekara20 aikin zai ida kammala domin za'a yanka yarinyar ne bayan ya yi jima'i da ita sannan a hade jininta da ruwan kwain Matarshi Aisha, wanda a halin yanzu sun jima da cire shi a jikinta, tin da jimawa, kuma Papa ne wanda ke d'auke da ragamar kula da shi har sai lokacin da yarinyar ta cika shekara20 a duniya baya anyanka ta amfanin shi zai soma.

Inda da zarar aikin ya kammala zai bar kungiyar Wizgiri ya kafa ta shi kungiyar assiri domin ya gawurta a wannan lokacin.

Inda kuma makarin wannan Assirin yana tattare ga wanda ya riga shi kwantawa da ita.

RUBINA!!!♦️Donde viven las historias. Descúbrelo ahora