Epi~ 8+8 =(16)

606 58 4
                                    

*—••••«•»••@••«•»••••—*

*RUBINA!!!♦️*
_[Rayuwata suke son ɗauka]_

*—•«•Novel series•»•—*
*{SEASON1}*

*Wattpad @Smart_Feenert*
*Be ~ smart*

*_{🌼Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—••••«•»••@••«•»••••—*

*🥀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🥀*
*—••••«•»••@••«•»••••—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—••••«•»••@••«•»••••—*

*Epi~ 8+8 =(16)*

A wahalce kamar wanda ya sha wani ɗan karen duka, ya juya baya ya nufi hanyar fita daga cikin palour'n, dan dole ba dan ya so ba.

Ba ta ɗaga daga wajen ba, sai da ta ga ya fita gabaɗai daga cikin side d'in ta daina ganin shi, sannan ta rufa mashi baya tare da saka ma k'ofar key ta kulle, saboda gudun kar ya kyakyace idanuwanta daga baya ya sake dawowa, dan yanzu al'amarin shi tsoro yake ba ta.

Sai dai ko da hakan ta na jin tsantsar tausayin shi a cikin zuciyar ta a yadda ta ga dik yanayin shi ya yi saurin canzawa farat guda, tamkar wanda ya kwana arba'in ba lafiya. ta ji ita ma dik ta damu, sai dai takaicinta guda, wanda idan ta tuna da shi yake kara tafarfasa tsokar zuciyarta, shi ne abinda ya faru yau. wanda har yanzu ta na mugun jin raɗaɗinshi a rai.

~~~~~

Ya na barin part din Rubina, direct part dinsa ya nufa domin ya gyara jikinshi, cike da kuncin dake damun shi.

~~~~~

Ita ma kai tsaye part ɗin Papa ta nufa dauke da sallamarta a baki. har ta kai ga isa cikin Palour'n, ganin ba ta same shi a nan ba ya sa a hanzarce ta ziyarce cikin bedroom dinsa ba tare da fargabar komai a rai ba, sai dai ko a nan ma shiru ne ba labari.

Nan dai cikin rashin gajiyawa ta ɗan rage tsawonta a kan kereriyar gado, ta gincira masukkan ta a nan tana zaman jiran ganin fitowar shi daga cikin bathroom kamar yanda take hasashe.

Sai dai ganin lokaci na ta tafiya kamar yanda ta gani a agogon da ke bangon d'akin, kuma ba ta ji wani alamun da zai nuna mata ana wasa da ruwa a cikin bathroom ɗin ba, ya sa a hankali ta taso daga saman bed ɗin ta nufi hanyar shiga bathroom ta tsaya kan kofar ta d'an kara kunnayenta a kai tare da bada aron hankalinta a wajen tana sauraren abin da ke tafiya. jin ko a nan ma babu amsar komai ya sa a hankali ta shiga kwankwasar kofar tana kiran sunan shi.

Sai dai ko a hakan ma shiru ne ta ji an k'i a amsa mata, nan take ta faɗa cikin bathroom ɗin a hanzarce.

Shigarta ciki ke da wuya ta tsinci kanta cikin wani mugun mamaki na rashin ganin shi a bathroom d'in domin babu shi babu samatarshi a ciki.

Nan dai ta yi karfin halin saita hanyarta, ta ficewa daga cikin part din shi, dan dole ta nufe nata bangaren.

In da ta na isa cikin part ɗinta ta lalabo wayarta dake kwance a saman makeken mirrorta, ta binciko number shi ta danna mata call.

Sai dai wayar na ta faman ringing amma an k'i a yi picking.

sai da ta jera mashi wajen miss calls goma sannan ta hakura da kiran number ta bude wardrobe ɗinta ta fito da tufafinta waje ta sauke masu farali a saman lafiyayyen gadonta sannan ta faɗa cikin bathroom domin biyan bukatarta.

Bayan ta gama uzurinta ta fito ta shirya jikinta tsaf sannan ta sauko kasa, a nan babban palour ta same shi zaune ya buga wani uban tagumi, kamar wanda talauci ya yi wa riga.

Sai dai sosai shigar da ya yi ta yi matukar ɗobo shi dik da tsakar dare ne amma hakan bai hana bayyanar ainahin kyawonshi karara a wajen ba.

Sanye yake cikin black jeans 3quater da T-shirt dark brown color had'i da bak'ak'en silifas a k'afarshi wad'anda suka yi matukar bayyanar da ainahin hasken kafafuwanshi waje tamkar baturen gaske.

Tun yadda ya ankaro da saukowar Mammie k'asa, ya yi hanzarin mik'ewa tsaye ya tunkaro wajen da take, yayinda suna had'a ido, ta watsa mashi wata uwar harara mai had'e da ruwan tsaki wanda ita kanta ba ta san ta iya ba, sai da ta ji ya fito a cikin kokon bakinta.

A takaice ta juya mashi baya ta koma  inda ta fito tare da nufar hanyar da za ta sada ta da bangaren Rubina.

In da ta b'angaren shi kuma tun lokacin da ya ji fitowar wannan raki'in tsakin a bakinta ya ji dik inda gaɓɓan jikinshi suke sun kwance, ya kasa ɗagawa daga wajen da yake, domin tun da yake bai taɓa jin Mammie ta taɓa tarbar shi da irin wannan d'an ballajja'un tsakin ba sai a wannan lokacin da yake jin dik abin da ta mashi daidai ne a wajen shi, muddin zai saka ta nishaɗi ta huce haushin da take ji a kan shi.

A sanyaye ya rufa mata baya cikin karfin hali mai haɗe da wani nakkasasshen kwarin gwiwa tamkar wanda kwai ya fashe ma a jiki, ya taka steps ya haye benen.

A daidai lokacin ita kuma ta kai kan kofar ta saka key ta bud'e, in da cikin rashin kula ta turo k'ofar ta rufe ba tare da ta sake saka ma kofar key ba.

Yana mird'a handle ya ji ya wangale mashi kofa, ya yi murmushi cikin yi wa Allah godiya ya fad'a ciki, bakinshi d'auke da bisimillah.

Ya na isa a cikin palour'n ya ga bai same su a nan ba, cikin tsarwakewar ruwan jiki ya dinga takon shi a hankali, dauke da zancen da zuciyarshi ke mashi na yanda zai shawo kan wannan karamin al'amarin tun kan ya haifafa ya zama babban al'amari a wajen shi.

~~~~~

Ko da ta isa a cikin bedroom ɗinta, ta same ta gincire a kan gado, idanuwanta sama suna kallon silin dakin, tana tunanin abin da ya dame zuciyarta.

Sallamar Mammie ce da ta ji a bedroom ya katse mata hanzari wajen ci gaba da abin da take, ta dan sake ranta cike da fuskar damuwa ta ce

" Mammie kin gaya wa Papa.? "

A raunane ta ce "A'a Rubina, ban same shi a side dinshi ba, kuma na kira wayar shi bai dauka ba ina ganin yana cikin masallaci ne! amma tashi mu je yanzu Ado direba ya kai mu ko bayan mun tafi ne zan sake kiran wayarshi na gaya mishi sai ya same mu a can Asibitin kin ga daga nan sai a san....." kasa k'arasa zancen ta yi ta dalilin jin wata murya da ta yi bala'in dukan cikin kunnenta...
*Follow me on wattpad and vote*

RUBINA!!!♦️Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz