Epi... 10+10 =(20)

676 54 18
                                    

*—••••«•»••@••«•»••••—*

*RUBINA!!!♦️*
_[Rayuwata suke son ɗauka]_

*—•«•Novel series•»•—*
*{SEASON1}*

*Wattpad @Smart_Feenert*
*Be ~ smart*

*_{🌼Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—••••«•»••@••«•»••••—*

*🥀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🥀*
*—••••«•»••@••«•»••••—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—••••«•»••@••«•»••••—*

*Epi ~ 10+10 =(20)*

Misalin Ƙarfe 8:30pm.

Rubina ce kwance a saman wani makeken gado da ke cikin part d'in da Hajiya Salina ta ware mata.

Hannu ta saka a hankali ta raramo wayarta da ke bedside ta soma danna a tsanake tare da mik'ewa zaune ta d'ora wayar a kan k'afafuwanta kafin bakinta ya soma k'usk'unniya da Salatin Annabin Muhammad (S.A.W).
Allahumma Salli Ala, Sayyidina Muhammadan Wa Sallim x10.

Sai bayan da ta gama sannan ta soma yunk'urin dannar wayar cikin rawar da hannayenta ke mata ta samu nasarar binciko wata wata number da ta tsareta da kallon one by one, kamar mai kidayar kwandalar saudiyya.

Cikin wasi-wasin da zuciyarta ke mata, ta kasa danna ma number calling, sai da ta kusan shafe wajen 20mins ta na kallon ta, kafin ta kai ga runtse idanuwanta gam, kamar cingan, sannan ta iya danna ma number kira, ba tare da ta bud'e idanuwan ba ko kuma ta kara wayar a kunnenta ba.

"Hello" d'in da ta ji an ce ne, ya katse mata hanzari wajen ci gaba da tunanin da take.

Slow-slow ta fara bud'e idanuwanta a hankali ta na kallon wayar, sai dai dik da hakan ta kasa cewa uffan.

Haka shi ma ta b'angarenshi tun "Hello."  d'in da ya ce bai sake aza wata kalma a sama ba.

Cikin d'an k'ank'anen lokaci suka soma yin azumin magana na karfin hali.

Sai can ita da ta ga uwar bari, ta ga idan ba maganar ta yi ba, ko za su kwana a haka ba zai damu ba.

Cikin gyaran murya, wadda ta kasa gane abin da ya tokare mata makogoro ta ce "Hello"

Cikin shauk'in da ya ji ya zunduma a cikin wani dadd'an yanayi marar misiltuwa, sanadiyyar jin muryata da ya yi ta dake cikin kussuwar kunnenshi, ya lumshe idanuwanshi a hankali yana ci gaba da saurarenta kamar kar ta tsaya.

Jin ta yi mashi shiru cikin son kawar da shauk'in da ya zumduma a cikinshi, ya saka shi tarar numfashinta cikin natsuwa da wayewa, ya ce da ita "Sisterna ya kike?"

Ita ma abin da ya ji shi ta ji, cikin ustazun farinciki mai hade da zallar shagwaba, ta ce "kanwa kuma?"

Sai da ya fitar da wani jarababben numfashi a waje kafin ya ji ya soma cewa da ita. "Eh man! ko ba kya son sunan ne na canza?"

A kasalance ta ce "A'a! ina so sosai ma"

Ya ce "To shi ke nan!, yanzu ya aka yi ne?"

Cikin sanyin murya ta ce "Daman na kira ne na ji da gaske za ka yi tafiyar da na ji an ce za ka yi gobe?"

Murmushi ya saka cikin jin dad'i, ya ce mata "Me zai hana kuwa?"

Ta ce "Shi ne ko ka kira ni ka sanar da ni?"

RUBINA!!!♦️Donde viven las historias. Descúbrelo ahora