Epi ~ 6+5 =(11)

641 68 2
                                    

*—••••«•»••@••«•»••••—*

*RUBINA!!!♦️*
_[Rayuwata suke son ɗauka]_

*—•«•Novel series•»•—*
*{SEASON1}*

*Wattpad @Smart_Feenert*
*Be ~ smart*

*_{🌼Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—••••«•»••@••«•»••••—*

*🥀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🥀*
*—••••«•»••@••«•»••••—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—••••«•»••@••«•»••••—*

*Epi ~ 6+5 =(11)*

Bayan wata Ukku da kwana shidda

Misalin 4:00pm.

Ya Rubin ne tafe daga cikin part dinsa, dauke da system dinshi a hannu ya haura saman upstairs inda kai tsaye part din Papa ya nufa.

Ko da ya isa part d'in Papa, bai same shi a palour'n ba, ba tare da tunanin komai a kai ba, ya nufe hanyar shiga bedroom sallama d'auke a bakin shi, sai dai ko kan kofar shiga bedroom din bai isa ba, ya tsaya cakk tare da saka ma kanshi wani zazzafan full stop a wajen, ta dalilin wayar da ya ji Mahaifinsa na yi wadda ko kad'an ya kasa fahimtar akan me Papa yake maganar, sai dai yana da tabbacin koma mene ne ba alkhairi ne ya ke furwata ba, domin bai tab'a jin k'irjin shi ya yi bala'in dokawa irin wannan lokacin ba.

Nan take kunnayenshi suka soma jiyo mashi wata babbar maganar da ta yi mugun saka rayuwarshi cikin ruɗu kala-kala da fargaban abin da ya ke sauraren Papa na magana akan shi.

Inda ya ji yana cewa "Ai Alhaji Sirajo ba ka san wani abu ba! Wannan ba wata babbar matsala ce a wajena ba, da yardar shugaba Wizgiri kafin karfe 10pm ta gwafta, dik sun kwanta bacci wanda ba lallai ba ne su iya tashi a tsakar daren ba, sai dai koda safiya za ta waye za su tarar da abin mamakin da na ce za su gani na farincikin zuwan wannan ranar, sai dai wannan ranar za ta kasance rana mafi soyuwa a cikin zukatansu, domin za su tsinci kansu cikin jimamen mutuwar 'yar karamar magen da na jima ina kiwo."

Jim kad'an cikin wata d'ind'imemiyar dariya marar ma'ana ya sake cewa, "Wato kana wasa da ni kenan Alhaji Surajo?, ai ni a tunanina kafi kowa sanina akan dik abinda na saka a gaba ba zan tab'a kai gwiwowina kasa ba har sai na ga bayanshi, shin wai ni yanzu akwai abinda nake shakka? Ko kuma akwai abinda ke bani tausayi a duniyar nan?, wlhy tin lokacin da na salwantar da rayuwar Mahaifana a doron duniyar nan, na daina tausayin komai a cikin zuciyata! shin ko ka manta ne na tunar da kai yanda na salwantar da rayuwar Iyayenta ita ma har suka bar duniyar nan, bari kuma na har a bada?."

Sosai Rubin ya girgiza da waɗannan kalaman da ya ji mahaifinshi na faɗi, har ya tsinci kanshi cikin fargaba da tunanin "wannan ba mahaifinshi ba ne, canza mishi shi ne aka yi."  inda kai tsaye ya zurfafa cikin kogon tunani, yayinda yana cikin zuba wannan aikin ne, ya soma jin Papa na cewa "A zahiri mahaifinta kaddarar hadarin mota ne ta afka mashi, amma a badili kaddarar karfin sihirina ne ya afka mashi, Ka sani fa ni da kaina na karkato wannan motar ta yi kan shi har ta ma naman jikinshi raga-raga a k'asa, haka ma matarsa ni ne na rad'a ma Nurse d'in da ke kula da ita, magana a cikin kunne kuma na kafeta wanda kai tsaye ta je ta tunkare ta da batun wannan mutuwar, wanda daman sanina ne idan har ta ji abinda zata yi ta huta ma kanta, shi ne ta had'iye zuciyarta ta mutu domin shi ne abu mafi sauk'i a gareta! hahahahaha" ya facce da wata arniyar dariya, kafin ya kara cewa wani abin.

Cikin rididda kamar wajen da ake bugun shadda rini, Rubin ya ji gabanshi na tuntsirewa sama yana faɗuwa kasa, nan take ya ji ko motsin kirki ya kasa yi a wajen da yake, tare da tunanin cewa "Anya ba wani tulluk'in mugu ba ne ya hauro masu ta gini ya fado masu cikin gida ya kwaikwaye irin muryar Papanshi dan ya ba shi tsoro ba?" nan kuma wani sashe na jikinshi ya ce da shi "idan kuma mugun ne kamar yanda kake tunani muryar kuma ta wanene?, afili ya ce, "Na kasa fahimta."

Shirun da ya ji Papa ya yi ne, hankalinshi ya kara mummunan tashi da tunanin Papa ya hango shi yana mashi laben da sanda yanke a rayuwarshi bai taba wa wani ba balantana iyayenshi.

Cikin wata uwar mazarniyar da yake Jin kafafuwanshi na mashi kamar wanda aka tsamo daga cikin miyar kub'ewa d'anya, ya shiga kokarin barin wajen a hanzarce, yayinda ko ida kai kafarshi k'asa bai yi ba, ya ji Papa na cewa "Ai wannan dik hauka da wayo ne nake masu kamar yanda kake gani, wato a fuska kokarin bayyana soyayyar d'a da uba nake a gare ta, amma a cikin zuciyata babu komai a cikinta face biyan bukata, kai kanka shaida ne akan ban raine ta dan ta yi tsawon rayuwa ba, na rainata ne sabida jiran lokaci tare da dibara domin ka san hausawa na cewa ' Yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba.'  da ace na barta a wajen dangin mahaifiyarta kamar yanda suka so a farko, shin da yanzu ba a yi mata aure ba? ko kuma idan ba su aurar da ita d'in ba, za su iya bata haramtacciyar tarbiya wani ya riga ni samun kanta ya kai mata dauki kafin ni, kaga kenan daga wannan lokacin dik abinda na binne kasa sai ya fito waje, assirina zaya tonu, karshen rayuwata kuma zai zo, za ku yi dinner da naman jikina, shugaba kuma ya shanye Jinin da ke jikina, kassan da suka rage a jikin kuma ya bawa karnukan aljannanshi su ci! Ko ba haka bane.?" Cikin dariya ya karasa zancen ya na mai kara ci gaba da maganar ya ce "Amma yanzu komai ya zo karshe domin an cin ma matsaya! zan jira zuwan 12:00am yau kamar mai zaman jiran ganin salary, tabbas yau babu shakka zan kore kishirwar da ta dade tana damuna a gareta da kuma cikar burina na zama babban matsafi na ukku a cikin jerin bil'adam a duniya, sannan na yi alkawarin kafin na fara shan jinin mutum na biyu a saman kujerar mulkina, jinin matata ne zai maye gurbi domin zan sake sabon zubin, shi ma sabon zubin da ya tsufa zan sake kawar da shi gefe na d'ora daga inda na tsaya."

Cikin wani mugun tashin hankali Ya Rubin ya ja da baya cike da firgici wanda kad'an d'e ya rage system din dake hannunshi ta fadi kasa domin ya yi bala'in girgiza da wannan al'amarin.

Wata Jakar dariya ce da ya ji Papa ya saka ta kara d'aga mashi hankali domin sai da ko ina ya amsa daga bisani kuma ya ji ya sake cewa, "Ai shi ne babban partyn da na ce zan had'a mata, kuma tabbas sai na cika mata wannan alk'awarin da na d'aukar mata tun tana 'yar k'ank'anuwar ta! riba biyu gare ni a kanta, na farko cikar burina na biyu kuma ni ne mutum na farko da zai amshe budurcinta wanda kuma ni ne na k'arshe da wani d'a namiji zai kwanta da ita! Sirajo ko ka san wani abin ma? tun lokacin da ta kai matakin balaga na yi kokarin fidda mata dik wata sha'awa a cikin rayuwarta, domin sanin kanka ne makarin wannan abin dik bai wuce wani ya rigani amsar budurcinta a lokacin ba, wanda zan iya cewa ma a yanzu har an shigo cikin wannan lokacin, cikawa ne kad'ai ya rage 12:00am ta yi, sai dai wani abin farincikin a nan shi ne, har yanzu ba a halicce wannan mutumen da zai b'ata man shiri ba kwata-kwata a cikin wannan duniyar, babu burbud'in numfashinshi a cikinta, kai ko da an yi shi a yanzu wlhy tun kafin ya fitar da numfashi na biyu a cikin wannan duniyar zan kawar da rayuwarsa izuwa lahira, domin wlhy kisa ce tsagwaron ta, amma yanzu kuma komai yana nan a tsare kamar yanda yake, misalin karfe 11:50pm sha'awarta ga ɗa namiji za ta motsa, kafin nan da minti goma za ta kasa controlling din kanta, inda kai tsaye dakina za ta nufo aguje domin da zarar wannan lokacin ya zo tunanin kowa fita zai yi a cikin kwakwalwarta, daga wannan lokacin kuma komai ya gama kammala kuma ya zamo tarihi hahahaha." Daga nan ya dasa aya, da dariyarshi ta mugunta ya karkare wayar ya na mai ajiye wayar a saman lafiyayyen gadonshi, ya mik'e tsaye cikin nufato hanyar fita daga bedroom d'in.

Ko kad'an Ya Rubin bai san da karkare wayar ta shi ba kamar yanda  hankalinshi bai ahamo ga nufato wajenshi da yake k'ok'arin yi ba, domin tintuni hankalinshi ya dad'e da barin gangar jikin shi, Imaninshi da tunaninshi dik sun bi sun gagare zuciyarshi game da mahaifinsa mai fuska biyu, kafin ya ankaro sai ganin saukar kafar Papa ya yi a kan hanyar fitowa daga cikin bedroom d'in izuwa palour'n...........
Follow me on wattpad and vote.

RUBINA!!!♦️Donde viven las historias. Descúbrelo ahora