MATAR DATTIJO page 1

5.2K 189 8
                                    

MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
           *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

1

fitowa nayi daga daki ina shure-shuren kafa, "ni Allah baxan je ba innah" da kayana innata ta biyo ni tana rarrashina haba Niimatullah me yasa Kullum idan xaki makaranta sai an yi tsallen tsiya da ke, karbi kayan ki saka, kinga idan kika makara aka xane ki kada ki fara dawowa kiyi min korafi ko kin fada baxan kula ki ba, idanuna ne suka cika da hawaye, ni baxan je ba innata Kullum naje sai malam ya dake ni bansan me nayi masa ba ya tsane ni. ina maganar ina share guntun hawayen da na kalato shi da gan-gan, rarrashina ta shiga yi har sai da na saka kayan na tafi ina tafe a hanya ina mita, cin karo nayi da Babana da gudu na karasa wajensa ina sharar kwalla, cikin tashin hankali ya dube ni, me yasa min ke kuka Niimatullah? idanuna cike da hawaye na dube shi, innata ce tace sai naje makaranta ni kuma ban son xuwa,  cikin kulawa tare da murmushi ya dafa kaina, kiyi hakuri yar lelen baba kije makaranta kin ji ko, ilimi shi ne gishirin xaman duniya, musamman ilimin addini, karbi wannan yasa hannu a aljihu ya miki min naira biyar, cike da shagwaba na tabe baki, ka barshi baba tausayinka nake ji, da dukkan alamu yaji dadin abinda na fada masa, dafa kaina yayi Allah yayi miki albarka yar lelen baba, Allah ya baki abinda kika tafi nema, amsa masa nayi da Ameen, na kwasa da gudu sai makaranta, cikin ikon Allah naci sa'a ba a fara dukan makara ba don haka cikin farin ciki na shiga Aji
Bayan an tashi na biyo ayarin kawayena muka taho muna tafe muna sha'anin mu irin na kuruciya, muna gab da shigowa ciki unguwa wata mota tayi parking a gaban mu, gaba daya muka ja da baya, saboda innata ta dade tana min gargadin idan naga mota na rika matsawa saboda masu satar yara, xuge glass din motar aka yi wani kyakkyawan dattijo ne ya leko da kansa, kallo daya xaka yi masa ka tabbatar da cewa kyakkyawa ne na ajin farko duk da ya fara manyanta hakan baxai hana ka fahimtar kyakkyawa bane, farin glass din da ke sanye a fuskarsa ne ya kara xayyana masa kyansa, sanye yake da farin voil wanda aka yi wa aiki da farin zare, kansa sanye yake da hula fara, babban mutum ne mai kamala duk inda ka kalle shi sau daya sai kayi marmarin sake kallonsa, saboda yadda Allah ya tsara masa halittar sa, cikin tattausar muryar sa ya kira mu, ku yaran nan ku xo, gaba daya muka fara ja da baya saboda mun tuna gargadin da iyayen mu suke mana, kwarjinin da yayi mana ne yasa muka kasa tafiya mu kyale shi, sake maimaita maganar da yayi a baya yayi, ku xo yara tambayar ku xan yi, daya daga cikin mu ce tayi karfin hali ta karasa inda yake cikin ladabi ta gaida shi, dagowa yayi tare da shafa kwantaccen farin gashin da ke kewaye a fuskarsa, kira min ragowar yan uwan naki xan tambaye ku gaba daya, da gudu ta karaso wajen mu, yace kuxo xai bamu sako ne, ba mu yi mata musu ba muka bita har wajen wannan mutum, murmushi yayi sannan ya fara yi mana magana, tsoro ku ke kada na gudu da ku ko, abinka da yara muka yi saurin amsa masa da eh. girgixa kai yayi to ku kwantar da hankalin ku ni ba irin wadanda ku ke zato bane, ke yarinya ya nuna ni da hannunsa ke nake son tambaya, hannu yasa ya dakko biron dake soke a jikin aljihun rigar sa sannan ya dakko takarda, tambayata ya fara yi ya sunanki gabana na dukan uku-uku na amsa masa da sunana Niimatullah, a wane unguwa kike, a nan bayan layi gidan mu yaje ba nisa daga nan, kafin na gama bashu amsa har hawaye ya cika idanuna, cikin damuwa ya dube ni, me yasa xa kiyi kuka Niimatullah, cikin kukan na bashi amsa, tsoro nake ji kada kaxo ka gudu da ni tsakar dare ni da innata, dariya na bashi sosai ki kwantar da hankalin ki ni ba haka nake ba, ku shige ku tafi gida kada a ga kun dade, wucewa muka yi kirjina na dukan uku-uku, ina shiga gida na fada jikin innata ina kuka, tambayata ta shiga yi me ya faru da ke yar lelen baba, cikin kuka nke bata labarin yadda muka yi da mutumin da muka hadu da shi, shiru innah tayi tana naxarin maganata, ki kwantar da hankalin ki Insha Allah alheri ne, tashu ki dauro alwalar magariba kinga lokacin sakkah ya gabato,  tashi nayi na dauro alwala na dawo jikin innah na kwanta saboda fargaba ce fal a cikina.

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now