MATAR DATTIJO page 11

1.9K 78 0
                                    

MATAR DATTIJO*
??????????

*©jeeddah Tijjani*
          *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*Don Allah don Annabi masu hade min pages 2 ya xama daya dan Allah ku daina bana so, gaskiya idan na kara cin karo da irin wannan xan dakata da typing*

11

Ina shiga gida naji wani bakin ciki ya tokare ni a makogoro, tambayar kaina na shiga yi me yasa har na amince da auren wannan dattijon gashi nan yana kokarin shigar min rayuwa, muna daf da shiga cikin gidan ya kira sunana.

Niimatullah!!! a sanyaye na waiga na dube shi, matsowa yayi daf da ni har ina jin kamshin turarensa, dafa kaina yayi tare da dago fuskata saura kuma mu shiga cikin gida kiyi min tonon asiri don nasan ki akwai surutu a wasu lokutan, kina yi xan dawo gobe na tafi da ke kin san dai innah da baba baxa su hana ki bini ba, shiru nayi masa saboda haushi yake bani yanxu.

muna shiga innah ta tarbe mu da murnarta,ya naga har kun dawo da wuri haka Alhaji, sunkuyar da kansa yayi tare da shafa fuskarsa, tafiyar tamu ce bata samu ba innah, cikin jimami innah ta bashi amsa, ayyah ai dama komai sai Allah ya nufa, hira suka fara yi ni kuwa sai kallon fuskarsa nake yi muna hada ido da shi sai nace na fada??

yana ji na fadi haka sai ya sunkuyar da ido kasa saboda kunya, sake maimaita masa maganar na rika yi, na fadawa innata inda muka je da abinda nayi maka? da hanxari innah ta dube ni, wai ke wace irin yarinya ce Niimatullah idan kika sake magana sai na hada miki kayan ki kin bishi, kuka na fara yi haba innata gidan wannan mutumin xaki kaini Kullum fa sai ya matse ni kamar wata yar tsana, duka ta kai min ke dai baxa ki daina halin ki ba ko, dole ma a tattara ki a kai ki gidan miji ko kya yi hankali a can bari malam yaxo na fada masa tunda abinda kike yi kenan, idan kika koma can kika tare sai ki bada labarin gidan mijin da hujja, kuka na fara yi ina mata magiya tayi hakuri,  shi kuwa dattijo kamar ya nutse saboda kunya ya rasa bakin magana, basu gama hirar ba ya tattara kayansa ya tafi, inna ce ta dube ni baxa ki tashi kiyi masa rakiya ba ko, cikin shagwaba nace yasan hanya fa innah, maficin da ke hannunta ta kwado min, idan ina magana kina min musu sai mun fara fada da ke a gidan nan, ina tafe ina turo baki na bishi soro,  tsayawa yayi yana kallona domin ya rasa bakin yi min magana.

gajiya nayi da tsayuwa na dube shi, ni xan tafi gida don na gaji da wannan tsayuwar da nake yi, lumshe idanunsa yayi tare da cewa lallai ina da aiki har yanxu akwai haukan kuruciya a kan matata, tsugunnawa yayi har kasa yana rokona, dan Allah ki daina yi min irin wannan abubuwan da kike fada a gaban innah ina jin kunya na rasa ina xan sa kaina, me yasa kike haka Niimatullah ba fa a kanki aka fara aure da wuri ba,  iyayenmu da kakannin mu duk kusan irin wannan auren aka yi musu, kuma akwai yara kanana da ake aurarwa a kai su gidan maxajensu kuma su basu hakkkinsu babu mai ji, amma ke daga na taba hannun ki sai ki rika yawo da ni kina kunyata ni.

Hararar shi nayi ni ba ruwana da su kaina na sani tunda innata tayi min karatun kada na bari wani ya taba ni baxan xubar da wannan karatun ba, kuma ko yau ka kuma yi min, sai na fada a gida idan baka gaji da taba ni ba nima baxan gaji da baka kunya ba.

Haushi na bashi don haka ya fara magana, tunda abin naki haka ne baxa ki daina ba ko, to nan da sati xaki tare a gidana ki fara taka irin rawar da sauran matan aure ke takawa a gidan maxajen su, sunkuyar da kaina nayi ina sauraren sa, kafin na ankare ya rungumo ni ya hada fuskata da tasa idanunsa naga ya canja ya rika aika min da sakonnin soyayya kala-kala,  sai da ya dawo cikin nutsuwarsa ya dube ni

tonon sililin da kike min ne yasa nayi miki haka yanxu ma idan kin koma gida ki sake fadawa inna xaki ga yadda xamu kwashe ni da ke,  yana gama fada min ya wuce ya tafi,  jikina a sanyaye na shiga gida, duk maganar da nayi wa inna bata amsa min ba, jikina ba karfi na karasa wajenta, kawar da kanta gefe guda tayi tare da juya min baya, cikin sassanyar murya na dora hannuna a kan cinyarta ina mata magana, me yasa xaki juya min baya innata ki daina kulani ni fa ba wani laifi nayi masa ba ko da muka je can din tausa yace nayi masa kuma nayi.

A hankali ta dube ni wannan rashin sirrin naki shi yake hada ni da ke, a ce baxa ki rika rike sirrrin mijinki ba kullum ina nuna miki illar hakan kin kasa ganewa, kuka na fara yi to ni innah me yasa yake min haka, dama haka aka ce ya rika yi min,shi yasa fa nake xuwa na fada miki don ki rika yi masa magana, ni bana son abinda yake min,hawaye na rika sharewa ita kuwa innah saboda takaici ma ta kasa cewa komai sai da nayi kukana na koshi sannan ta rarrashe ni tace xata yi masa magana.

Baba na shigowa take fada masa yadda ta kaya tsakanina da dattijo, kama baki yayi lallai Niimatullah ba hankali, yanxu da hankali xa a rika wannan xancen, amma dai xan nemi mijin nata nayi masa magana ya dan saurara har xuwa tayi wayo tunda bata san ciwon kanta ba xata iya xuwa wani wajen ta fadi abinda ke faruwa tsakaninsu.

ba karamain dadi naji ba da baba yace xai neme shi yayi masa magana.

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now