MATAR DATTIJO page 31

1.8K 57 0
                                    

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
           *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

                       *معذرة🤦🏼‍♀*
*Har yanxu ina samun korafi da maganganu a kan cewa akwai pragrap na karshe na page din jiya a kan sak komai da komai irin na auren sirri ne, tabbas baxan musa muku ba domin ba xargi kuke ba gaskiya ne abinda ku ka fada, kuma duk wanda yasan littafina da yadda nake rubutu yasan wannan ba rubutuna bane sanya min aka yi sbd ni ban fiye fito da abu kirikiri na fade shi kai tsaye ba, ina fatan masoyana xasu fahimce ni, abinda yasa ban cire wajen ba saboda rubutun ya riga ya gama xaga duniya idan na cire ma kamar ya xama aikin banxa, na gode da kaunar ku gare ni*

31

Tsintar kaina nayi cikin rashin karfin jiki gami da kasala, domin kuwa dukkan wata gaba ta jikina ciwo take yi, can kasan xuciyata kuma wani haushin dattijo nake ji, ban taba xaton abinda xai aikata a gare ni ba kenan, gefena na juya na tarar da shi yana ta faman sharbar bacci abinsa.

kokarin komawa baccin nayi amma radadin da ke ratsa min kwakwalwata ya hana ni komawa, da karfi nake magana Allah baxan kuma kwana a gidan nan ba sai kuma na fadawa innah ta dauki mataki a kan ka tunda abinda kayi min kenan, cikin bacci yaji surutan da nake yi a hankali ya bude idonsa yana kallona, murmushi ya sakar min sannan ya fara min magana.

kiyi hakuri Niimatullah dukkan abinda ya faru ba laifin bane sonki ne ya jawo min, kamata ma yayi kiyi farin ciki amaryar dattijo domin wata darajar ki ce ta kara shiga xuciyata kuma kaunar da ke cikin raina ta kara ninkuwa fiye da, da.

turo baki nayi tare da cewa ba wani nan tunda ka xalunce ni komai ma sai ka fada, ni daga yau na daina kula ka tunda haka kake, rarrashina ya fara yi gami da bani hakuri, ni kuwa wani haushinsa ke kara kama xuciyata. kifa kaina nayi jikin pillow ina cigaba da kukana saboda a halin yanxu shi ne kadai abinda xai sanyaya min raina.

tashi yayi ya nufi toilet, yaje ya kintsa kansa sannan ya dawo, muna hada ido da shi na kawar da kaina gefe saboda a yanxu kallon axxalumi nake masa, kiran sallar asubah aka yi don haka na rika kokarin mikewa amma na kasa tashi, wani kuka na saki tare da cewa, gashi nan ka karya min kafa na kasa tashi, cike da kulawa ya karso gare ni kiyi hakuri Niimatullah ki yiwa mijin ki uxuri na fada miki komai nayi sonki ne ya jawo mini.

taimaka min yayi ya mikar da ni tsaye ya kai ni har bandakin inda ya hada min ruwan dumi na gasa jikina da shi,bayan na kammala na fito yaja mana jam'i muka yi sallah.

muna idarwa naji wani xaxxabi ya rufe ni jikina banda rawar dari babu abinda yake yi, hawaye ne ya shiga fita a idona cikin kuka nake yi masa magana, ni dai ka kira min innata mu yi magana, na fada mata xaxxabi nake yi taxo ta tafi da ni, matsowa yayi kusa da ni tare da kwantar da kaina a kirjinsa, kiyi hakuri Niimatullah kin ga yanxu safiya ce idan aka kira innah a irin wannan lokacin aka fada mata baki da lafiya hankalinta ne xai tashi, ki bari gari ya kara wayewa sosai sai na kira miki ita.

cike da shagwaba nake masa magana, ni dai Allah yanxu xaka kirata idan ba haka ba kuma na dauki jakata na tafi gida, shiru yayi ba tare da ya amsa min ba, wayar da ke gefensa ya dakko ya fara kiran waya, duk a tunanina innah ya kira kawai sai naji salon hirar tasa ya canja.

wani doctor ya kira inda ya shaida masa cewa bana jin dadi, ya fada masa dukkan abinda yake damuna daga karshe ya fada masa cewa yaxo asibiti ya karbar min magani.

cike da mamaki na dube shi, haba dattijona dama ba innata xaka kira min ba sai ka tashi kira wani doctor ni ko ya bani maganin ma baxan sha ba tunda baxa ka kira min innata na fada mata ba.

cike da kulawa ya dafa kafadata kiyi hakuri gari ya waye sosai Niimatullah, yanxu idan innah taji ba ki da lafiya xata iya tahowa yanxu saboda yadda take ji da ke.

shura kafata nayi ina kuka har sai da na hargitsa shirin gadon gaba daya, cikin kuka nake masa magana, ni dai sai ka kira min ita Allah, rarrashina ya shiga yi to kiyi hakuri ki daina kuka yanxu xan kira miki innarki.

ringing daya wayar tayi naci sa'a innah ta dauka, muna fara magana taji na rushe da kuka, Haba innata tunda na tafi kika manta da ni yau kwanana shida amma baki taba xuwa kin ganni ba, gashi nan yanxu haka ba nida lafiya.

A raxane innah take tambayata me ya same ki Niimatullah, cikin kuka nace mata xaxxabi nake kuma............ina maganar dattijo na kallona yana min warning a kan kada na fadawa innata abinda ya faru.

tambayata ta cigaba da yi kuma me Niimatullah?kin fara magana kuma kin yi shiru, cikin sarkewar murya na bata amsa ni dai kixo innah xan fada miki dukkan abinda ke damuna a gidan dattijo, sallama muka yi da ita sannan ta kashe wayarta.

murmushi yayi sannan ya dube ni, Niimatullah kenan sarakan tonon silili, idan innah taxo kika fada mata sai na kara maimaita miki abin jiya, turo baki nayi Allah sai na fada wa yace ka rika takura min.

lallaba ni ya shiga yi saboda yasan wannan kadan ne a cikin karamin aikina babban aikina ya fi gaban haka. tashi yayi ya shiga kitchen ya hada mana breakfast sannan ya dawo ya fara bani har sai da naci na koshi, tashi yayi tsaye yana dubana.

Amaryar dattijo, a hankali na dago ido na kalle shi tare da cewa na'am dattijona, lumshe kyakkyawan idanunsa yayi sannan ya fara yi min magana, xan je yanxu na karbo miki maganin ki, saboda bana son xaxxabin yayi karfi a jikin ki, ki kula min da kanki kinji amaryar dattijo, dago kaina nayi tare da cewa to a dawo lafiya.

Bai dade da fita ba ya dawo hannun shi rike da ledar magani, cikin kulawa ya ballo maganin ya bani amma naki karba, sai da rigima nasha guda daya saboda a rayuwata na tsani magani da allura.

Da misalin karfe sha daya na rana innata ta iso, tun daga nesa na jiyo muryar dattijo na mata sannu da xuwa, ina jin alamun shigowarta dakina na rushe da kuka,  karasowa dakin tayi ta same ni ina kuka har da su majina.

cike da damuwa ta karaso inda nake, tambayata ta fara yi, me yake damun ki Niimatullah, kishiyar ki tayi miki wani abu kike wannan uban kukan ko kuma mijin ki,ni dai naga alamun ki baki da wata matsala a tare da ke, kuka na cigaba da yi naki bata amsa har sai da ta fusata.

baxa ki amsa min maganata ba sai na bata miki rai, cikin kuka nace dattijo ne, tana ji na ambaci shi ne ta dakatar da ni, to ya isa kada ki fada min abinda ya hada ku don nasan kwanan xancen, turo baki nayi dan Allah ki bari na fada miki abinda ke faruwa innata.

shi ne Kullum yake...........hannu tasa ta toshe bakina, nace bana bukatar ji ko Niimatullah idan kika kara magana xan dauki takalmana na tafi duk wata mace da kike ganinta a gidan aure hakuri take, saboda aure ibada ne, kuma duk abinda ya xama ibada dole sai an yi hakuri an jure an kuma jajirce wajen yin aiki tukuru, don haka kema ki dage wajen kulawa da mijin ki ta haka ne xaki xama mace ta gari, wacce mijinta xai yi alfahari da ita.

kalaman innata sun shiga kunnena sosai kuma na kudiri niyyar cigaba da amfani da su indai xan xama mace ta gari a wajen dattijona, hirar da muka rika yi kenan har xuwa lokacin da xata tafi gida.

yau ma da riguma muka rabu ji nayi kamar na bita mu tafi, wata kaunarta ce ta kama ni a ranar wuni nayi ina kuka ban iya aikata komai ba wannan dalilin yasa xaxxabina ya kara tsananta saboda kukan da na sha.

*follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*

*jeeddahtulkhair😘*

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now