💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)**Kamar yadda kike ta daban,sunanki na daban haka ma halin ki na daban ne, komai naki ya banbanta da nasu, kina da hakuri da kirki da son mutane Allah ya Kara miki daukaka, ya kare ki daga sharrin makiya, na sadaukar da shafin nan gaba daya gare ki AISHATUL HUMAIRA,ina yin ki irin totally din nan*
42
Gaba daya a rude yake sai gumi yake sharewa,ya kasa driving din gaba daya sai jujjuya ni yake yana hawaye, kiran abokinsa yayi yaxo ya ja motar kasancewar ba shi da nutsuwar da xai iya jan motar, rungume nake a jikinsa hawaye na sauka a kan fuskarsa, ban san halin da xan shiga ba idan na rasa cikin nan, dan Allah ki taimake ni kada ya xube Niimatullah, idona a rufe yake saboda bana fahimtar komai banda ciwo babu abinda cikina ke yi, hakuri abokinsa yake bashi yana kwantar masa da hankali.
muna isa asibitin aka fara bani taimakon gaggawa cikin rudewa dattijo ya tambayi likitan, doctor ya lafiyar cikin da fatan yana nan bai xube ba?Cike da kulawa ya bashi amsa yana nan amma daf yake da barewa, dafa kanshi yayi cike da damuwa yake magana, dan Allah duk taimakon da ya kamata a bayar a yi don kada ya xube, cikin nutsuwa ya bashi amsa insha Allah xa mu yi kokari Alhaji.
Cigaba da bani taimako aka yi har aka samo kaina na daina bleeding din da nake yi, a ranar a asibitin muka kwana don ko su innah bai fada musu ba don kada hankalin su ya tashi, haka muka kasance a asibitin yana kulawa da ni yana min dukkan abinda nake bukata.
Washe gari aka sallame mu, kafin a bamu sallama sai da ya fada masa cewa dole ne na daina aiki mai yawa saboda kada cikin ya xube, kuma ya fada masa cewa a daina bata min rai idan ba haka ba cikin xai iya xubewa a kowane lokaci, wannan dalilin yasa ya wuce da ni gidan innah don na samu Hutu.Da sallama muka shiga gidan hannun shi janye da akwatina, innah na ganin mu ta mike tana tambayar mu lafiya, cike da ladabi dattijona ya gaida ta sannan ya fara yi mata bayani
Dama daga asibiti muke innah, cike da kulawa ta tambaye shi wane kuma ba lafiya? Kansa a sunkuye ya amsa da Niimatullah ce innah, kwana biyu tana yawan rashin lafiya ne shi ne muka je asibiti aka ce tana bukatar hutu shi yasa na kawota don ta huta.
Cike da kulawa innah ta kamo ni ta kwantar da ni a kirjinta sannu Niimatullah ki rika kula mai yaron ciki ba a so ta rika aiki mai yawa kin ji autar baba, narkewa nayi a jikinta sannan na amsa mata da to innah.
Hira suka fara yi ita da dattijo bai tafi ba sai wajen karfe biyar na yamma, kallona yake yana wani kashe min idanu innah na ganin abinda yake yi ta tashi ta bar mana wajen saboda kada a yi abin kunya a gabanta.
Matsowa yayi daf da ni ya kwantar da kaina a wuyansa yana shafa fuskata, cikin salon soyayya yake min magana wallahi bana so na tafi na bar ki amma hali ya kama dole na tafi na bar ki.Xan kasance cikin kunci da bakin ciki a cikin wannan daren,musamman idan dare ya tsala bakya kusa da ni, fatana dai ki kula min da kanki duk abinda doctor ya hana ki daina yi mana don tabbatar da lafiyar jaririn mu,rungume ni yayi kamar baxai sake ni yana sumbatata ta ko ina, cikin shagwaba na bashi amsa xan kula maka dattijona, rike hannuna yayi ya tsura min ido kamar xai yi kuka bana gajiya da kallon kyakkyawar fuskar ki Niimatullah, ba don kada su innah su ga kamar nayi rashin kunya ba da a nan xan rika kwana.
Murmushi nayi tare da lumshe ido yanzu ma xaka iya dawowa ai dama ba kunya ne da kai ba,jan hancina yayi xaki ga ba nida kunya idan na tattaro kayana na dawo nan, harararshi nayi dawo din mana, bayana ya koma ya sakalo hannunsa ta wuyana, cikin rada yake min magana.
Yau xan yi irin baccin da na dade ban yi irinsa ba Allah ya sani bana so na tafi na bar ki,kina samun sauki xan xo gobe na tafi da ke don baxan iya wannan xaman hakurin ba.
Marairaice masa nayi kamar xan yi kuka dan Allah kayi hakuri ka barni dattijona kaga a nan innah xata kula da ni kuma baxan rika shiga damuwa ba. Tsare ni yayi da ido yana kallona idan kince haka Niimatullah ni kuma ya xan yi da soyayyarki na riga nayi sabo da ke baxan iya zama babu ke ba,kawai xan xo gobe na tafi da ke yau dai na hakura ki huta.Duk nacin da nayi masa a kan ya barni na xauna har na haihu amma yaki, sallama muka yi sannan ya xaro kudi ya bani.
Bayan ya tafi innah ta shigo cike da tsokana take min magana, har kun gama rashin kunyar ko Niimatullah, wato har kin goge kin san dadin miji yanzu ba a kawo min karar laifin da yayi,hannu biyu nasa na rufe fuskata Allah ba haka bane innah hira kawai muka yi.
Murmushi tayi dama nima ai ba wani abu nace ba, mayar da kallona nayi gareta, kafin na fara magana har idanuna sun fara hawaye, cikin rawar murya nace innah wallahi ina cikin matsala dalilin hakan ne ma yasa kika ga na dawo gida.
Cike da fargaba ta fara tambayata saboda bata san irin matsalar da naxo mata da ita ba, cikin kulawa take magana, matsalar Menene Niimatullah?har xuciyata ta shiga fargaba wlh bana so naji an ambaci matsala.
Goge hawayen da ya fara sakko min a idanuna nayi sannan na fara yi mata bayani, wallahi innah matar dattijon nan ta takura min da xagi da cin mutunci, baro bangarenta take yi ta taho wajena kawai don ta tayar min da hankali,kwanaki ta kawo min wani magani tace na sha da naki sha shi ne jiya taxo ta hau xagina ta kama ni da kokawa har da cewa sai ta xubar da cikina, ni dai wallahi innah na hakura da auren nan baxan koma ba, ya nemi wata matar ya aura.
Tunda innah ta sunkuyar da kai bata dago ba saboda abin ya daure mata kai, cike da damuwa ta dube ni, kiyi hakuri Niimatullah kowace rayuwa da kike gani akwai jarrabawa a ciki baxai yiwu a ce kina xaman aure kuma kina samun abinda kike so dari bisa dari ba,dole sai kin yi hakuri da matsalolin da xaki fuskanta, ke ki godewa Allah ma da ba mijinki ne yake wulakanta ki ba kishiya ce, don haka ki cire damuwarta a ranki ki fuskanci abinda ke gabanki ki farantawa mijinki, kuma kada na sake jin kin ambaci Kalmar saki a bakinki.
Kwantar da kaina nayi a jikinta ina kuka, dan Allah innah ki taimake ni ki raba ni da auren nan wallahi ni nasan irin axabar da nake sha a hannun matar nan, indai ba so ku ke bakin cikinta ya kashe ni ba to ku raba ni da mijinta.
Rarrashina innah ta rika yi tana kwantar min da hankali.
*****
A bangaren Hajiya Maryam kuwa kwanan farin ciki tayi domin duk a tunaninta cikin Niimatullah ya xube sai kiran kawayenta take yi a waya tana fada musu, fitowa tayi tana kewaye gida tare da leka kanta bangaren Niimatullah samun kofar tayi a kulle, wani dadi taji ya ratsa xuciyarta, tasan cewa Niimatullahi na asibiti tana cikin wani hali.
Motar dattijo ta hango na kokarin shigowa cikin gida da sauri ta koma wajenta ta xauna a parlour, yana ajiye motar ya shiga wajenta, kawai ganinshi tayi a kanta yana huci kamar xai dake ta ya fara yi mata magana.
Burin ki na son hallaka abinda na dade ina burin mallaka a rayuwata bai cika ba kuma baxai cika ba har abada, domin wannan cikin ya fi karfinki sai dai ki kalle shi kiyi kuka,kuma wallahi ki nutsu tun wuri ki kama mutuncin ki idan ba haka ba kuma xaki ga hukuncin da xan xartar a kanki...
Fita yayi ya bar mata dakin, wani tsallen dadi tayi har a ranta tana jin ta fara samun nasara, girgixa kai tayi tana magana, kawai nasan fada yake yi amma wannan dukan da nayi mata dole yasa cikin nan ya tashi daga aiki,masifa kuma yanzu aka fara ta har sai ta gudu don kanta.
Dattijo na shiga bangaren Niimatullah yaji gidan ba dadi, komawa parlour yayi ya kwanta tare da daga kansa sama, gaba daya gidan yayi masa xafi ji yake kamar ya dau mota ya tafi ya dakko matarsa, juye-juye ya rika yi don a yanzu babu abinda yafi bukatar gani a kusa da shi fiye da Niimatullah.
*follow me on wattpp@jeeddahtulkhair Tijj*
*jeeddahtulkhair😘*
YOU ARE READING
MATAR DATTIJO Complete
RomanceLabari ne mai cike da soyayya tare da fadakarwar da nishadantawar wa, akwai darasi mai yawa da mata zasu dauka dangane da zama da kishiya