MATAR DATTIJO page 41

1.1K 41 0
                                    

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
          *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

41

Da karfi na rike kafar shi ina masa magiya,dan Allah ka dawo dattijona kayi hakuri ka kyaleta kada kaje kayi masa magana har da dan guntun hawayena, xaunawa yayi yana mayar da numfashi cike da nutsuwa ya dube ni, ina ji a raina baxan samu nutsuwa ba har sai na samu matar nan na ja mata kunne ta fita a harkar cikin nan tun kafin igiyar aurenta tayi rawa, cikin marairaicewa nake masa magana, kayi hakuri dattijona ka kyale ta yanzu idan kaje ka fada mata xata canja wata hanyar ne kuma ta haka ne xata samu damar cutar da mu, girgixa kai yayi haka ne Niimatullah na fahimce ki.

Tun daga wannan ranar yasa mata ido baya bari ya fita ya barni ni kadai, ita ma tunda taga haka sai ta daina shigo min gaba daya sai dai idan ya dan fita ta saci jiki ta leko mu gaisa, wannan dalilin yasa na kara gane tana da wani mugun nufin a kaina tunda gashi bata shigowa a lokacin da dattijo yake nan,sai ta tabbatar da baya nan take xuwa.
Yau da safe bayan dattijona ya fita nima na fita don yiwa mai gadi magana a kan wani sako da aka bar min, ta saman bene ta hango ni da sauri ta sakko wajena da fara'arta ta karaso inada nake cike da ladabi na gaida ita, cikin sakin fuska ta dafa kafadata, murmushi tayi sannan ta fara yi min magana kin yi amfani da abin nan kuwa Niimatullah? kaina a sunkuye na amsa mata da eh nayi Aunty yana da kyau sosai Allah ya bar xumunci.

murmushi tayi tare da cewa ba komai kanwata kin fi haka a wajena, kokarin ja na da hira tayi tana bugun cikina a kan xamana da dattijo ni kuwa kin hirar nayi na hanxarta na koma bangarena.

Rayuwa nake cikin farin ciki ni da mijina babu wata matsala da nake fuskanta daga gare shi, cikina kuma na cikin koshin lafiya don laulayin da nake yi duk na fara samun sauki, yau kusan sati uku kenan da bani wannan maganin a tunaninta xan samu wata matsala amma shiru babu labari.

Don haka ta sake dawowa, yau ranta a bace na ganta don kana kallonta xaka gane cewa bata cikin walwala, sallama tayi min cikin sakin fuska na amsa mata tare da bata wajen xama ta xauna, tabe baki tayi tare da cewa ba xama ne ya kawo ni ba,cike da mamaki na dubeta ki xauna mana Aunty ya naga duk ranki a bace ko wani abin ne ya faru?

Yatsina fuska tayi ko ban fada miki ba kin san da abinda ya faru,don haka kawai baxa ki ganni a wajenki ba,sakin baki nayi ina ganin yadda take jujjuya idanu kamar xata dake ni..

Cigaba da magana tayi, nayi asarar kudina na baki magani amma baki yi amfani da shi ba ko gani kike xan cuce ki ne?cikin marairaicewa nace ai nasan baxa ki cuce ni ba, nayi amfani da shi tun a ranar da kika bani, dakatar da ni tayi kada ki raina min hankali ki mayar da ni karamar yarinya mana, idan har kin yi amfani da shi wlh xan sani kuma yanzu ma nasan baki yi amfani da shi ba kawai kin fada ne,don haka yi sauri ki bani abuna kafin na yi miki rashin mutunci.

Tsareta nayi da ido ina kallonta jira kawai nake naga kalar rashin mutuncin da take cewa xa ta yi min. Sake daka min tsawa tayi ke nake jira ki dakko min kayana kafin na saba miki kamanni na illata ki yanxun nan.

Cike da mamaki na dubeta wai me kike fada ne haka da har kike cewa xaki illata ni,dole ne don kin bani abu sai kin san nayi amfani da shi ko ban yi ba?nace da ke ina bukatar wani abu ne da xaki kawo min ko an fada miki ni irinki ce salam ba test? Wani duka ta kawo min Allah ya bani sa'a na kauce, cikin xafin rai take min magana.

Wallahi yau babu mai raba ni da ke a gidan nan sai kin gane ba ki da wayo,ranki sai ya baci yau sai na xubar da cikin nan sai dai duk abinda xai faru ya faru, kokawa muka fara yi ta buga ni jikin bango Allah ya bani sa'a nima na turmusheta tana dukana ina ramawa, babban burinta kawai ta daki cikina Allah bai sa ta cimma burinta ba kokawa muke yi sosai ni da ita,kwantar da ni tayi tana bugun cikina, kokarin kwatar kaina na rika yi.

Ban Ankara ba naji ta saki wani ihu ashe dattijo ne ya dawo ya kai mata duka,kokarin raba mu ya rika yi amma taki sakina sai dukana take yi Shi ma dukanta ya rika yi ba sasautawa har sai da ta sake ni, cikin fushi yake mata magana dama ba ki da hankali maryam me yasa xaki xo wajen karamar yarinya ki hau kokawa da ita kuma alhalin kin san tana da karamin ciki.

Da karfi ta danki wuyan rigarb shi na gaji da bakin cikin da kake cusa min a cikin gidan nan wallahi yau ko ni ko kai a gidan nan,sai inda karfina ya kare don a yau sai na barar da cikin nan kowa yayi asarar sa, yana jin ta ambaci barar da ciki yayi wurgi da ita ya kulle kofa ya kyaleta a waje tana masifa.

Wajena ya dawo yana duba jikina sannu Niimatullahi, shi yasa tun tuni naso naje na yiwa tumfar hanci amma kika hana ni gashi nan taxo tana neman cutar mu.

Kwantar da kaina nayi a jikinsa duk jikina ciwo yake yi, rarrashina ya shiga yi yana cigaba da duba cikina, wani kara yaji na saki cikin tashin hankali ya karaso wajena yana tambayata,lafiya Niimatullah me kuma ya faru? nuna masa cikina nayi jini ya gani yana xuba daga jikina cike da tashin hankali ya fara jijjiga ni ki taimake ni Niimatullah kada cikin nan ya cube dan Allah.

Daukana yayi cikin rashin hankali ya fita da ni ya saka ni a mota.

*Follow me on wattpad @Jeeddahtulkhaeer Tijj*

*jeeddahtulkhair😘*

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now