MATAR DATTIJO page 39

1.1K 52 0
                                    

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*jeeddah Tijjani*
       *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*dedicated to Zee fulani*

*Bansan da irin bakin da xan gode miki ba aminyata ta kaina maijidda Bello naga abin arxiki na gode Allah ya bar xumunci*

39

A hankali ya rika jan kafa har ya isa wajen Niimatullah, duk ransa a bace yake saboda wulakancin da matarsa tayi masa a gaban abokinsa, nadama  ya rika yi  a ransa ba yasan  abinda xata y masa kenan da bai bari sun je wajenta  ba.

A sanyaye ya karaso wajena cikin sassanyar murya ya kira sunana, ni  kuwa banda aikin kuka babu abinda nake yi, a hankali yasa hannu ya dago kaina ganin yadda fuskata ta jike da hawaye ne yasa hankalinsa ya tashi cike da damuwa ya dube ni, niimatullah kin manta akwai jaririn cikina a jikin ki kike kuka, baki san kuka yana illata mai ciki ba hannu yasa ya fara share min hawayen tare da yi min magana.

Kiyi hakuri amaryar dattijo Alhaji Hamza bai fahimci halin ki ba ne shi yasa ya fadi wannan maganar a kan ki, amma ko yanxu sai da ya Kara yabon ki ya kuma tabbatar min da cewa nafi kowane namiji sa'ar abokiyar rayuwa saboda yadda kike kula da ni kuma kike gudun bacin raina, kiyi hakuri ki daina kuka wallahi ina matukar kaunar ki.

Hawaye ya shiga share min, sai da ya tabbatar da hankalina ya kwanta sannan ya kyale ni, a  ranar cikin farin ciki muka kasance.

Washe gari da sassafe dattijona ya fita  Office, kasancewar yana da aiki da yawa a office, bayan na gyara gida na fito parlour na kunna TV ina sauraren wa'azi a tashar sunnah TV, turo kofar dakina aka yi da sallama aka shigo nayi mamakin jin sallamar saboda ban taba xaton wadda ta shigo xa tayi min sallama ba, cike da mamaki na dubeta tare da saurin mikewa tsaye don ban san da abinda taxo min ba.

cikin sakin fuska ta karaso gare ni tare da neman waje ta xauna, ganin yadda ta saki ranta ne yasa na gaida ita cikin sakin fuska ta amsa min, komawa nayi na tsaya saboda xuciyata bata amince na koma na xauna ba saboda ina tsoron kada ta turmushe ni tunda ta nuna a xahiri bata kaunar cikin da ke jikina.

ajiyar xucuya tayi tare da kiran sunana niimatullah,a hankali na dago na kalleta kirjina sai dukan uku-uku yake yi saboda tunda naxo gidan nan bata taba yi min kallon rahama ba ballantana har ta ambaci sunana.

Tsayar da idona nayi a kanta ina jiran jin abinda zai fito daga bakinta, cike da kulawa ta fara magana, hmm nasan xa kiyi mamakin ganina a wajen ki a kuma irin wannan lokacin, kaina a kasa na amsa mata da ina jin ki.

Murmushi tayi tare da cewa ya naga kamar bakya cikin nutsuwar ki ni fa naxo ne mu yi sulhu, mu ajiye dukkan makaman yakin da muka dauka, nasan nayi kuskure a kan abubuwan da na rika yi miki dan Allah kiyi hakuri mu tsaya mu nutsu mu kwantarwa da mijin mu hankalinsa.

wani sanyi naji ya ratsa xuciyata saboda ni bana son tashin hankali ina son naga muna xaune lafiya ko don mu farantawa dattijo, cike da sakin fuska na fara yi mata magana, ba komai aunty Allah ya yafe mana gaba daya dama ni bana jin dadin irin abinda muke yi insha Allah xaki same ni mai yi miki biyayya.

Cike da kulawa ta dube ni yauwa kanwata na gode dama dadyn Munir ya dade da fada min cewa kina da saukin kai ashe kuwa abinda ya fada haka ne, murmushi nayi kawai ba tare da na bata amsa ba.

Wani abin mamaki na gani tare da ita duk motsin da nayi idanunta a kan cikina har sai da na tsargu saboda kallon da take bina da shi ya shallake tunani, daki na shiga na sanyo hijabi sannan na dawo, a xuciyata na kosa ta wuce ta tafi tunda mun fahimci juna amma ta xauna tana bina da mayataccen kallo.

cikin kasalalliyar murya ta sake kiran sunana wanda har sai da naji gabana ya fadi, ba tare da na amsa ba na dago na kalleta, murmushi tayi bakya son na rika ganin cikin jaririn da xaki haifa mana ne shi ne kika sako hijabi ko, rufe fuskata nayi a'a ba haka bane aunty, rausayar da kai tayi haka ne mana kanwata, Allah dai ya kawo mana babyn nan lafiya ya sha lele. Murmushi muka yi gaba daya.

Mikewa tsaye tayi tana gyara mayafinta bari na tashi na koma wajena, akwai yan aikace-aikacen da ban karasa ba, tashi nayi na bi bayanta don yi mata rakiya sai da muka kai bakin kofa ta juyo ta dube ni.

Naji dadin yadda kika karbe ni hannu biyu ban taba xaton zan samu hakan daga wajen ki ba ganin yadda muka samu sabani da ke a baya na gode sosai, wani abu ta miko min aleda karbi wannan amaryar mu, hannu biyu nasa na karba.

kallona ta cigaba da yi, nasan baki san abinda na baki ba ko? Girgixa kaina nayi alamar eh, dafa kafadata tayi tana min magana, saboda karbar da kika min hannu biyu yasa na baki wannan tukwicin, ki duba ki gani gumbar mata ce tana kara niima sosai yadda angon nan naki yake xumudi a kan ki idan kika sha har kyautar mota xai baki, wata mata ce take kawo mana tallanta office, ina siya sosai kuma naji dadinta, shi yasa kema  na  siyo miki, kada kiyi wasa kisha yana da kyau.

Karba nayi tare da yin godiya sannan muka yi sallama.

*follow me on wattpad @jeeddahtulkheer Tijj*

*jeeddahtulkhair😘*

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now