💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)**follow me on instagram @jeeddahtijjani*
51
Haka suka cigaba da kasancewa a cikin wannan hali na kunci da tsangwamar mahaifiyar su,gaba daya ta daina damuwa da su, kullum ni nake basu abinci duk shawarar da suke bukata wajena zasu xo, don ko yan kallo basu isheta ba, duk yadda dattijo ya so yayi musu sulhu taki sakkowa tun yaran suna damuwa har suka koma suka dangana. sun shafe kusan wata biyu a wannan hali ni kuwa dama ko haduwa muka yi na gaisheta bata amsawa, bana damuwa da dukkan abinda take yi saboda na riga nasan halinta.
Tun daga wannan lokacin muka shaku da su sosai, babu abinda xa su yi ba tare da na sani ba, kuma sai sun nemi shawarata, shi kansa dattijo nasa ya kara jawo yayansa a jiki saboda a da ko hira baya xama yayi da su,saboda irin abubuwan da mahaifiyar su take masa.
Munir ne ya shigo bangarena da sauri fuskarsa na gani cike da walwala, karasowa yayi wajena xaune ya tarar da ni ina ninke kayana,cike da ladabi ya tsugunnah ya gaida ni, waje ya samu ya xauna sannan ya dube ni, Aunty yau surukar ki xata xo ta kawo miki xiyara me kike ganin ya kamata a shirya mata, farin ciki ne ya bayyana a fuskata naji dadi sosai da yaxo min da maganar aurensa saboda na kosa yayi aure ko don ya huta da matsin lambar da yake fuskanata daga mahaifiyar sa, cike da kulawa na bashi amsa xan shirya dukkan abinda ya kamata kada ka damu, amma da ka sani ka fada da wuri don a san abubuwan da xa a yi. murmushi yayi tare da cewa na gode Aunty, amma abinda yasa ban fada muku ba ina so ku yi mamaki ne sosai, yana gama fada ya mike xai fita har ya kai bakin kofa na kira shi, ina fatan dai ka fadawa mama don bana son taji abin daga sama, dan naxarin maganata yayi sannan ya bani amsa ban fada mata ba Aunty saboda nasan baxa ta karbi maganar ba, sauke ajiyar xuciya nayi ina kallon shi, kayi hakuri kaje ka fada mata saboda ka fita hakkinta a matsayinta na mahaifiyarka, bai yi min musu ba ya fita don sanar da ita, sai dai ban san yadda suka karke ba don bai dawo ya fada min yadda suka yi ba.
Kai tsaye daki na shiga tarar da dattijona nayi kwance yana hutawa cikin nutsuwa na karasa inda yake, shafo fuskarsa nayi ina murmushi naxo maka da wani babban albishir don haka baxan fada maka ba sai ka biya ni ladana, tashi yayi daga kwanciyar da yake ya matso kusa dani ya makale ni a kirjinsa fada min babyna ko nawa ne xan biya amma kafin lokacin ga wannan tukwicin, sambatata ya shiga yi ta ko'ina sai da ya kammala ya dube ni wannan shi ne tukwicin ki na farko na biyun na nan xuwa, fada min na bude kunnuwana ina sauraren ki.
Narkewa nayi a jikinsa albishir naxo yi maka ka kusa samun suruka kaima a haifa maka jika, fuskarsa cike da farin ciki yake min magana da gaske kike amaryar dattijo ko kuma tsokanata kike yi?
Lumshe idanuna nayi, da gaske nake dattijona munir ya samu matar aure anjima ma yarinyar xata xo ta gaishe mu, rungume ni yayi naji dadin wannan albishir din naki amaryata dama na damu yaron nan yayi aure ko don ya samu yanci daga wulakancin da maryam take musu, sai kace ba ita ta haifi yaran a cikinta ba kullum a cikin fitina. rausayar da kai nayi hakuri xa mu yi da ita dattijona tunda Allah ya hada mu dole mu daure mu xauna da ita haka, kuma ya kamata mu rika yi mata addua sannan kaima ka rika jawo hankalinta a kan ta daina irin abubuwan da take yi.
Sake manna yi yayi a kirjinsa na gode matar dattijo gaskiya ke mace ce ta gari, kina nuna min abinda ya dace da ban yi dace da ke ba da tuni kin rikita gidan nan saboda kina da kuruciya da iya soyayyar da xaki iya juyar min da tunani, amma ga shi kullum kokarin nuna min abinda yake dai-dai kike yi.
Kwantar da kaina nayi tare da shafa gashin da ke kewaye a fuskarsa, hakkina ne na dawo da kai hanya idan xaka karkace ita ma Auntyn xata dawo yadda muke so insha Allah, amsawa yayi da Allah yasa amaryar dattijo.
Cike da shagwaba na dube shi, dattijona xan je na fara hadawa bakuwar mu abinci, kallona yayi yana dan hararata dubi fa abinda ke jikin ki a haka xaki ce xaki yi musu girki, ni sam ban yarda ba restaurant kawai xan aika a yi musu order amma matata baxa tayi aikin wahala ba.
Marairaicewa nayi kamar xan yi kuka, ni fa ba haka muka yi da shi ba dattijona, ya fi son nayi musu komai da kaina, dafa hannun shi yayi a kaina, ni kuma nace baxa a yi ba ko, kin ma janyowa kan ki tunda aikin kike so sai kin kula da ni yanzu.
Aika min da sakonni ya shiga yi har sai da ya kashe min jikina.Magiya na fara yi masa amma ko saurarata bai yi ba sai da ya Isar da abinda yake so.
Da misalin karfe hudu ya kira ni a waya cewa sun kusa isowa, a lokacin na shirya musu koma, fada masa nayi ya fara kai ta wajen mamansa kafin ya kawo ta wajena da farko ya nuna kin amincewarsa ga hakan saboda da yaje ya fada mata bata saurare shi ba.
Hakuri na bashi na kuma nuna masa girman hakkin da mahaifiyar sa take da shi a kansa.Ba mu dade da waya ba suka iso ta window na hango su sun shiga sashin Maman sa, dawowa nayi na xauna don jiran shigowar su.
Da sallama suka shiga bangarenta, tana ganin shi da budurwa ta mike tana nuna shi da hannu, munir kada ka fara kaaraso min nan, dama ba kada hankali, me ya hada ka da budurwa yanzu?to tun wuri ku bace min da gani ba yanxu xan aurar da kai ba.
Cikin rawar baki ya dubeta xai mata Magana da sauri ta dakatar da shi bana son jin komai daga gareka kawai ka fitar min daga gida, saura kuma naga ka tsaya wani gurin, jikinsa a sanyaye ya tashi yarinyar ta bi bayan shi.
Suna fita ya rika bata hakuri a kan abinda aka yi mata sannan ya roketa da taxo su shiga wajen Niimatullahi kememe taki amincewa saboda wulakancin da aka yi mata, da kyar ya sha kanta ta yarda xata je, a bakin window Hajiya maryam ta tsaya don ganin inda suka nufa, tana ganin sun nufi bangaren Niimatullah ta shiga daki ta dakko xabgegiyar wayar television.
Kai tsaye bangaren Niimatullahi ta nufa cikin xafin rai ta tura kofar shiga wajen.....
*follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*
*jeeddahtulkhair😘*
YOU ARE READING
MATAR DATTIJO Complete
RomanceLabari ne mai cike da soyayya tare da fadakarwar da nishadantawar wa, akwai darasi mai yawa da mata zasu dauka dangane da zama da kishiya