chapter 2

151 4 0
                                    


ZAITUN

******

Azabure ta miki tana waige waige jin an zungureta da karfi .

Mamakine ya cikata ganin mutum agabanta itadai a iya saninta jiya kafin bacci ya dauketa ta rufe kofar da key .

Kamar ko yasan metake tunanin ya zaro ey din daga aljihun wandon shi na baya ya girgidashi .

"Extra key hope u know it and didnt forget its my house "ya fada yana karewa dakin kallo .

Ko alamun tabashi ba'ayi ba bare a gyara barnar dayayi jiya kwapa yayi ya zagayeta ya nufin cikin dakin yana wani ya mutse fuska kamar yaga kashi .

Baki itama ta tabe ganin abunda yakeyi ta wuce cikin bandakin ta dauro alwala.

Koda fito baya dakin jin ana kiraye kirayen sallah yasa tasan dalilin fitar tashi .

Koda ta idar da sallah bata tashi daga gurin ba lazumi da karatun alkur'an tayi har garin ya fara haske .

Chan wajen bakwai bacci ya fara gaba da ita tajiyo hayaniya daga waje har dai hayaniyar tafara shigowa cikin dakinta da sauri ta miki ganin mutum agabanta sai huci yake kamar bashine ya shigo dakinta dazuwa ba duk da dai bawani fara'a yayimata ba amma atleast fuskarshi ba a hade take ba kamar yanzu .

Wata katuwar jaka ya cilo mata aiko da ita da jakar suka samu mazauni a kasa . Dago kai tayi da sauri ya kauda kanshi ya nunata da yatsa yana wani huci kamar zaki .

"Pack your things and leave my house this instant  " ya fada a tsawace " ohhh t forgot that baki zo da ko tsuma ba right "ya fada yana wani murmushin mugunta .

Wani irin bugu zuciyar maimunatu tafara yi ga wani faduwa da gabanta yake numfashinta ko harwani tsere yake nason futowa .

Wata tsawar ya daka mata daya hargitsa mata yayan cikin da sauri ta dauki jakar da ya cilo mata tin farkon shigowarshi tayi saurin fita daga dakin.

Tofah anan akeyinta ko hanyar fita bata sanin ba bare tasan unguwar datake harta nemi motar hawa komawa gida .

Karo taci dawata yar datijuwar mata dukda kwaliyar da taci bai boye tsufanta ba sai sheka dariya take da sauri maimuati tabar gurin ganin kamar baa haiyacibta take ba tanemi hanyar fita daga gidan .

Wata kofa ta hango datake tunanin palour ne a ciki bako bata lokaci ta murda kofar aiko palour dine da sauri take tafiya hartana hade hanya itakam gidan ma gaba daya tsoro yake bata sai ga hawaiyen suna tseren sauka ian kuncinta ta .

"Anty bara na rakaki "tajiyo wata murya a bayanta yar budurwace da bazata wuci shekarunta ba kota fita da kadan doguwace fara  siririya , masha Allah tanada kyau dai dai gwargwado amma daga ganin ba yar gidan bace dub da irin shigar datayi riga da zani ne da da kwalli amma kowane daban .

Abaya nake binta kamar jela  masha Allah gidan ya hadu iya hadu amma sai dai kash bai dace da yan gidan ba.

A harabar gidan mukaci karo da wani bawan Allah matsakaici ne atsayi baki mai da kauri ya saka rigar shadda blue da jeans wando blue dariya ha hau yi ganin mun kusa karasowa . Gaisheshi sukayi yako amsa da dariyarshi magana budurwar data rakoni tayi naji ya amsa da toh safiyya.

Mota ya dauko a gareji ya karaso da ita dap damu tace kishiga ko zai kaiki hargida sai hakuri muma hakanan muke hakuri muka zauna saboda neman halal amma matar gidanan bt da girki ko kadan ta karashe maganar abun tausayi .

Murfin motar ta bude tana mun sallama tareda mun alkawarin ziyara idan ta samu lokacin .

Titi muka hau sai gudu yake don ya samu ya koma akan lokaci kar hajiya ta mai masifa .

"Kiyi hakuri ko wlh banson abunda zai hadani da hajiya yau danko abun bazai mun dadi ba" ya fada idonshi  bai bar kan titin ba.

"Lah ba komi baba ai kama taimaka mun danko sunan unguwar ma bansani ba bare nasan inda na nufa"  .

"Aikinsan hajiya ba daganan ba akwai masifa ga rashin hakuri kanar zawo "ya karashe yana yar dariya.

Dariyar itama ta tayashi dan ta lura shi din akwai hira ga abun  dariya ga kuma saurin sabo .

Hira sosai mukeyi harna soma mata damuwar danake ciki . Dai dai kofar gidanmu dayasha fenti brown colour gakuma wani gyara da akamai bayan tafiyata  lailai Alhaji yayi aiki .

Kirjinta ne yake bugawa kanar zai fado sanin abunda zata tarar agidan sanin halin uwartata.

Godiya tawa driver dan har suka iso batako san sunanshi ba sanan ta kinkimi jakar ta ta nufi hanyar cikin gidan.

Shiru kamar alamun bakowa kenan duk yan biki sun watse  . Dakin umminta ta nufa kirjinta na tsanaita bugu da sallama ta shiga dakin ga mamakinta taganta cirko cirko a tsaye kamar dama jiran isosarta take . Amasar jakar hununta tayi sanan taja ta zuwa kan gado suka zauna .

" Tun dazu nake jiran isowarki" tafada tana murza hanunta .

Atsorace ta dago idon ta zuba matasu tana son gano mai umminnata take nufi .

"Ummi tundazu kuma mai kike nufi daman kunyi dashi zan dawo ko daman kinsan haka zata faru"ta jiro mata waenan tambayoyi idon kuru akan mahaifiyar tata.

Shiru tayi ganin bata da alamun amsa mata tambayoyin data zabgo mata sai ma niyar mikewa dataga tana shirinyi.

Saurin mikewa itama tayi tariko mata hannunta batajin zata iya koda motsawa batareda ta samu amsoshinta ba .

"Ummi baki bani amsata ba haba ummi kinfada mun mana kona daina sarkayi a zuciyata " tafada murya na rawa .

Zama tayi tareda kamo hannun diyarta  ta zuba mata idanunta cikin nata .

" kiyi hakuri maimunatu naso na sananda ke yace nukayi da Alhaji bulama kafin auren amma sai dai kash abun ya ci tura jama'ar gidan sunyi yawa  " tafada tareda kawar da kanta gefe .

Wani das taji a zuciyarta wani makoko ne ya tsaya a wuyanta yaki wucewa me take nufi da yace sukayi da Alhaji?was the marriage under condition ?was there anything ummanta needed that she had to agree with his  condition?  Ta tambayi kanta without getting  any of her answers .

"Ummi now talk to kifada what were the conditions da kukayi dashi plz "she was already tensed tasan Alhaji bulama  is not a cool guy  amma if shi beyi tunani ba ne isa ummi bazatayi ba .

"The condition was that he will provide us with komi  he made a stupid promise to his wife and had to fullfill it "she smirked .

Why will ummi of all people agree with this stupid condition to her own daughter for goodness sake inshi bashi da hankali ai ita tanada . Koba komi sun maida ita karama bazawara kalamar bazawarar data fada yasa gabanta mumunan faduwa innalilahi wa'ina illahi rajiun they have destroyed her life.

Mikewa tayi tana hawaye tanufi dakinta upon all the kira da umninke mata citake kamar ta kashe kanta wlh she hate her life wallahi.

Kan gado tafada sai kuka carrrrr kamar an tunzurata kuwa sai zabgashi take tasan da mahaifinta na da rai bazayimata haka ba . Tunawa dashi yasa ta mike ta nufi wardrobe dinta ta ciro picture dinshi kamarsu daya sosai kamar an tsaga kara farine dogo mai jiki amma ba sosai ba yanada long face da kuma tana dauke da murmushi daya dace da long nose dinshi with bulgy eyes and pink lips so masha Allah ga curly hair dinshi na fullani . Ya rabbi grant this soul with Aljanna tafafa tana hawaye she niswed hin so much .

Haurawa kan gadon tayi ta rungume picture din Abu dinta agirji tana mai addua hartaji zuciyarta tafara sanyi chan kuma tashiga tunanin yace rayuwarta zata kasance yanzu datake karamar bazawara abaya ma ya ta cika bare yanzu.

"Allah kayi mana jagora ka datar damu "tafada cikin kuka da tausayin kanta da rayuwar sasuke ciki .

Ko cikaken hour batayi ba bacci yayi awon gaba da ita daman agajiye taje ga ciwon da kanta yakemata ga rashin  bacci da bata samu ba jiya  tuni bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita .



MAIMUNATUWhere stories live. Discover now