Chapter 7-10

143 4 0
                                    

"MAIMUNATU"

💖💕Dedicated this chapee to my one and only sweetheart 💓💘💕 Asma'u Muhammad (husna) thanks 🙏  for ur support  u will for be in mah heart,  much luv sweety 💗👄.

*****
5:30 pm

Hayaniya Maimoon ta faraji sama sama Dan bacci ne mai nauyi akanta.
Da kyar ta mike daga kab gadon ta nufi hanyar fita Kawai taci karo da wani abu aiko da sauri ta matsa Tana duba kafarta, wasu akwatuna tagani mash kyau kalar Gold sai sheki suke daga gani Sabine  rashin sanin maisu yasa ta tsallakesu tayi wuce warta Dan ganin hanyaniyar me takeji a tsakar gidan nasu.

Ga mamakinta mutane tagani makil kamar gidan biki Ita a iya sanninta ba... Wani mugun faduwa gabanta yayi  data tuna wai Ashe ya daurin aurenta da mijin kawar ummanta wani makokone ya tokare mata a makogaro g wani juyi da kanta yakeyi.

Dafata taji anyi ta baya jiyo tayi ta hada ido da Anty halima kanwar mahaifinta wace rabon data ganta tun ranar arbain din babbanta wani guntun hawayene ya gangaro fuskarta gani haka yasa Anty Halima tajata wani daki a soron gidan idan babu kowa ta rufo kafar ta zaunar da Ita Dan gaba daya tausayin yarinya ya adabeta.

"Mamana "ta fada a nutse gani tayi raurau da ido tana neman yimata kuka.  Tana kiranta Mamana saboda taci Sunan mahaifiyarta.

"Dan Allah ki nutsu ki bani nutsuwar ki inaso muyi magana " tafada tana kawar da kanta Dan gudun kar makalalen hawayenta ta zubo.

"Mahaifiyarki jiya taje gida take fada mana wai aurenki ya taso wai ayau kenan zaa daura babu irin masifa da ranshi yarda da Baba bai nuna ba amma ta murzawa idonta kwalli taki yarda wai ai yartace babu yace muka iya hakanan muka hakura amma da gudurin yau da sassafe zamuzo Amma Mamma ta hanamu da kyar tabari nataho di daya.

Tsagaitawa tayi ganin tana neman hi mata kuka,  jawota tayi jikinta tafara rarrashinta.

"Kiyi hakuri  Mamana Hakanan taki kadarar take saidai muta miki addua  Kiyi hakuri kiyiwa mijinki biyayya kizauna da yaranshi da matarshi lafiya Allah yayi miki Albarka tana kaiwa nan ta miki ta zameta daga jikinta tafice Dan idan ta cigaba da zama zasu hadu suta kuka ne.

Babu yace ta iya kuka ne Kawai a yanzu zai sassauta mata radadin da zuciyarta takeyi.  Tana ta zabga kuka change tajiyo muryar umman tana tambayar ko sunganta sai masifa take wai bata shirya da wuri ba ga yan daukar amarya sunzo.

Ba yace ta iya hakanan ta mike jiki babu dadi taja kafafuwanta ta fita daga dakin a tsakar gida ta tada umman tana ko ganinta tayo kanta sai kumfar Baki take kamar wace ta gudu.

Janyota tayi tayi dakinta da Ita bata ko kula da halin da take ciki ba.  Halin ko in kula take mata yarta gama shiryata ta zaunar da Ita tana Kara mata kashedi Ita alailai karta kuma nemanta ta rasa.

7: 30 pm

Tanan zaune babu Wanda yashigo dakin sai budar mutane datakeji yana tunkaro dakin runtse idonta tayi wai itace zaakai gidan miji Hasubanalahu waniimal wakil abunda bakinta ya iya furtawa kenan sai innalilahi wa inailaihi rajiun datake ta jerowa.

Manya manyan mata ne su uku sika shigo dakin ciki harda umma sai wani fara take Ita a lailai autar ta tayi aure.

Zama sukayi kan gadon suka farayi mata nasiya su ala dole nasiha mai kyau suke mata.

In banda hudubar banza babu abunda suke hada mata daga me cemata ta juyashi yace zata kori matarshi ta malake yaranshi sai mai cemata zasu hado mata magungunan agurin malaminsu yace zata zama matar gidan sai kuma hajiya umma wace Ita burinta bai wuce suci dukiya ba.

Ahakadai suka Karaci suki burutsunsu suka gama aka dauketa.

Mota suka shigar da Ita fuskarta  arufe take Dan haka bata san suwaye a gefenta ba.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 09, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MAIMUNATUWhere stories live. Discover now