*******
As usual da wuri na tashi na kamala garan gidan kafin umma ta tashi daga bacci .Rayuwa kenan kawai yace gidan mu yake ada na tuna so lively wallahi Abba was an extraordinary man .
"Tunanin me kike tun dazu inata magana "ta zunguri ganin tafi kusan mintuna nawa akaina .
"Bakomi Umma kawai ia tunanib rayuwa ne "ta mike ta nufi hanya dakinta sai kuma tajiyo tana magana.
"Yo Allah na tuba mai kika sani a rayuwar da har zakiyi magana"ta fada tana tabe baki.
Yar dariya tayi ra wuce a ranta tana fadin niko nasan rayuwa tunda har aka aurar dani a shekaru 16 aka kuma sakeni a washe garin da aka kaini kwafa tayi tashi daki dan yanzu lamuran ummanta ya fara bata tsoro da haushi.
Shirin kumawa makaranta tayi dan bata karasa ss3 ba aka katseta , sabon registration tayi awata school tafara zuwa da kudin da Alhaji yabata duk da umma ta karbu wasu .
Karatu take sosai bata kula kule , dan wani lokacin mantawa ta taba aure . Adadape tana cancana kudinta har Allah yasa ta kamala kartunta tayi waec ,neco da jamb murna agunta ba'a magana .
"So finally i am done with secondary school saura University ko Umma"ta fada tana fara . Sun zauna zaman hira itada ummanta da wani daren Asabar bayan results dinta duk su fito kuma masha Allah duk sunyi kyau .
"Eh insha Allahu maimunatu sai jami'a wayagakin a jami'a"tafada suka kwashe da dariya.
Ba lefi gidan yana dan mata dadi koba komi yanzu suna hira sosai kuma suna samun 3 square meals dinsu Allhmdllh.
*******
2 months laterChan na hango mlaimunatu sai sauri take zabgawa gudun kar malamin da take nema ya bar office din dan ance mata baze dade ba .
Sunanta taji an kira daidai lokacin data karaso hanzari takara ta cusa kanta cikin dumbun jam'ar dake jiran nasu sunan . Hanya suka bata tashige cikin office din da sallamarta .
" Good morning sir tafada tanemi gurin zama " kwafa tayi ganin bashida alamun dagowa bare ya saurareta .
"Maimoon Haroun Muhammad sir "tafada ahankali gudun kartayi lefi . Ganin yana binciken abu acikin tarin papers din hanunshi yasa tayi ajiyar zuciya daga dukan alamu yaji sunnanta .
Dagowa yayi da idonsa ya kalleta sannan yakuma mayar dakanshi . Babban mutum ne wanda bazai wuce shekaru 45-50 ba amma inhar ba kallon nutsuwa kamai b bazaka iya gano tsufansa ba kyakyawa ne ba karya ga nutsuwa daga gani kuma addini ya ratsa shi boko da Arabi .
Zaro wata takada yayi ya miko mata sannan ya bukaci wasu credentials dinta kafin dagq bayq yace taje wurin HOD din department dinsu tabashi wasu paoers din da photocopy din wace ya bata , jiki a sanyaye ta miki ta nufi hanya pita gudun karya sauke fushinshi akanta dan taga alamu ranshi a bace yake .
Da tambaya ta samu office din HOD din nasu tabashi abunda waccen yace tabashi sai a gurinshi taji wai shine registrant dinsu.
Allah ya taimaketa ta kamala komi kawai sigining na Course Registration form (CRF) baa yi mata ba shima wai suntashi sabida 6 tayi. Agajiye ta karasa gidan tun 8 data fita sai 6 tadawo gaba daya kamaninta sun chanza saboda wahala. A tsakar gida ta tarar da Umma tana girkin dare a murhu ,kusa da ita taje ta zauna tana maida numfashi ga gajiya ga kuma yunwa datake adabarta .
Miko mata kwanon data zuba mata abincin tace ta cinye tashigo daki suna da magana . Ba musu ta amsa ta fara ci .
Bayan ta gama cin abincin ta wanke kwanukan da suka bata kafin ta amsa kiran ummanta . A tsaye ta isketa sai safa da marwa take a tsakiyar dankin kamar mai jiran tsamani .
YOU ARE READING
MAIMUNATU
RomanceMaimoon was brought up by a single parent (mother) whom because of self-interest sold her own daughter into marrying different men in because of greediness of luxury.