****Gaba daya gidan ya cika da hayaniya koke koke kawai kakeji na kananan yara da kuma buda da manya sukeyi don murna .
Gefe guda koh uwar amarya ke kai kawo cikin gidan tanata dawainiya da baki.
Ranar asabar kenan ranar da aka daura auren diyarta tilo Maimoon Haroon da Alhaji Bulama .
Dakin da aka aje amarya Anty talatu kanwar uwar amarya ta leko ta sanarda su cewa a shirya amarya yan daukarta sun karaso . Aiko sai daki ya kuma hargitsewa kowa ya shiga shiri dan kowa na son zuwa ya ganewa idonshi dan kashe kwarkwatar idonsu.
Motocine ajere kowace sai sheki takeyi tsavar kyau dakuma alamun tsadarta .
Lodasu abokanen ango suka farayi ganin dare ya soma yi aiko himili guda aka kwashesu kusan motoci 5 sukayi aka nufi gidan amarya .
******
Akatafaren katon gate din Alhaji Bulama dake Nasarawa GRA suka danna horn dagudu mai gadin ya wangale gate din tareda wangale baki yana wa amarya barka da zuwa .Cikin kantamemen gidan aka shiga da amarya maimoon wacce fuskarta arufe da babban mayafin mai kauri. Part din da aka ajeyi domin amarya aka kaita kowa sai fadin albarkacin bakinshi yake iya haduwa gidan ya hadu kamar aljanar duniya .
Dakinta aka kaita aka ajeyeta masu nasiha suna mata masu leke leke sunata fama . Itako amarya inbanda rusa kuka ba abunda takeyi kamar tashike.
Da kadan kadan yan kai amarya suka fara watsewa ya rage daga amarya sai kawayenta .
Chan dare wirin 11 abokanan ango suka rako ango kawayen amarya sukazo agaugauce aka yi siyan baki suka basu kudi ko jayyeya basuyi ba suka basu ganin dare yayi kowa ya kama gabansa .
Ango ne ya dawo daga raka abokanensa ya tada amarya adukunkune agefen gado sai kuka take . Ahankali ya haura gadon yae dap da ita ya fara magana ahankali.
"Amarya kinsha kanshi dazaki bar kukannan zuwa anjima dayafi "ya fada da wata iriyar murya kamar dan shaye shaye.
Ido ta zaro waje duk da ba kallonta yake ba , yo me yake nufi da tabar kukanta sai anjima chab dinjam idan ma abunda take tunani yake magana to wlh bai isa ba ayace takeji da kankantar shekarunta idan aka kusanceta shikenan ta kamu da cuta to wlh bazai yiyuba .
Kokarin zame mata mayafin kanta ya farayi ako ta kankame mayafin ta cukuikuyeshi ta sa akarkashin kafarta ja yafarayi ahankali ganin taki saki yasa ya fizgishi da karfi ya wular dashi a kan kafet ya kuma yin yunkurin warce mata dan kwalin kanta aiko da hanzarinta ta miki tana jada baya sai zaro ido take.
Ranshi ne yayi mugun baci ganin tana kokarin bata mai lokacin , binta yayi tako fara ja dabaya baya yana binta harta kai jikin bango ganin ta makure sai kara binta yake dataga dai da gaske yake sai ta saki wani irin wawan ihu da ita kanta saida ta razana ganin haka yayi sauri ya wawuro pot flower din kusa da dressing mirror din ya buga shi da bango .
Ganin dai bazata bashi hadin kaiba yasa yayi wani irin wurgi da ragowar glass din hanunshi ya daki dressing mirror aiko atake ya tawarwatse sannan ya bugi bangon da hannunshi kafin ya fice tareda bugo kofar dakin.
kamar jiratake da sauri ta nufi kofar harda dan tuntube tayi saurin sawa kofar key . Ahankali ta zame ajikin kofar ta rushe da wani irin kuka mai soya zukatun mai sauraro .Wannan wace irin rayuwace ace an aurar da kai kankanin shekaru (16) sannan kuma ga sa'an babbanta wanda bataso takuma tabata mahaifiyarta saboda kudi ta aura da ita .
Kuka tadingayi mai tsuma zuciya chan kuma tafara ajiyar zuciya tana karanta "Allahuma ajirni fi basibati wakalifni khairan minha" dawasu ayoyin alkurani sannan taji zuciyarta tafara sanyi anan dukurshe tasoma bacci batareda tasani ba har bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita .

YOU ARE READING
MAIMUNATU
RomanceMaimoon was brought up by a single parent (mother) whom because of self-interest sold her own daughter into marrying different men in because of greediness of luxury.