ƘPage 1

5K 319 27
                                    

*ƘADDARAR RAYUWA*

Zaynab bawa
Wattpadd@zeyybawa

Haske writers association💡

Alhamdulillahi Allah nagode maka daka bani damar fara rubuta wannan littafi kura kurenda zan rubuta aciki Allah yayafemin wanda nayi dai-dai kuma Allah yabani ladansa, Godiya ta tabbata ga ubangiji mai kowa mai komai daya bani damar dawowa mukuda wannan labari bayan hutun shekara d'aya."
Makaranta littafina inaso kusani shi d'an adam akullum tara yake bai cikawa goma, idan nayi kuskure cikin rubutuna ina maraba da gyara amma banda cin fuska,
Yawwa sannan kuma abuna gaba book dinnan yanada yawa kada nafara rubutu qananun magana su taso akan cewa inajan book kamar yanda yafaru abook dina na baya, Allah yasa mudace Amin."

Page 1
Iska sosai ake kad'awa yayinda ko'ina yadauki sanyi, qura ta lullu6e ko'ina yayinda aka samu karancin wucewar jama'a saboda qarfinda iskar take dashi, yanayinda ake ciki agarin yanayine mai cikeda ban sha'awa da d'aukar hankali
Domin iska busawa takeyi tako'ina ka dukkan alamu hadarine mai qarfin gaske yakeson had'uwa,
Ganyayyaki na bishiyoyi sai kadawa sukeyi suna bada iska mai dad'in gaske.*

Cikin qanqanin lokaci hadari yahad'u sosai garin yayi baqin qirin, daga nan gari yad'aure hadari yafara bugawa alamun kowani irin lokaci ruwa yana iya sauka."

Yanda hadari ya hadu alamu yanuna ruwa zai zuba sosai, duk wani mahaluki kamata yayi ace yanemi hanyar gida, saboda Allah kadai yasan lokacin tsayawar wannna ruwan idanya barke,

Wanda yake waje kuwa to tabbas hankalinsa bazai kwanta saboda gabaki daya hankalinsa zaiyi gidane.

D'an muskud'awa yayi akan y'ar yololuwar katifarsa, wanda yakejin bugawar hadari dakuma tsawa kamar wanda zai rusa gidan yafad'o akansa, saboda rashin qarfin ginin da dukkan alamu ginin yadade sosai gashi na qasane hattada rufun kwanon yatsufa yayi tsatsa,
Daga yanda yake kwance yana hango yanda hasken walqiya yake ratsowa ta bulellen bugun kwanan, ya tabbata yau idan akayi ruwannan d'akin sai yayi yoyo'
Nisawa yayi sannan yaSanya hannu ya lalu6o wayarsa itel mai torch wacce taji jiki sosai idan ka ganta a'ido bazakayi tunanin tana amfaniba,
Kunna torchin yayi sannan yajuya gefe ya dubi wacce take gefensa tana kwance, d'an bubbugata yayi yana fad'in daga kwanciya har kinyi bacci'
Cikkn muryar da take nunida tafara bacci amma baccin baiyi nisaba tace" tukunna dai,
Ajiye wayar yayi agefe yana fad'in kinga hadarine yahad'u sosai agarinnan yarinyarnan kuwa tadawo?
Nishi tad'anyi sannan tamiqe tazauna tana mutsutsuka idanuwa sanda tad'an watssake sannan tace" yanzun qarfe nawane?
Tara da kwtaa yabata amsa ayayinda yake kallon lokacin ajikin wayarsa,
Cikin halin rashin damuwa tace aii tanafin hakama domin tana kaiwa har da rabi ko wuce hakama,
Eh nasani amma yanzun hadarine agarin sosai, kuma wannan ruwa idanya barke Allah kadai yasan lokacin tsayawarsa, hankalinku bai kamata ya kwantaba sanin cewa diyarmu tana waje koda nine nake waje wannan lokaci na tabbata hankalina gida zaiyi, jira tayi sanda yagama maganar sannan ta muskutawa tace yanzu hakama tadawo tana d'akinta ai taga hadari bazata bari takai hakaba, idan tadawo nasan dakinsu zata shige dan idan nayi bacci kasan bata tashina, gyada kaii kawai yayi yakoma ya kwanta amma badan hankalinsa ya kwantaba."

Sauri-sauri takeyi tagama had'a kayanta takama hanyar gida saboda yanda hadari ke bugawa,
Ido tatsura ma wasu samari wanda ga dukkan alamu su take jira su gama su bata kwanonta takama hanyar gida,
Had'e jikinta tayi tatakure awaje d'aya saboda iska da akeyi ga wani irin sanyi da yake shigarta, sun d'an dauki lokaci kafinnan suka gama suka miqa mata, sauri-sauri ta kar6a tahad'e cikin kayanta takama hanyar gida, wani irin tsorone yashigeta tafiya takeyi cikin sauri saboda bbu kowa ahanya kafa tad'auke, ga kuma wani irin duhu da hanya tayi, wani lokacin sai hadarin yad'an harba kafinnan take hangen hanya,
Batayi auneba tajita ta buge mutum dasauri taja baya cikin tsoro saboda kokad'an bata lurada waniba itadai kawai taji ta bugi mutunme,
Wani irin nishi taji mutumin yanyi kamar wanda ake shirin zare ransa ga dukkan alamu baida cikkekken lafiya,
Gudu tayi niyyar arcewa dashi saboda atunaninta aljanine,
Amma ina kafin tayi wani yunkuri wannan mutumi yakamata wanda baya iya kallon fuskarsa saboda baqin da garin yayi,
Ihu ta kwala tana neman taimako amma babu wanda yajiyota saboda yanayinda garin yake ciki,
Sun batu tafarayi tana fad'in" dan Allah kuyi hakuri bansan ku bane awajan yasanyani nabi hanyar harna bugeku bansaniba, tana fad'in haka ita atunaninta cewa aljanine,
Ita bata saniba wannan mutumi wani nufi daban yake dashi akanta,
Cikin qanqanin lokaci yafara qoqarin aiwatarda mummunan nufinsa akanta, hakan yayi dai-dai da sauqowar ruwan sama, duk ihunta takeyi babu wanda yajiyota sakamakon ruwan sama dayake sauka da qarfi, har saida yagama aiwatarda nufinsa akanta."

ƘADDARAR RAYUWATahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon