5 Habib 2 And The Crisis

94 9 0
                                    

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONS

*Abin da wanda ya ji tsoron wasu mutane zai fada:*

اَللَّهُمَّ اكْفِنِيهِمْ بِمَا شِئْتَ.

Allahummak finihim bima shi'ita.
Ya Allah! Ka isar mini su da abin da Ka so.

_*Habib 2 and the crisis*_....

Suhaila ta daɗe a inda take tana juya maganar da Surayya ta sanar da ita. Ta ina ma zata fara idan ya kira me zata faɗa mishi, ta san dai Surayya baza ta taɓa cutar da ita ba, kuma idan da ace yana da wasu halaye da ta sanar da ita, kuma baza ta taɓa yarda ta amsa mishi ba ballantana ma har ta kai ga sanar da ita.

Haka dai tayi ta tunani har lokacin sallah yayi.

Bayan ta idar da sallah ne ta yanke shawarar kiran fatima taji ko sunyi nisa sosai daga nan sai ta sanar da ita, don ji take baza ta iya bari har sai ta isa gida ba, gudun kar ya kira ta kuma bata san me zata ce mai ba.

"Assalama alaikum".

"Wa alaikum Salam, Suhaila ya dai? lafiya dai ko?

" Yes lafiya lau wallahi, Amma akwai maganar da zan sanar da ke please ki bani shawara yanzu".

"To ina jin ki Suhaila".

"Ina Uncle ɗin Surayya, wanda jiya naje gaida shi a gurin convocation".

"Uhmm ina jin ki me ya faru da shi?

" Cewa yayi wai yana so na shine nake tunanin idan ya kira ni a waya wacce amsa zan bashi".

"Hmm Allah ya shirya ki dai wallahi, ki ce mai go to hell kawai".

"Haba ya Fatima don Allah fa".

"To Suhaila idan banda abunki, abunda ake nema ya samu har ki tsaya kina sanya ma".

"Am just scared wallahi, tunda ta faɗa mun sai naji hankali na sam be kwanta da abun ba wallahi".

"Anya kuwa baki da aljanu Suhaila?

Sai da Suhaila ta tunzuro baki gaba kamar Fatima na kallon ta kafin ta ce" Ni wallahi lafiya  ta lau babu abunda yake damu na, kawai naji be yi mun bane".

"To ai shikenan sai ki yanke duk hukuncin da yayi miki, kuma dama ba shawara kike nema ba kin bugo ne kawai ki bani labari".

"To shikenan bari zanyi istikara mu gani, abunda Allah yayi ai shikenan".

"Okk ki gaida Ammi"

"Zata ji. Kunyi nisa ne? Kun kai ina yanzu?

" Hmm sai da kika gama faɗar buƙatar ki tukunna. Gamu a zariya mun kusa shiga Kaduna".

"Ayya ki gaida mun babies ɗina please".

"Ahan, ma'asalam".

"Bissalam".

*****

After Suhaila tayi sallar isha'i ta shiga gurin Ammi don sanar da ita halin da ake ciki nan ta same ta itama akan prayer mat daga gani Bata daɗe da idar da sallah ba.

"Ammi barka da dare".

"Barka dai, ya aka yi?

Sai da Suhaila ta tattaro duk wata nutsuwar ta, ta sunkuyar da kai ƙasa kamar me neman gafara kafin ta fara magana a hankali.

" Ammi dama Surayya ce ta kira ni ɗazu take ce mun wai akwai wani ƙanin maman ta da yazo taron mu na jiya shine ya ce ayi mun magana, zai zo ya ganni".

"Tofa! Ikon Allah, ni kuma kinga ban ganshi ba wallahi, amma ai babu komai idan yazo munga yana yin shi ko".

"To Ammi dama cewa nayi bari na sanar da ke".

AL'AMARIN SUHAILA Where stories live. Discover now