11 Heat Break

103 6 0
                                    

GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION ✍️✍️

Addu'ar Neman Biyan Bashi

اللّهُمَّ اكْفِنِي بِحَلالِكَ عَنْ حَرَامِكَ، وَأَغْنِنِي بِفَضْلِكِ عَمَّنْ سِوَاكَ.
Allahummak-finee bihalalika 'an haramik, wa-aghninee bifadlika 'amman siwak.

Ya Allah! Ka wadatar da ni da abin da Ka halatta barin abin da Ka haramta, kuma Ka wadatar da ni da falalarka ga barin waninka.

اللّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْهَمِّ وَالْحُزْنِ، وَالعَجْزِ وَالْكَسَلِ وَالْبُخْلِ وَالْجُبْنِ، وَضَلْعِ الدَّيْنِ وَغَلَبَةِ الرِّجَالِ.
Allahumma innee a'oothu bika minal-hammi walhuzn, wal'ajzi walkasal, walbukhl, waljubn, wadal'id-dayni waghalabatir-rijal.
Ya Allah! Ina neman tsarinka daga kunci, da bakin ciki, da kasawa, da lalaci, da rowa, da tsoro, da nauyin bashi, da rinjayen mazaje.




Abunda ta gani ba komai bane kuwa illa *"NI HABIB MANSUR NA SAKI MATA TA SUHAILAT MUHAMMAD SAKI BIYU, A DALILIN BAYAN AUREN MU NA GANO ITA BA CIKAKKIYAR BUDURWA BACE"*.......

Suhaila kam ji tayi kamar an luma mata wuƙa a ciki, nan da nan jinta ya ɗauke, yawun bakin ta ya ƙafe, idanun ta kuwa kamar an zuba mata yaji domin wani raɗaɗi suke mata gashi nan da nan ta fara gani dusu dusu, babu ƙwalla ko a ɗaya a cikin idanun nata, tana daga tsaye inda  take ta saki takardar  hannun ta kafin ta faɗi daɓas, Allah ma ya tamaketa bata faɗi akan mugs ɗin da suka fashe ba.

Wani irin ihu ta fasa wanda ni da nake gurin sai da na girgiza tsabar tsoro, shi kuwa gogan yana tsaye kamar an dasa bishiya ko motsawa be yi ba amma fa sai dai akwai tsantsar tausayin ta a idon shi, ji yayi gaba ɗaya zuciyar shi ta karaya kamar shima ya fasa ihun irin nata, ganin ba zai iya jurewa ba yasa ya juya mata baya yana me runtse idanun shi da suka kaɗa suka yi jazur. A hakali ya fara furta"Am really sorry SUHAILAT ki yafe mun amma bazan iya cigaba da zama da ke a gidan nan ba, ba zan iya jurewa ba, bazan iya mantawa da daren mu na farko ba, duk kuwa da cewa ba don budurcin ki na aure ki ba amma na rasa me yasa na kasa jurewa. Suhala bana son na shiga haƙin ki ko kaɗan shiyasa kawai naga wannan hukuncin shi ya kamata na ɗauka, ki yafe mun don Allah, Allah ya baki mijin da ya fini komai da komai,ba abunda zan iya ce miki yanzu sai dai Allah ya haɗa kowa da rabon shi, and also, you can stay here har sanda zaki yi iddar ki, na tafi ki yafe ni don Allah".Ya ƙarashe maganar yana bin hanyar da zata sada shi zuwa tsakar gidan.

Ita kuwa Suhaila da tunda ya fara magana ta tsaya tana kallon shi with her dry mouth, abun ma abun mamaki really Habib ya sake ta, shikenan yanzu zata koma gidan Ammi, shikenan yanzu ta zama bazawara, shikenan shikenan.

Jin ya ɗau hanyar barin palon yasa ta fara rarrafowa tana bi ta cikin broken mugs ɗin da suke zube a ƙasan carpet ɗin gurin ba tare da ta sani ba, ba tare da ta ji zafin da yake ratsa ta ba, wanda idan mutum yana cikin hayyacin sa sai da kawai muce Allah ya kikaye. Gudu gudu sauri sauri ta ƙarasa inda yake tana me riƙe ƙafar shi.

Cakk ya tsaya yana jin yadda ta ƙaƙume mai ƙafa kamar her life depend on it.

Cikin gushewar hankali da rashin sanin abunda take faɗa tace"Don Allah, don son ka da soyyayar fiyyayen halinta kayi haƙuri, ka janye maganar sakin nan, wallahi ban san irin halin da zan shiga ba idan har ka barni, Habib sai da nayi shekara ishirin da biyar kafin na samu nayi aure, Habib idan na koma gidan mu ban san wacce irin rayuwa zanyi ba, Habib idan ka rabu da ni zan shiga cikin wani yanayi, Habib you are my cynosure, my first love, my first husband, Albi ina sonka don Allah ka bar zancen sakin nan mu cigaba da rayuwar mu plsss don Allah, wallahi a shirye nake na maka duk wani abu da kake so amma don Allah kar ka rabu dani na roƙe ka don Allah". Ta ƙarashe maganar ta sakin wani kukan me cin zuciya.

AL'AMARIN SUHAILA Where stories live. Discover now