45..Finding Solutions

89 10 1
                                    


*Bintu Ahmad*

*Wattpad@cynosure3*



*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Addu'a Idan Mutum Ya ga wani abu mai ban Mamaki, ko na farin ciki*

سُبْحَانَ اللهِ!
Subhanal-lah!.

Tsarki ya tabbata ga Allah.

اللهُ أَكْبرُ!
Allahu akbar

Allah ne mafi girma.

*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. 👇

https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp

_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._



Nigeria, Kano.

Da misalin ƙarfe 9 na safe Umma da Zainab suka gama shiri don zuwa wajen wani malami, babu ɓata lokaci suka ɗau hanya sai da suka yi tafiya me nisa sosai sannan suka isa don a ƙalla sunyi kusan 1hour a hanya, wani ɗan daji suka shiga wanda ba shi da wani duhu sosai don daga nan ma kana iya hango ƙauyikan dake gefan gurin, a hankali suka taka zuwa cikin ɗakin dake gurin babu ko sallama suka danna kai, ita kuwa Zainab sai zare ido take kamar an farauci ɓera, wani gwalangwace nasu na bokaye yayi musu hakanne yasa cikin Zainab yayi mugun ƙullewa, kallon ta mamanta tayi alamar ta kwantar da hankalin ta babu wata matsala.

"Me ke tafe daku?".

Muryar Bokan ya daki kunnen su, cikin dagiya da jarumtar Umma wanda dama daga gani ta saba zuwa tace; "Boka wata yarinya ce ta tsaya mana a hanya, ta hana mu rawar gaban hantsi shine muke so a mana maganin ta, ta kowace hanya mudai fatan mu kawai Zainab ta auri Ahmad".

"So kuke a kashe ta kenan!?"

Zainab ce tayi saurin girgiza kai"A'a ina so a batta a raye idan son samu ne ma, ta zama ƴar aikin gida na sai abunda nace".

Dariya bokan yayi yace; "To ai aikin ki ma me mugun sauƙi ne kuma anfi saurin samun nasara, zaki aure shi kuma zata zama a ƙarƙashin ki sai abunda kika ce za ayi".

Murmushi Zainab tayi tana riƙe hannun Umman ta alamar za su samu nasara.

Wani surutu yayi akan wani ruwa sai ga hoton Ahmad da Suhaila ya bayyana a cikin ruwan, kwance suke a kan gado sai bacci suke kowa ya shige jikin ɗan uwan shi.

Wani irin murmushi Hajiya tayi yayin da Zainab ta haɗe rai ganin su a haka.

"Kar ki ji haushi ƴan mata har yanzu be kusance ta ba".

AL'AMARIN SUHAILA Where stories live. Discover now