9EMBER

97 8 0
                                    

Wattpad@cynosure3

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

Hawayen da yake zubo mata ta share kafin tace" I WAS RAPED BY 3 MEN A SHEKARU SHIDA DA SUKA WUCE, don haka don't ever call me a prostitute!".

Komawa tayi ta zauna a bakin gado tana cigaba da kuka, ji take Ina ma ace irin wannan ranar bata zo mata ba. Duk wani baƙin ciki da azaba, da hantara da kuma wariya a lokacin da abun ya faru da ita suka dawo mata sabo fil.

Shi kuwa ya tsaya a bakin ƙofa kamar wani gunki ya kasa motsawa kuma ya kasa ce mata komai.

Ganin dai alamar ba shi da niyyar neman ƙarin bayani yasa ta share hawayen fuskarta ta dawo bakin ƙofar inda yake tsaye ko motsawa be yi ba.

Hanun shi ta sa cikin nata tana me murza su alamar rarrashi, ɗayan hannun nata tasa ta shafo gefan kumatun shi kafin a hankali tafara tafiya da shi zuwa palo.

Shi kuwa sai binta yake kamar wani wawa, yayi wani sakato sai ka ce irin down syndrome ɗin nan.

Akan 2 sitter kujera tayi musu mazauni, bayan ta zauna tayi placing kanta a ƙirjin shi tana me cigaba da murza hannun wanda take jin daɗin sofness ɗin shi.

Cikin nutsuwa da kwantar da hankali ta fara magana"Am really sorry Albi na san munyi lefi duk kuwa da cewa  nayi insisting amma kaƙi sauraro na, sannan kuma Abbu shima yayi nauyin baki da be sanar da su kawu Alhaji ba, kuma nasan shi tunanin da yayi na riga da na sanar da kai shiyasa har ka yarda zaka aure ni. Albi i was raped by arm robbers a shekaru shida da suka wuce, and then ban san dalilin su nayin hakan ba dumin kuwa ko kuɗi basu tambaya ba they just raped me and leave, kuma bayan ni babu wanda suka taɓa a gidan".

*_"But then this is not the end of the story, wannan kawai kake da haƙƙin  sani". ta faɗa a cikin ranta_*

Ƙara gyara kwanciyar ta tayi tana daɗa shigewa jikin shi, shi kuwa gogan ko gezau be yi ba kuma babu wani abu da yaji ya sauya a can ƙasan zuciyar shi

Jin shirun yayi yawa yasa ta ɗago kai ta kalle shi, nan ta ga fuskar nan babu ko alamar tausayi ko kuma wani change of emotion.

Tashi tayi ta zauna, tafi 10 minutes tana kallon shi amma be ce mata komai.

Hannun ta takai zata ƙara shafar gefan kumatun shi ya riƙe hannun gam yana watsa mata wani kallo me kama da gargaɗi.

Yasar da hannun gefe yayi kafin ya tashi akan kujerar ya nuna ta hannu yana faɗin"Kina tunanin wannan labarin ƙanzon kuregen da kika bani shi zai sa na yarda da ke? Never wallahi, you cheated me,kin gama da ni, kuma wallahi Allah ya isa tsakanina da ke, soyyayar da nayi miki da damuwar da na shiga saboda ke ban yafe ba".

"Kuma ki sani wallahi wallahi bazan bar wannan maganar a iya tsakanin mu ba ki jirayi abunda zai faru". Ya ƙarashe maganar yana ɗaukan keys din motar shi.

Da gudu taje ta sha gaban shi harda su tsugunawa tana bashi haƙuri amma ina be ko saurare taba daga ƙarshe ma haɓar ta ya kama ya matse mata baki kafin ya hanƙaɗa ta gefe har sai da ta bugu da dining area ɗin da ya ƙawatu da flowers masu shegen kyau da sheƙi, ai kuwa nan komai ya kama gaban shi, flower verses ɗin gurin duk suka fashe tartsatsin kwalba ya fasa mata ƙafa ga kuma bakin ta shima da ya fara futur da jini saboda tsabar matsar da ya sha.

Ko kallon inda take be ƙara yi ba ya fice acikin gidan.

_*Ni kuwa nace ohhhh namiji kenan duk ina su I love you ɗin take? you are my life, can't leave without you, you are my happiness, idan babu ke bazan iya rayuwa ba, na ƙagu mu kasance tare,duk suna ina? Kenan duk ƙarya ne? Virginity ɗin ta kawai yake yi wa? Ohhh maza kenan  sai dai Allah yasa mu dace*_

AL'AMARIN SUHAILA Where stories live. Discover now