Unexpected

1.8K 155 4
                                    

*_BAHAUSHIYA𖣘︎_*

 

   😭𝘏𝘢𝘵𝘵𝘢𝘳𝘢 𝘠𝘢𝘯 𝘔𝘢𝘵𝘢💔


𝙆𝙖𝙘𝙤𝙠𝙖𝙣 𝙇𝙞𝙩𝙩𝙖𝙛𝙞𝙣 𝙎𝙖𝙙𝙖𝙪𝙠𝙖𝙧𝙬𝙖 𝙘𝙚!
𝙕𝙖𝙞𝙣𝙖𝙗 𝘼𝙗𝙙𝙪𝙡𝙡𝙖𝙝𝙞 𝙒𝙖𝙯𝙞𝙧𝙞! 𝙈𝙖𝙢𝙖𝙣𝙖🥰
𝙈𝙖𝙝𝙖𝙞𝙛𝙞𝙮𝙖𝙩𝙖 𝙩𝙖 𝙠𝙖𝙞𝙣𝙖! 𝙄𝙣𝙖 𝙩𝙨𝙖𝙮𝙚 𝙣𝙚 𝙨𝙖𝙗𝙞𝙙𝙖 𝙠𝙖𝙧𝙛𝙞𝙣 𝘼𝙙𝙙𝙪'𝙖𝙧 𝙙𝙖 𝙠𝙞𝙠𝙖 𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙪𝙣𝙙𝙖 𝙧𝙖𝙣𝙖𝙧 𝙙𝙖 𝙠𝙞𝙠𝙖 𝙝𝙖𝙞𝙛𝙚 𝙣𝙞 𝙝𝙖𝙧 𝙕𝙪𝙬𝙖 𝙔𝙖𝙪😘🥰😍, 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝 𝙮𝙖 𝙜𝙖𝙛𝙖𝙧𝙩𝙖 𝙢𝙞𝙠𝙞 𝙙𝙖 𝙍𝙖𝙝𝙖𝙢𝙖!🥰😍

Unexpected

Babi-Biyu.

  Cukume wuyar rigarta nayi cikin tashin hankali da dimauta, nace.
"Dan jin tsani tarayya na dashi, shine zaki bijiro min da labarin kanzon kurege! Meye na tsare miki Fatimah? Bakin cikin kike da samuna!"

       Cire hannuna tayi daga rikon da nayi mata.

       "Dalla ki nutsu! Wallahi ban fada miki dan na cutar dake ba! Na gaya miki rufa rufar da ake miki ne! Husnah HABIB meye sai sanya ya miki hassada, Husy! Wake up, tashi daga barci da kike yi Dr Aahil Aliyu maitama jibu warhaka yana cikin jerin angwaye."

          Zan iya cewa naji jerin angwaye, daga nan ban kuma sanin inda kaina yake ba, sai da akayi sallar asuba.

            Tashi nayi zaune, na kalle ta tana azkar, sai naji kunya ta kamani, a cikin wata shida kacal sallah asubar ma sai rana ya fito.

    Zama nayi na fashe da kuka, sosai, sabida na zalinci iyayena,
Nayi watsi da tarbiyyan da suka min, nayi fatali da kimata,. Hawaye ne ya zubo min.

     Tashi nayi naje nayi alola sannan na koma daki nayi sallah, ina zaune, kasancewar muna da ajin yau jumma'a,Bayan ba idar da sallah kuka na cigaba da yi sabida bakin ciki da abinda Dr A.A yayi min.l shiryawa nayi cikin sauri na dauki hijab dina,  ganin Yadda Hadiri ya hadu har da ita yasani fitowa.

           Ester wata bakatafiya wacce muke course daya da ita ta kalle ni, cikin jin dadi tace.
"Our Superb! Da wuri zaki tafi Class kin manta Mr Arrogant ne a ajin yau."

    Karamin murmushi nayi wanda ya boye b'acin rai na, na kalle ta kadan sannan nace mata.
"My Superb ai kece, gwana dan naga Kina mutuwa akan Dr Bature Yohana Chibok! Ni kuwa ko akan kafa aka daura min zan gudu na bari."

             "Allah sarki! Husy! Am sorry, amma kinsan waye Dr Bature Yohana Chibok! Baban shi Baban Pastor ne. A churchi din Christian Centre Of God."

Cikin jin haushi na katseta da cewa.
"Dalla kiyi min shiru! Uban me zan miki da bani labarin shi wai ku me kuka dauke mu! Mu musulimai bamu san abinda ya dace ba ko me? Wannan damuwar shi ce amma karki manta addina na gare Ni, addininku na gare ku."

   Tunda ta fahimci yau bani cikin jin dadi da zan kalubalence ta, sai ta share, ita ta wuce ni kuma na dawo hostel, na dauko takardan project dina, kuma ina son tabbatar da abinda Teemah ta gaya min.

   Cikin sauri na saka kai zan shiga sai naji muryan Teemah tana cewa.
"Wallahi ku ji tsoron Allah, meye ribarku na zama yin gulmarta, wai me yasa bamu gane rayuwa ne! Na rantse da Allah! Husy bata da lokacin ku, sabida ita goben ne a gabanta, kunsan me yasa Allah ya bada soyayyar mutane! Saboda bata taɓa burin zaluntar wasu ba, shi yasa kome tasaka a gaba bai bata wahala, tana da ilmi Yes! Kone ina mamakin Yadda take jan Point, dana zauna sai nayi nazarin, Husnah bata tab'a fashin aji ba, Husnah bata tab'a."

BAHAUSHIYA.....!?Where stories live. Discover now