girls-education

1.3K 129 5
                                    

_BAHAUSHIYA𖣘︎_*

 

   😭𝘏𝘢𝘵𝘵𝘢𝘳𝘢 𝘠𝘢𝘯 𝘔𝘢𝘵𝘢💔

𝙆𝙖𝙘𝙤𝙠𝙖𝙣 𝙇𝙞𝙩𝙩𝙖𝙛𝙞𝙣 𝙎𝙖𝙙𝙖𝙪𝙠𝙖𝙧𝙬𝙖 𝙘𝙚!
𝙕𝙖𝙞𝙣𝙖𝙗 𝘼𝙗𝙙𝙪𝙡𝙡𝙖𝙝𝙞 𝙒𝙖𝙯𝙞𝙧𝙞! 𝙈𝙖𝙢𝙖𝙣𝙖🥰
𝙈𝙖𝙝𝙖𝙞𝙛𝙞𝙮𝙖𝙩𝙖 𝙩𝙖 𝙠𝙖𝙞𝙣𝙖! 𝙄𝙣𝙖 𝙩𝙨𝙖𝙮𝙚 𝙣𝙚 𝙨𝙖𝙗𝙞𝙙𝙖 𝙠𝙖𝙧𝙛𝙞𝙣 𝘼𝙙𝙙𝙪'𝙖𝙧 𝙙𝙖 𝙠𝙞𝙠𝙖 𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙪𝙣𝙙𝙖 𝙧𝙖𝙣𝙖𝙧 𝙙𝙖 𝙠𝙞𝙠𝙖 𝙝𝙖𝙞𝙛𝙚 𝙣𝙞 𝙝𝙖𝙧 𝙕𝙪𝙬𝙖 𝙔𝙖𝙪😘🥰😍, 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝 𝙮𝙖 𝙜𝙖𝙛𝙖𝙧𝙩𝙖 𝙢𝙞𝙠𝙞 𝙙𝙖 𝙍𝙖𝙝𝙖𝙢𝙖!🥰😍

girls-education

Babi-hudu

        Da farin cikin suka dawo, tare da alkawarin baza su bari kowa yasani ba sai cikin ya nuna kanshi.

      Tunda suka dawo Baba ya zamewa Innarmu kamar Jela, idan tana aikin wahala fada yake sosai, har ta kai Innarmu ko ruwan wanka bata kai mishi, ƙomai na niman lada ya hanata, inda yake cewa.
"Ba damuwa Zainab, Ni zanyi aikin Allah ya baki ladan."

   Wannan sauyin ya sanya aka shiga cewa Innarmu tayiwa Baba faraku. Da Yadiko,.yana ji amma yayi biris da kowa.

      Haka suka gama surutunsu babu wanda ya tanka musu, kwatsam sai ga Yadiko Rakiya da ciki.
     Allah ya gani baba yaso suke birni a duba cikin amma suka daurawa kansu muguwar al'ada.

                 Haka suka zauna har cikin Innarmu ya fito, ranar da Yadiko ta kyalla ido taga cikin Innarmu,  bata kwana ba sai da cikinta ya zube, sabida mugun nufinta a kan Innarmu, sai aka shiga cewa toh Innarmu tasan abinda ta taka.
       Sabida Jahilci, da duhun kai da rashin hankali irinta mutanen kauyen.
              ...... Tafiya tayi nisa inda tasaka mutanen da suke bayan Yadiko suka fara hijira zuwa bayan Innarmu. A hankali kome ya sauya.

      Cikin Innarmu yana cika wata tara, aka shiga kawo mata rubutu daga Kakanmu Malam Manga. Tana sha tana shafawa a cikin.

        Sai da Cikin ya wuce kwanakin shi sannan, Allah ya d
Sauketa  lafiya, inda aka samu mace.
     Murna a gurin Baba ba a magana, dan tunda aka kawo ni gurin Malam Manga, yake satar kallona. Murmushi Malam Manga yayi sannan yace.
"Ina bawa kowa Zabi a kowacce haihuwa, musamman na fari, sai dai wannan karon ka taimake ni na sanya mata Asma'u"

          A son iyayena idan namiji aka samu, zasu sanya mishi Abdullah, idan mace ce kuma zasu sanya mata Amatullah!

  Sai gashi Malam Manga ya min huduba da Asma'u, kasancewar Baba yayi zaman maraya,(birni) sai yace toh a kirani da Husnah.

        Haka aka yi kuwa, Husnah ya karaɗe gidanmu, Idan na gaya muka girman gidanmu zaka sha mamaki, domin kuwa Babban gidane.

        Satin suna na zagayowa aka yi suna, inda Dangin Innarmu suka mata sha tara na arziki, tare da fatan badi su dawo suna, dan since da alama shukar da suka yi zata yi yabanya da yado.

        Sannu sannu bai hana zuwa, sai dai ajima ba aje ba.

     Tafiya tayi nisa, ga Yadiko kullum ta samu ciki sai ya zub'e.
     Wani abinda ya kashe mata jiki shine yadda Innarmu, ta bata ni ba tare da ta nuna damuwarta akai na ba.

        Wata na takwas, Innarmu ta fara wani laulayi me zafi, dole tasanya aka yaye ni, abinda ya kuma bawa mutanen gidan mu mamak yadda Innarmu tace tabarwa Yadiko ni duniya da lahira.

BAHAUSHIYA.....!?Where stories live. Discover now