Manga

1.3K 118 0
                                    

BAHAUSHIYAH𖣘︎

   𝘏𝘢𝘵𝘵𝘢𝘳𝘢 𝘠𝘢𝘯 𝘔𝘢𝘵𝘢

Manga!

Babi-sha-bakwai.

   D'ago kaina nayi cike da mamaki, yo Allah na tuba tunda na shigo garin narabi, ko namijin fara bai tab'a zuwa inda nake ba balle namijin mutum.

  Kallon Yan uwana nayi naga suma mamaki suke, can sai ga yara a guje, har suna shirin faduwa.
         Sai ihu suke, Malama Kiga bakon da yazo ya bamu kudi mu raba.

      "Waye??!"
          Na tambaya a takaice,
"Wani me kama da mutanen cikin tv?!"
      Dumm kirjina ya buga Dr Aahil?!

    Cikina ne ya bada wani irin sauti, kululu. Kamar zan fasa kuka na dauki hijab Dina me hannu, sannan na kalli Luluh da tayi tsuru tsuru.

    Mika mata hannuna nayi ta mike tare da shiga daki ta dauko hijab ɗinta, kallon su Innarmu nayi sai ga hawaye sharrrr.

           Na rasa meke min dad'i.
"Toh kije mana!"
  Innarmu tace min.
A hankali nake jan kafana, wata bakar audi 2018 na gani, ji nayi kamar zuciyata zata fito daga cikin kirjina.
    A hankali nake takawa, har na isa gefen motar, kaina a sunkuye.

     Ga uban kwalla da yake zuba da mugun gudu, daga Idanuna.
        Sauke glass din gefen shi da nake yayi bakin shi dauke da toothpick, yana sarrafa ta. A bakin shi.
    Juyowa yayi tare da zuba min ido.
   Buɗe motar yayi sannan yace.
"Beautiful Girl! Zo Nan tunda Auntynki kuka ya zame mata, madubin dubawa ta."

   A kagge na d'ago kaina, muka zubawa juna ido.  Jikina ne ya dauki rawa, cikin tashin hankali da firgici nace.
" Dr Bature!"

           Rufe bakina nayi jikina yana keerrma, duk sai na diririce. Ƙamar na zura da gudu.
     
    "Shigo mota!"
      Yace min a takaice,
  Kallon su Baba Haruna nayi , tare da girgiza mishi kai,

          Bai kuma min magana ba ya kalle ni, na wani lokaci, sannan yace.
"Baki iya girmama bakon ki bane?!"

  Da sauri na koma cikin gidan, na dauki kofin silve na cika mishi ruwa, ajiyewa nayi na tuna muna da Faro a shago, na dauki. Kular abincin Baba wanda Innarmu tayi dambun Shinkafa.
   Na saka a tire, tare da jerawa. Sannan na fito, kicibis nayi da Manga yasha gabana, fauce tiren yayi sannan ya watsar dashi, sannan ya riko suma na da karfi, yana jana, abinda ya fiddawa Dr Bature da sauri daga cikin motar shi tare da Luluh, wacce ta saka kuka itama.

     "Manga sake Ni?! Manga ka bari idan na sallame shi sai kayi abinda ka saba na tijaranmu."

           "Naga shegen da ya isa miki magana, tunda na fahimci ke din baki gane Yaren da nake miki baki san ke din mallaki.."
      Ban san meye ya gani ba, domin Dr ya iso, yana jijjiga, Luluh.

      Sake ni yayi da sauri ya bar gurin, cikin wani irin kuka nace.
"Kayi hakuri! Abincin da zan kawo maka ne."

          Kusan a tare dashi muka durkusa, yana kallona. Ina share kwallar dake bin idanuna.
     
    Daukar cokali naje yi, muka dauka a tare, da sauri muka kalli juna. Nice na fara janye idanuna da hannuna.

      Sannan na kuma kai hannu zan dauki filet muka dauka a tare.
   Kauda kai  muka yi a lokaci guda, Luluh tace.
"Laaa! Addarmu yau sai kallon kuda kuke,"
     "Ya labari?!"
          D'ago jajjayen idanuna nayi, na dan kalle shi, kafe ni yayi da idanu. Sannan ya juyar da kan shi.
     "Ohhhh! Manga ko? Kuma."

     "Husnah! Wannan shirmen fa?!" Kin tsaya shiririta." Inji Baba,

   D'agowa Dr yayi cikin nutsuwa ya gaida Baba, sannan ya mike da Luluh a kafad'arshi, ya koma gurin motar shi.

BAHAUSHIYA.....!?Where stories live. Discover now