First challenging

1.2K 123 4
                                    

BAHAUSHIYA𖣘︎

     𝘏𝘢𝘵𝘵𝘢𝘳𝘢 𝘠𝘢𝘯 𝘔𝘢𝘵𝘢

First challenging...

Babi-tara

    Haka na bar makarantar ina kukan zuci, har na isa tasha.
         Babban damuwata me zan gayawa Innarmu?  Ambaton Allah nake  baji ba gani. Har na iso Kaduna, na rasa inda zan kai kayana.
    Kawai sai na dauka na wuce gidan wata Yar unguwarmu matar tsohuwa ce, bata gani. Na ajiye zan zo na amsa.

     Sannan na wuce Asibiti nan naga Halin da Baba yake ciki zafin ciwo ya tab'a mishi brain, sam yaki a ya zauna ni kawai yake son gani, yana gani na ya rike hannuna sannan yace.
"Muje ki kaini Mahaifata kar na mutu anan dan basu da asara sai ke."

      Duk yadda naso ya fahimci halin da yake ciki yaki, dan dole aka mishi Alluran barci. Muna cikin jarabta, amma Alhamdulillah tunda Allah bai wulakantamu ba. Jikin Baba da sauki matsalar shi yasa rai sai mun bar Kaduna, dan har zuciyar shi ta soma tabuwa. Abun tausayi haka muka tsayar da shawara, tare da rubuta mana magani, sauran kudin da ya rage aka bamu.

      Ranar da muka dawo, jikin mu duk yayi sanyi dan a ranar muka tattara kayanmu tsaf, muka yi bankwana da garin Kaduna.

          Baya bata kad'an...
   Tafiyar mu kadan Sai ga Dr Bature yazo nima na, kuma abin takaici ya manta sunan Garinmu, sai dai Rabi yake cewa.

        ...... Tafiyar awa hudu ya kawo mu, garin Narabi. Abin bakin cikin shine anki bamu inda zamu sauka, duk yadda muka roki arziki, amma suka k'i.

    Sai da wani dattijo Abokin Malam Manga yayi musu fatafata, aka bamu wani karamin part me dauke da dakuna biyu, nan ma, mutumin yace ba zai yu ba shine suka bamu shashin Innarmu na dame dauke da dakuna hudu, dukda ginin jar kasa ce. Amma yayi, dan haka muka shiga da baba cikin dakunar bayan mun gyara ko ina.

         

           Abin tausayi sai gashi wai kyamarmu ake a cikin gidan, babu me zuwa gurin mu, Mubarak da Abdullahi, da Ghaddafi idan suka je masallaci ba'a tsayuwa kusada su.

            Tsagwama kuwa ba a cewa kome, daga ni har Meemah da lulu bamu fita ko ina. So muna cikin wani halin rayuwa.

    Godiyar Allah mun tanadi kayan abincin mu, shi ya taimake mu, kome muna dashi. Sannan ga Atm din Dr B, na kasa amfani dashi.

       Jinyar jikin Baba shine matsalar mu.

         Satin mu biyu da dawowa, Baba Yawale da Baba Haruna suka zo har kofar shashinmu, wai sun zo duba Baba.

        Basu shiga ba suka tsaya daga bakin kofa.  Suka gama abinda zasu yi sannan suka fita.

     Alhamdulillah, dukda halin da muke ciki, cimmar mu me kyau ce, domin da masarar mu ta kare, kudin Hannun mubarak ya tafi nabardo yayi mana siyayyar kayan abinci.

            Haka zalika baba na cika wata guda muka kawo shi, bauchi kunsan sha'anin kudi kuma zara bata kyale dami ba, dan haka na tafi bankin da naga ansaka sunan shi a jikin Atm din, wato Ecowa, nan naje cire kudin abinda na fara duba balance din, dafe machine din nayi kwalla na zubo min, sabida kudin da suke cikin account din ya wuce misali, asalima kamar account din shine na CAN.

     Dan haka cikin hankali irin nawa na cire naira dubu 50, sannan na bar gurin, na koma asibitin nan na samu sun bashi gado, duk abinda aka rubuta sai da muka saya.

          Idan naga halin da muke ciki, blime kaina nake sabida duk abinda ya faru laifina ne.

      Bazan tab'a yafewa kaina ba, dan haka, na duba wayata na kira Mubarak, na gaya mishi ya gayawa Innarmu an kwantar damu.

BAHAUSHIYA.....!?Where stories live. Discover now