Second Challenging....

1.1K 124 4
                                    

BAHAUSHIYA𖣘︎

    𝘏𝘢𝘵𝘵𝘢𝘳𝘢 𝘠𝘢𝘯 𝘔𝘢𝘵𝘢


Second Challenging.

Babi-sha-daya

       Ban san me ya faru ba, kawai sai ga Mubarak ya shigo da Baba rike dashi, fitowa muka yi dukkan mu. Innarmu tace.
"Lafiya Mubarak"
           Ganin Abdullahi muka yi ya zari wani itace ya fita da gudu, babu dan kwali na bi bayan shi, wallahi yaron nan baya ji. Yana zuwa ya sami kafadar Baba Haruna ya zabga mishi b'arin Itacen nan.

        Cak na tsaya ina kallon ikon Allah, haukacewa yayi baki daya yayi ta muka musu itace.
     Kusan shekarun shi nawa, sha takwas! Amma dake yana da tsayi ya mike zaka rantse yafi mu shekaru.

              Zuwa nayi na zabga mishi mari, cikin ciwon rai dan ban san me zan iya yi mishi after all,
     Yana huci yace.
"kai Tsohon banza maza sake min kanwa! Saketa kafin na ci..."

       Jijjiga shi nayi cikin gigita nace.
"What?!"
       "Wannan tsohon banzan wai dan ya renawa mutane hankali, wai auren meemah yazo yi, wallahi idan bai saketa ba, Allah sai na kashe banz...."

Rufe mishi baki nayi. Ina kallon su, cikin nuna dagaske haka ne, dattijon yace.
"Bashi na Haruna yaci. Na kusan dubu talatin, shine ya bani auren diyar wan  shi."

          Akan 30k an wargaza future din kanwarmu.

         Juyawa nayi na koma cikin gida, birkita kayana nayi na ciro dubu talatin cif na kawo ishi, nace.

              "Bani? Sakinta!" Na mika mishi hannu, cikin duniyanci yace.
"Ko kina da inda zaki kaini tsohuwar kilaki?!"

          "Abdul! Ji min da tsohon nan ba shi ba hatta wanda ya tsaya mishi ka karya min kafafuwan shi."
   
    Allah kenan, ganin yadda Abdul ya kinkimi itace zai kai mishi, aikuwa yace.
"Toh mara kunya ko girman tsofa na baki gani ba, toh na saketa daya."

    
       "Ina ukun zaka yi tsohon banza!"
         A take dai sai da muka raba auren abinda babu kyau, Allah mun tuba. Baba Haruna kan ai shiga dashi cikin gida aka yi, tare da nima mishi maganin tsamin jiki.

     Koda muka shiga cikin gidan, rufe Abdul Innarmu tayi da duka, tana yi tana kuka.
    
Ba shi daya ba, nima bata kyale ni ba.

           Mun zata case din ya kare washi gari sai ga, yan sanda.

       Ban san yadda zan fada muku halin da muke ciki ba, amma maganar gaskiya, muna cikin bakin ciki mara iyaka, muna ganin tasku da jarabta, bamu rasa kome ba, sai kwanciyar hankali da nutsuwa.

        An tafi da Abdul, wani abin bakin ciki, shine ba ajiye shi a Toro ko Magama gumau, ba sai aka kawo shi bauchi.

         Sannan aka ki gaya mana inda yake, tsabar zalinci.
      Koda muka zo bauchi mun fara bin kananun ofishin yan sanda. A ranar a cikin garin bauchi muka wuni.

     Har dare babu labarin inda yake, sai da muka gama yawo. Dakyar muka sami labarin inda yake, an kai shi can Dass.

    A daren muka dauki shatar mota har Dass, acan suka ce baya nan. An kai shi wani karamin kauyen dass, wato Zan.

      Abinda bamu sani ba, tsohon da ya auri Maryam ne ya biya kudi aka kawo Abdul gurin, mun same shi an mishi mugun duka, ko daga kai ba ya iya yi.

        Kuka rahama ce, dan haka basu bamu shi ba sai da muka yi Yaren hannu da aljuhu.

     Aikuwa suka sake mana shi, a daren muka wuce dashi asibitin bauchi, aka bashi magani.
    
    Muka kuma biyan kudin mota aka dawo damu gida, Muna isowa karfe biyar na asuba. Gida muka shiga dashi, Mubarak da Driven da ya kawo mu, suka wuce masallaci.

BAHAUSHIYA.....!?Where stories live. Discover now